RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book
WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣8️⃣Har yanxu jamb result ya fito huda ta samu mark din da akeso dan haka cikin farın ciki take itama burinta zai çıka ta samu ta shiga jami a ta samu karatu mai kyau , Nan kuma data tuna da pretty sai ranta ya baci zuciyarta ta karye Allah şarkı pretty ta fada a hankula, Allah yayi miki rahama
A cikin zuciyarta tana jin bakin cikin yadda pretty ta rasa ranta akan biyewa son zuciya da rudin zamani shiyasa take tsoran fadawa irin rayuwar dan haka ya yanke hukuncin baiwa faisal dama dan ta yi aurenta aman sai gashi faisal ya wasta mata kasa a ido yaki aurenta wanan abun na mata daci sosai yanxu baban abunda yake damunta ma shine waye zai biya mata makaranta idan har sun bata gurbin Karatau tasan jummai bazata taba biya ba koda kuwa giyan wake tasha goje kuma ba ranar dawowarsa tunda shi ganinsa sa a ne watarana sai suyi shekera ma basu saka shi a ido ba dan haka ta shiga damuwa ainun dole tasan wanan lokacin indai bata samu ganin goje ba ta nemi Zee kuma Zee ha hanyar arziki zata nuna mata ba dan haka itadai tasan tana cikin tsaka mai wuya sosai
Ba a fi wata daya ba kuwa aka basu grubin karatu daga Zee har huda dan haka kowane cikin farın çıkı yake da anashuwa saidai huda ta shiga cikin damuwa haka ta samu Jumai Tana kuka tana rokanta akan ta Biya mata küdin makaranta da wasu abubuwan da zata tafi dasu garin kano tunda acan suka samu gurbin kararu a makarantar jami ar bayero aman Jumai kiri ta fada mata ita bazata biya mata ba saidai ta nemi kowace hanya ce ta samu ta biya ma kanta aman fa da yawunta ta amince
Huda batayi mamakin abunda Jumai tayi ba kawai dai taji Jumai din ta kara bata tsoro saikace ba daga tsastonta ta fito ba abun Nan na bata tsoro da mamaki
Haka ta gama kukanta ta shiga Tunanin ma fita , karar wayarta ce ta kaste mata tunanin da zurfafa a cikinsa Zee ce ta Kira dan haka ta daga wayar Murya can kasa , hello huda wai ya shirin makaranta zanzo fa muje cafe registration Allah yasa dai kin shirya da kudin ki a hannu ina zuwa tafiya kawai zamuyi Zee da biyu ya fada hakan saboda ta gane ko hudar tasamu kudin wanan karin ma
Girgiza kanta huda tayi kamar Zee na kallonta sanan tace Zee wlh kudin basu samu ba jummai taki bani goje kuwa bansan inda yake ba ballantana ya Bani kawai kije abunki nikam sai wani lokacin ina tunani
Zee ce tayi murmurshin samun nasara sanan tace haba huda karki fadi haka ke kinsan dare baiyi miki ba alhaji UBale wlh yana sonki kuma zai Baki ko nWa ne kike so dan haka ki daina wani fadin magana haka saikace dai ke ba mai kyau ba ae waenda ta Karema ne ba kyau ba abun da zasu siyar sune zasu ce basuda mafita aman dai ke Saidai idan ki cuci kanki ki hana kanki samun farın cikin rayuwa aman ke kinsan kinada mafita wlh huda
Huda ce ta nisa sanan tace haka ne Zee yaushe shi Alhajin zai bani kudin kinsan fa an kusa rufewa. Ae alhaji kina zuwa ma shi baki zaiyi huda bashida wasa dan haka shirya bara na kirashi yan mata
Tana gama fadin haka ta kashe wayar tana murna harda rawa yau dai Allah ya bata sa a ta shawo kan huda cikin Ruwan sanyi kai aman yau saita hada yar liyafa mudin burinta ya çıka huda ta siyarda mutuncinta akan kudi
A take anan Zee ta Kira alhaji ubale aikuwa ta sanar dashi zata kawo masa kawarta kuma sabon hannu ce dan haka nWa zai bata
Dariya alhaji ubale yayi sanan yace zeezee kenan nawa kikeso ke kinsan zan iya bada ko Nawa ne akan sabon hannu dan haka fadi nawa kikeso kanki tsaye
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Cerita PendekYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...