Ramin karya 04

27 0 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 0️⃣4️⃣

Ilham shiru tayi na dan wani lokaci dan tantance muryar Wanda yake magana

"Dan Allah wacece naga missed calls dayawa ne , ?oh Besty nice fa shukra ta bata amsa tana murmushi

Ke wa please ? And why are you calling me Besty Ta jefo mata tambayar

Shura ta dan bata rai sanan tace nice shukra fa wace muka hadu dake a kasuwa jiya

Oh kece Ashe toh Ykk ? İlham ta tambaya

"Eh wlh nice " daman cewa nayi bara na Kira ki mu gaisa Ashe baki ma yi saving number na ba shukra ta fada muryarta ta nuna bataji dadin rahsin saving numbern ta da ilham batayi ba

Oh thanks ilham ta fada a takaice dan shukra Sam batayi mata ba tana gani kamar ita din ta girmi class dinta duba daga wayar ma da take rike wa

Yauwa daman insha Allahu idan nasamu lokaci zan zo fa gidan naki

Okay toh bye ! Aman wait kina ji na ko İLham ta tambaya

Eh inajinki Besty

Yauwa daman ce miki Zanyi idan kika Kira mutum once bai daga ba please ki kyalet maybe mutum is busy with something because dayawan mu munada abun yi pls dan Allah a kiyaye tana gama fadin haka ta kashe wayar tana jan tsaki

Shukra wani banbarakwai taji kamar dai wasa wasa matar nan magana ta fada mata , aman dai kodai bata gane ta bane ba

Ko ma dai menene zataje gidan su hadu dan sosai take son suyi amintaka dan ta iya daukar wanka ga kamshi da take na turare Wanda ita ta kasa gane irin wanan kamshin mai dadi shi ba kabbasa ba shi ba turaren ruwa ba matar dai Kata nan Masha Allah

Hafsa wace tana sauraron wayar da shukra tayi ta tabe Baki sanan tace

"Wlh shukra kina jan girman ki yanzu mene haka magana fa ta gaya miki a fakaice

Hmm ke Hafsa dadi na dake saurin fushi ba wani magana a nan Allah matar nan fa sosai mun Saba kuma kırkı ne da ita

Ke wlh nayi kawance da wanna ae nazama celebrity dan ko cikin dangin MIJINA musaman wanan yan iskan kanen nasa suka ga wanna a mastayin kawa ta sai sun ajiye raini a gefe sun dawo suna girmama ni

Hafsa ce tace yanzu ke sabida mutane kike zubar wa da kanki mutunci shukra haba

Dakata Hafsa , shukra ta kaste ta , ke kinsan kema kina aikata abunda kikaga dama gwanda ma ni kalan dangi nake ,

Dakata shukra basai kin cimun fuska ba ni bara na tahsi na daura girki

Nashiga uku shukra ta fada da karfi tana mikewa, na manta da na bar miya Akan wuta wai ya soyu Kai nashiga uku Allah yasa bai kone ba ta zura takalmanta ta dauki kayan ko salama bata yi wa hafsa ba ta fita a guje har tana tuntube ta nufi gidanta tana ta sauri kamar zata kifa...

✍️Mrs abba

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now