Aman ya fito daga Dakin karatun shi ya bude wa Ahmad kofa. Ahmad tare da cute girl wadda ya dauke ta a hannun sa wato zara. Hannu ya ba Aman suka gaisa sannan ya shigo Aman ya rufe kofar. Zaunar da ita yayi kan kujera amma ta ki zama sai dai yayi lapping din ta. Aman ya zauna. Tara da yi wa zara murmumishi. Ahmad yace biki gaida shi ba. Ta gaida shi. Ahmad ya tambaye shi ina amarya. Aman daure fuskar shi yayi yace kai malan wurin na ka zo so kar ka bata min rai. Ahmad yayi murmumishi yace dadi na da kai akwai saurin fishi daga na tambaya. Ga Zara ta zo gaida ta dan Allah ka je ka kira ta ko in kira ta.
Ka kira ta????
Eh mana tun da kai ba zaka ba, daman ina da digit din ta. Aman ya daure sannan ya tashi ya nufi sama. Ahmad murmumishi yayi yace my man!!!
Nur na kawnce da waya a hannun ta Yana shigo wa ta daure fuskar ta cigaba da harkar ta. A kofa ya tsaya "Tashi ke je kasa za ki gaida Ahmad." Ya fadi cikin bada umarni. Nur aranta tace ya Allah ba damar mutum ya huta. Ta mike ko Kallen shi batayi ba ta nufi kofa. A haka za ki sauka?? Tace Amtanfa ce Kuma kaftan.
Wuce ki sako hijabi. "Amma..."
Zata yi magana kallan da yai mata ta sha jinin jikin ta. Ta nufi closet din ta ta dauko hijab din ta ta dora bisa dankawlin. She is Not comfortable with that ta cire hijabin ta ja dankawlin zata cire, ta manta da ta sa pins. Pin din da dankawlin suka makale a gashin ta, da ta ja sai ta ji zafi. Toilet ta shiga domin ta duba dankawlin. Aman da ke jiran ta ya karaso wurin closet ya ganta a toilet ta na faman cire dankawlin. Daga mirror din toilet ta hango shi fuskar sa a daure. Yace ke Baki da hankalin ne da zaki zaunar da mutane. Cikin Murya kuka tace. Noo.. Ni na kasa cire dankawlin. Tana ta fada da dankawlin da ya harde da Gashin ta ga rebon din dake kanta. Nur a ran tace ko ma yace zai taimaka min. Mai baƙin hali kaiwa tayi tsaki chan kasa ta cigaba da famam cire dankawlin. Ya juya ya nufi kofar Dakin. Nur tace marar tausayin kawai. Tunanin sabir ya zo mata bata san lkc da zafafen hawaye suka fara sauko wa. Hannu taji a kan ta ta daga idon ta ta ga Aman fuskar sa a daure. Hada ido suka yi da shi ta mirror toilet din ya ɗauke idon shi ya cigaba da cire pins din sai da ya cire su sannan ya aje mata dankawlin yace goba ma ki kara. Ya juya zai fita yace ki sauko ana jiran ki. Ta kokarta tace mai thank you for the help.. ko kallon ta bai yi ba ya wuce. Rebon din kanta ta ida cire wa ta daure kashin ta sannan ta wanke fuska ta fito. Zaune ta gan shi kan gado. Wurin mirror ta nufa zata zauna a tsawaice yace wuce mu tafi. Tace amma.. ta sa hijabin ta ta bishi a baya. Suka sauko kasa. Ahmad yace amazing!!! Kun sanya ni anan daga ka je ka kira Amarya. Murmumishi Nur tayi tare da Gaishe shi sannan ta zauna. Ahmad yace daman na kawo miki zara ta Gaishe ki. Zara tace ina wuni. Bayan sun hada ido da Nur. Nur tace zo mu gaisa. Ta sauko daga kujerar ta nufi wurin Nur. Nur ta bata hannu suka gaisa tace ykk? Zara tace Lfy Qlau, ina Mummy? Zara ta tsaya ta na kallo ta dan ba ta san wa ta ke tambaya ba. Ahmad da Aman kallon juna suka yi. Ahmad yace Ummu ta sani ba Mummy ba. Nur ta ɗan yi dariya tace ki gaishe min da ita. Ta kada kan ta. Nur tace bari in Kawo soba zaki sha ko?? Ta kada mata kai. Nur ta mike ta shiga kitchen. Ahmad yace kai Aman haka a ke daga ka kira ta sai ka bar ni ni kaɗai. Aman ya Kalle shi bai ce mai ko mi ba. Ahmad yace ko da yake Ni wurin Amarya na zo ba wurin ka ba. Aman ya kalla shi yace Wurin amaryar ka zo??? Eh mana. Ga inda za a tarbe ka hannu bibbiyu, ni Aman tun da kayi auran nan ka ke wani jan fuska sai kace Ni na ma auran. Aman bai tanka mai ba sai dai ya tambayi zara ya school. Tace school lfy Qlau. Aman yace good. Nur ta fito tare da jug sai tray da ke dauke da cups da ruwa. Ta aje kan center table ta dau cup din ta zuba wa zara ta mika mata tace Thank you sannan ta Zuba wa Ahmad ta mika Mai. Ahmad ya tambaye ta ya shagon ku, i dan na samu time zan dau zara muje. Nur tace alhamdullilah, gsky kam gawra ita ma a kai ta dan na lura ana ji da ita. Ahmad yace yaushe kuma zaki fara zuwa shagon ko har yanzu ba a gama cin amarci ba. Nur ta kalli Aman wanda kawta kawta Bai ji dadin maganar Ahmad ba. Yana so ya tashi amma bai so ya bar su. Nur ta ɗan yi murmumishi tace ko daganan ina sa nin yanda shagon ke wakana kuma Uncle hanif da Mammy suna kula da shi. Cup din Zara ta mika wa Ahmad tace Daddy a kara min zobo. Nur cikin mamaki ta kalle su daman zara iyar shi ce?? amma basa ko yanayi dashi balle Ummu. Ta fadi a ranta. Kafin tace wa zara Kawo in kara miki. Zara ta bata cup din sannan ta zuba Mata. Ahmad yace Nur Gaskiya sobon yayi daɗi. Nagode. A takaice Nur tace Bakomi. Wayar Ahmad tayi ringing ya dauka bayan wasu dakiqa yace to ganin nan zuwa. Ya katse wayar tare da mike wa. Yace Aman Ni zan wuce. Aman shima ya mike. Ahmad yace Nur sai anjima sai mun kara zagayo wa. Nur ta mike tare da zara. Suka yi sallama suka nufi kofa. Nur ta tattara cups din ta kai kitchen. Aman yace mai sai anjima. Ahmad yace korata kake. Aman yace kai din nan kana bata min rai. Ahmad yayi murmumishi yace to yi hakuri inna bata min rai. Kai din ney da abin ban dariya. Dan Allah kadin ga skin rain ka. Nur dai na hakuri in har haka ka ke wani dadaure fuska. Ahmad!!! Aman ya kawbe shi. Allah baka hakuri Ni zan wuce. Aman ya koma ciki ya rufe kofa tin kafin Ahmad ya tafi. Karo ya ci da Nur wadda ita ma fuska daure. Ta nufi sama dan yau ya bata mata rai da ya ki barin ta taje wurin Mammy.
YOU ARE READING
NURUl QALBI 💖
General Fictionlabarin rayuwar Nur wadda a ka aura mata mutumin da bata sani ba. ta auri mutumin daga shi har dangin shi basa San ta sai mahaifin mijin. like always in all marriages there's chanllages. Nur have to over come all the challenges. ku biyo ni domin ga...