📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 1️⃣3️⃣Huda nace dan ubanki ki tashi kije gurin su danlami ki karbo mun kwanunka na sanan su baki Dari biyar kudin abicin da suka ci mu hada Ina mu Ina mu mu bar kasuwar nan tunda dai kingani mun siyar da komai har yan karere ma sun siyar jummai ta fada tana hararar badariya ta gefen ido dan sosai sun siyar da zobon da kunun ayan duk da dai bai kare ba aman sun yi ciniki sosai
Toh jummai huda ta fada Tana tashi rai a bace dan ita a rayuwarta idan akwai abunda ta tsana shine a aiketa gurin mazan kasuwar karbar kudin abincin ko kwanuka aman jummai ta kasa daina ai kanta wasu daya wansu zancen banza süke mata wasu kuma su Nuna sonta suke wasu kuma su mata kalllon banza kamar kaskantaciya
Tashi tayi ta yi cikin kasuwar har shagon su dan lamin tana hade rai
Tana zuwa tayi musu Salama ciki ciki , Danlami na ganin ta ya Washe Baki yace aa su hüdallahi yan mata jummai ce ta aiko ki ko dan nasan ke Baki zuwa gurin mutane sai dai jummai ce ta aiko ki
Bala dayake gefen sa shima washe baki yayi yace kwarai kuwa mutumina huda ae daban take yarinya ga kyau ga diri dan Allah huda ki amince mun wlh idan kika aure ni kin daina wahala zakina ci kina koshi ya fada yana kashe mata ido
Harara hüda ta galla masa sanan tace dan Allah ni kun bi kun ishe ni da zance ni ba abunda yakawo ni kenan ba kwanukan jummai nazo karba sanan kuma Allah ya kiyaye na aure ka ni sai nayi jami a sanan ko da ma banyi ba wlh bazan auri irin ku ba ni Nafi karfin ajin ku dan haka ku bani kudina nayi gaba
Bala ne ya saki baki rai a bace yace au ke wace kuke tallar abinci har kina da damar zaban mijin aure kinga bara na fada miki ba kaskantatu irin masu kasa abinci a rumfar kasuwa ehe taimako nayi niyyan yi aman tunda ke bakida wayoo na fasa
Danlami ne yace kaga dakata Bala duk wanan bai taso ba huda ga kudin ki ya miko mata Dari biyar guda 2
Aa jummai tace Dari biyar ne
Eh Nasani Dari biyar din Kai naki ne kema
Nagode huda ta fada tana juya kudin
Ya nuna mata wani tebur yace ga kwanunka ki nan sai ki dauka ko
Tom ta amsa sanan ta dauki kwanunkan ta fita daga shagon
Dari biyar din da Danlami ya bata ta boye cikin Riga dan hüda bata kunyar ansar kudi ko Wanda bata sani bane ya bata kudi karba take abunta dan haka karbar kudi gurin samari irin su danlami ba sabon abu bane gurinta
Tana komawa shagon ta Mika ma jummai kudin sanan ta ciro Dari biyar din data ajiye a rigar tace ga kudin abincin ki jummai
Karba jummai tayi sanan tace Allah ya kiyaye ki da wlh bazaki kici na dare ba aman yanzu tunda kin biya bashi ae shikenan
Jummai changi zaki bani yanzu huda ta fada tana kallon jummai
Ae Nasani Kai wanan yarinya akwai bakin hali yanzu changin naira dari da hamsin dine sai na Baki yara mata suna zama jari aman ni kam jummai Kaya kika Zame mun wlh huda
Dana Haife ki Ina tunanin sai kin siya mun mota da gida aman kin nace ma boko mai makon ace yanzu kina Lagos kina Neman kudi kalle ki dan Allah yarinya mai jini mai kyau dake kin kare da siyar da shinkafa da wake a bakin kasuwa huda wlh Allah wadaran ki hüda wlh banyi sa ar haihuwa ba
Huda ce tayi shiru ta sunkuyar dakai wato ita jummai bata damu bama inda ta samu kudi bayan tasan ba sana ar komai take ba aa haushi take ji ta tambaye ta changi harda yi mata baki duk da tasan idan da sabo ta saba da halin jummai aman na yau yayi mata ciwo sosai
Ita so take tayi karatu ko zata samu miji mai arziki dazai aure ta tunda kawayen ta na makaranta sunce yanzu maza masu kudi basa auren marasa ilimi mussaman yan matan da basuyi jami a ba shiyasa ta yanke shawarar zatayi jami a Kodan itama ta samu miji mai kudi saidai jummai ha hakan take so ba gani take boko shine ma yake sawa mutum ya ki samun kudi shiyasa ba son makarantar huda take ba ita idan ta ita ne huda ta hakura da karatu tazo su cigaba da tallan abinci ko a kaita aikatau wani garin kamar su Lagos da Abuja su samo arziki mai yawa
Jummai ce ta kunce zaninta ta jefo ma huda naira dari tace ta gashi hamsin din kuma na cinye banzar yarinya kawai marar wayoo
Har tayi gaba kuma ta juyo tace kuma a fara harhada mun kaya su Modibo zasu Nemo mota mu koma gida ke kuma zaki iya fara tafiya kina gama hada Kayan dan wlh bazan biya miki kudin mota ba Tana gama fadin hakan ta bar wajen
Badariya wace tana kallon duk dramar da akeyi ta kalli hüda tace hüda kiyi hakuri kinji idan kingama hadawa karki damu sai mu tafi tare kinji
Gyada Kai huda tayi hawaye fal idonta sanan ta yima badariya godiya ta saka Kai ta bar wajen zuwa ga rumfar tana hada Kayan zainabu ta Taya ta har suka gama hadawa , Modibo ya Nemo musu dan sahu suka jera Kayan sanan zainabu da jummai suka hau suka tafi gida suka bar hüda anan tsaye
Ko a jikin jummai duk da magariba tayi sosai dan har an fara kiran sallar mağrib dan ba yau ne rana ta farko ba da take barin huda a kasuwa tace ta San yadda zata dawo gida bazata biya mata kudin mota ba duk da tasan hudar batada kudin aman hakan bai dame ta ba
Badariya ce ta dafa huda dake tsaye tana kallon titi gaba daya abun duniya yayi mata yawa
Muje ko hüda kinga na samu dan sahu , Tom badariya aman nagode sosai
Uhm ba damuwa huda ae yayan ki goje shine ya nema mun alfarma har jummai tazo Dani kasuwar nan ta yarda na kasa kaya na a rumfar ta da badan shi ba da inajin yanzu mun yi sadakar zoban nan
Goge ya dawo ne huda ta tamabaya tana murmushi
Eh aman yakoma yace sai wani lokacin kuma zai dawo
Ayyah Allah sarki goje bansan yanzu yaushe zan kuma ganin sa ba gashi inaso nayi masa maganar waec Dina nasan jummai bazata biya mun ba ta fada da fuskar tausayi
Kiyi addu a Allah ya sake dawo dashi Kwana kusa kinsan dawowar goje zuwa zuwa ne taho muje kinga mai dan sahun nayi mana horn ta Kamo hanun huda
Huda ce ta Kama wa badariya cooler suka saka a dan sahu sanan suka hau yaja suka tafi suna dan taba hira har suka zo gida ...
![](https://img.wattpad.com/cover/373258922-288-k585625.jpg)
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...