chapter 25

32 4 0
                                    

"If Allah want to do good somebody, he afflict him with trial"   √Sahih Bukhari

Tasnim ta dawo daga wurin aiki ta yi ido biyu da tsalayliyar Motar Nur. Daya daga cikin yan aikin gidan ta kira. Ya kara so kusa da ita tare da runtsina wa ya Gaishe ta. Ta tambaye shi waya zo da motar nan.

Mai aikin yace ranki ya dade ay Motar ta na Gidan ce kuma kamar ma ta Hajiya ce.

Tasnim tace Ummi...

Dan matashin yace A'a ta Hajiya Nur.

Nan take tasnim taji abu ya tokare ta a wuya. A fisace ta shiga ciki. Dakin Ummi ta shiga.

Ummi tambayar ta; lfy Tasnim ki ka shigo ko sallama ba bu.

Tasnim tana huci kammar wadda tayi gamo a kan hanya. Tace Ummi... Biki san me ya faru.

Ta ke hankali Ummi ya tashi dan yanda Tasnim ta shigo da yanda take mata magana.

Ummi tace ki fadi min mi ya faru.

Tasnim tace Ummi mota mai tsada a ka siya wa Nur. Tayi biyun ta Jannah.

Ummi mike tayi tace chabdijan! waye ya siya mata??

Tasnim tace ban san Ni ba. Muje ma ki gan ta.

Suka tafi parking space. Ummi tsaye tayi ta na nazarin mi zata yi. Tana so ta kashe Motar amma in ta yi haka ta zubda mutumcin ta. Tsaki tayi takoma ciki. Tasnim ta bi ta. Bayan sun koma tasnim take tambayar Ummi mi ne ne abin yi.

Ummi tace lalle ma, mi ko min waya ta.

Tasnim ta miko mata wayar ta. Ta kira Aman ta tambaye shi wa ya siya wa Nur Mota. Yace abi ne ya siya mata.

To kun kyauta. tayi tsaki ta kashe wayar.
Na rasa uwar mi suka mai amma daga su har Ni dai dai da su nake.

Aman ya dawo gida ko part din Ummi bai shiga ba ya wuce na shi. Sama ya hau ya iske Nur na tallata shagon su. Abin da ya bashi haushi daga ita sai gown din da ta Fido mata kusan duka surar ta, Sai hula da ta sa. Karaso wa yayi ya dauke wayar. Nur ta kalle shi.
Fuskar sa daure yace ba na hana ki shigar nan ba. Ya Matso zai kama ta tayi sauri ta kawce tare da bashi hakuri. Dan ita kawai tana tallata shagon Mammy ne kuma ba duk ji kin ta ta dauka ba tunda ba face. Ya kalle ta ya wuce. Ajiyar zuciya tayi tare da cewa jaraba.
Ta kashe laptop din ta.

Sometimes Nur ta na sa kayan dan ta tallata su but face din ta a rufe yake duk wainda suke following din ta social media Basu san fuskar ta ba sai dai wainda tayi following kadai suka san ta.

Ummi ta samu abi a part din shi cikin dakin sa yana cire agogon hannu sa tace Alhaji abin da kayi ka kyauta ke nan. Yanzu waccen yarinyar dan asarar kudi ka siya mata Mota. Duk motocin gidan nan.

Shiru yayi ya kyale ta har sai da tace abi magana fa nake maka.

to mi zan ce miki. Hakkin yarinyar nan ne dan haka Dolle in mata. Ita din ba iya tace ba, Bayan haka jannah da tasnim ba su da mota ne?? Da dai ace ba su da mota in na siya wa Nur za a ce dan mi balle suna da ita ke ko ba su da ita na siya wa Nur ba wanda zai tuhumai ni a kan haka. Dan haka kar ki bata min rai in ba ki da abin da zaki ce min tashi ki tafi.

Ummi ta saki baki tace lalle alhaji wai Ni yau ka ke kora saboda wata banza, jaka, low class da ita.

Abi ya tashi ya bar mata wurin dan bai da lkc sauraran shirmen ta. Ummi ranta ya yi mugun b'aci ta dawo part din ta tana gungumi.

Asabe ta iske a parlourn. Asabe ta gyara zaman ta tare da tambaya; lfy Zainab ki ka dawo kina balali.

Ummi ta zauna tana hucci kamar wadda tayi gudu tace dan adam butulu wai Ni abi zai wulakanta kamar Ni.

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now