Ramin karya 11

21 0 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 1️⃣1️⃣

Gurin makeup ta wuce tana ta Tuna'nın yadda zata samu sauran kudi ta bawa  mai makeup a haka dai har ta karasa shagon mai makeup

Salma touch ta karbe ta hannu bibiyu duba da shigar dake jikin ta dan tasan kudin Kayan da sarkar dake jikin shukura dan haka cikin girmamawa tayi mata iso cikin shagon ta bata waje ta zauna nan kuwa kan shukura ya kara girma taji ta tazama wata Hajiya sai izza take tana dadaga Kai abunta

Ta tarar da mutane kusan biyar tana zaune akayi musu kuma taga basa bata kudi saidai su ce sunmata transfer su tace tom Tagode sai su tafi gashi ita account din ma bata taba bude wa ba ballantana ma tace zatayi mata transfer din aman dai tasan Allah zai fitar da ita daga cikin wanan masatalar da ta saka kanta haka dai tayi shiru tana dana wayarta har layi yazo kanta

Zama tayi kujerar zaman customer nan fa aka fara cancanda mata makeup cikin lokacin kadan aka gama nan fa Shukura ta kuma fitowa a hajiyar şak nan fa Salma touch ta shiga zuba mata hoto dan tayi mata kyau sosai gashi kuma tana kallon ta matar manya dan ita duk zaton ta matar wani hamshakin mai kudi ce dan shukura akwai kamewa idan ta shigo cikin mutane dan karda a rainata

Bayan ana gama hotunan shukura ta dauko dubu biyar dinan ta Mika ma Salma touch tace ga wanan 5k ne zan miki transfer din 10k yanzu ta dauko wayarta ta shiga wani waje ta ce Salma touch ta fadi mata account number din

Salma touch ce tayi murmushi tace aa Hajiya basai kin bani cash ba ki hada ki tura mun gaba daya wlh bana son ajiyar cash ne sai ayi ta kashe wa

Shukura ce tace okay toh kinga yanzu ma ba network aman Ina zuwa gida zan sake tura miki

Salma touch bata kawo komai ba dan ta Saba yiwa manya irinsu shukura makeup kuma a biya ta bayan sun bar wajen daywan su ma har Kari suke mata mai tsoka dan haka tace wa shukura ba komai saitaji ta , ta karanta mata account number din ta saka sanan tayi saving number dinta sukayi salama shukura ta fice abunta a ranta tana godewa Allah

Kai tsaye mai dan sahu ta tare ta nufi gurin bikin dan shamsiya ta Kira ta Akan itafa tana gurin bikin kuma amarya ma har tazo aman dai ba a shigo da ita ba ana jiran manyan yara su karaso sai a shigo da amarya

Gani nan shamsiya shukura ta fada lokacin da ta hau dan sahun tana wani baza hancı dan gani take wanan kwaliyyan data dauka bai kamata ta hau dan sahu ba taja tsaki lokacin da suka hau wani jakin baban gida yayi sama da ita sanan ya dawo kasa

A haka har suka karasa gurin event din , ta fito daga napep din ta salame shi tana ta waige waige kar wani ya ganta a sauke ta a napep

Karaf kuwa shamsiya ta gano ta ta karaso dai dai lokacin da mai napep yaja mashin dinsa yayi gaba

Ke Kawata ya naganki a dan sahu har yanzu oga bai siya miki mota bane ba ko ya kawo ki da kansa tunda dai yana da mota shamsiya ta fada Tana dariya

Uhm Kedai Bari shamsiya ae yakawo mun mota nice dai batayi mun ba shine zai Chanza mun sabo

Shikuma tasa motar tana garage wlh ta dan samu mastala shiyasa kiga gani a napep aman kinsan ae Nafi karfin napep Kawata ta fada tana dariya

Gskia kam Nima nayi mamakin ganin ki a napep aman fa Kawata kin hadu wlh sosai gaskiya mijin ki yana kula dake sosai kalli fa jikin ki

Far da ido shukura tayi sanan tace Kedai Bari madara kamar abun banza a gidana ba dole ne kigani a haka ba kaji kuwa har sadakar sa nake wlh

Ae Nasani Kedin nasha fada miki tun Muna makaranta ke ba matar yara bace dole sai mai kudi kamar mijin ki kwanaki Maryam isa tana mun wani magana wai kamar taga mijinki a bakin titi gurin masu faci wai da wasu irin kaya toh nidai nace mata karya ne tun a lokacin nace zata iya yiwuwa gyaran motansa yakai wai tace ita ba haka tagani ba kinsan banason munafurci Maryam kuma akwai gulma shiyasa ban bata fuskar ta karasa maganar ba aman dai zatazo gurin bikin nan ki same ta da maganar

Shukura kuwa cikin ta ya duri ruwa aman saita dake ta dan bata rai tace yanzu Gülmar Maryam isa yakai ta ce ma MIJINA yana faci sabida ita ta rasa mijin aure wlh saina ci ubanta shegiya wace tayi kwantai

Shamsiya ce ta shiga bata hakuri akan ta dauki abun da sauki karta dauke shi da zafi shukura tayi kwafa kamar gaske karyan akayi ma mijinta ta ce shikenan bara na jira shegiyar

Toh shikenan zo mu shiga cika nan ta janyo hanunta suka shiga cikin hall din waje suka samu suka zauna har lokacin shigo da amarya yayi wasu kawayen nasu suka karaso aka shigo da amarya Anata nishadi

Sun zauna kenan saiga Maryam isa ta zo ta janyo kujerar kusa da shukura ta zauna tana murmushi

Yauwa Maryam daman ke nake jira kizo shukura ta fada tana mata mugun kallo

Toh nema na kuma shukura Ali dake. Haka suke fada mata sabida kowa yasan yadda aka sha Şoyaya tsakanin shukura da aliyu sai kawayen su suka mayar mata sunan ta shukura Ali

Eh daman maganar wai kinga MIJINA a gurin faci ne Akan menene xaki je kina munafurci na ta fada tana hade rai

Maryam isa ta kalli shamsiya dan tasan ita kadai ce zata fada ma shukura maganar ta dan risina Kai dan bata so shukura taji magnar ba dan Maryam isa irin wanan munafukan kawayen nan ne Wanda zasu fadi Abu a bayan idon ka sanan kuma su nuna basu fada ba

Ganin Maryam isa tayi shiru na shukura ta shiga zazaga mata rashin mutunci inda take shiga ba tanan take fita ba har da su gorin aure aman Maryam isa bata takanma saima kunya daya kamata tayi kasa da kanta tayi shiru tana Jin zafin abubuwan da shukura take fada mata har shukura ta gaji tayi shiru tana huci

Allah ya baki hakuri anan kisani aure lokaci ne Nima allah zai bani nawa mijin idan lokaci yayi kiyi hakuri tana gama fadin haka ta tashi ta bar wajen tana hawaye

Shamsiya ta kalli shukura tace ke da kika San mijinki ba sana arsa Kenna ba sai ki rabu da ita ba aman yanzu dai ma abunda kika yi bazan ce miki baki kyauta ba aa kin kyauta ko dan gobe idan taga Abu zatayi shiru da bakin ta bazata taba hada gulma ba aman maganar taki aure da bakiyi mata ba shukura aure fa lokaci ne

Uhm rabu da ita shamsiya ae gwara na fada mata banson karya da gülma

Nan suka ji mai dj yana ta kiran kawayen amarya nan fa suka tashi  suka je filin rawa aka shiga liki shukura ganin an fara miki kar a Raina ta ta je gun masu Chanza kudi suka Chanza mata gaba daya wanan 5k dinan ta dawo filin rawa dj yana mata kirari tana zuba kudi a haka saida ta lika gaba daya kudin harda na motan nata bata Ankara ba

Saida suka gaji da rawa sanan suka je suka cika tumbin su nan fa hankalinta ya dawo kan gida ta duba wayarta taga har 6 na yamma yayi

Na shiga uku ta fada tana dafe kirji ....


✍️Mrs abbah

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now