Ramin karya 03

87 4 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 0️⃣3️⃣

   Yi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "kınsan fa har yanzu bai San Ina wanan sana ar ta ara wa mutane kaya na ba shiyasa duk inda yamma take nake hada Ina wa Ina wa nake boyewa shikenan asirina a rufe abuna dan wlh nasan duk ranar da rabiu zai San Ina bada kayan sawa na haya toh wlh sai igiyar aurena ya girgiza

Tafa wa sukayi suna dariya , shukra tace ke fa duk bakin ciki ne fa wai ace za a hana ka Jin dadin rayuwa , sun karkame mu a gida kuma su ce baza muyi abunda zai saka mu farin ciki ba

Kingani nan wlh babu abunda nafiso irin na saka kaya na shiga taro naji Ana ce mun nayi kyau ko kuma ana kodani, ko kuma naji Ana zuzuta kudin suturar dake jikina ke yafi mun a biyamun kujerar saudiya

Kai shukra saudiya fa daban ce Hafsa ta fada tana dariya

Hmm bazaki gane bane ba hafsa , ke kinji dadin ki ma mijinki a siya miki suturar kece raini , ni fa wacan sallahar Atamfa fa roba aliyu  ya kawo mun wai roba ni shukra ni zan saka roba sabida ya raina ni

Wlh hafsa kadarace ma aurena da aliyu  da naci da datuni na auri wani shegen mai kudi abuna na huta

Wayar shukra ce tayi Kara dan haka tayi saurin dauka dan ganin waye yake kiranta

İlham ce wata matar da suka hadu a kasuwa gurin siyan jaka ta ganta yar Gayu gashi ta siya jakankuna kusan na dubu 100 a gurin mai Shagon nan fa shukra ta rikice ta dinga jan matar nan da hira har suka Saba a kasuwar sanan sukayi exchanging number

Saidai da shukra ta dawo gida tayita kiran ilham din  aman bata dauka ba shine yanzu ta biyo kiran , dauka tayi ta na fadin hello Besty

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now