Ramin karya 25

52 1 0
                                    

📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha

WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣5️⃣

Shukura kuwa duniya ce ta bude mata sabuwa da wanan kudin da ta karba a gurin jama a ta dinga Çin duniyar ta da tsinke yanzu bata damu da Aliyu ko ya kawo mata cefane mai kyau ba duk abunda yakawo shi take sarafawa ta bashi yaci abunsa itakuma ta aika yaro ya siyo mata duk abunda take so ta saka a gaba taci abunta tasha lemon gora abunta

Yau kuwa tana Zaune ta na bude status nan ta ci karo da status din ilham tayi hoto a cikin wani katon gida mai kyau kamar gidan shugaban kasa da yaranta ma masu kyau daya bazata wuce shekaru 5 ba daya kuma bazata wuce shekara daya ba sunyi dariya a hotan

Sake zooming hotan tayi tana kallon irin dukiyar dake gidan ga kayan dake jikinta ma lace ne mai shegen tsada ga sarkar gwal a kunenta da wuyanta yastun ta ma zoben gwal ne sunkai guda hudu a jere

Tab Ashe matar nan ba karamin kudi ne da ita ba Kai dole ma nayi kawance da ita wannan itace dai dai Zama kawata Kai kaga wani gida kamar a aljana tab hka dai shukura tayi ta magana ita kadai sanan daga baya ta yanke shawarar kiran ilham a waya dan Sanar da ita gobe tana tafe

Kira daya biyu ana uku ilham ta Dauka ta Kara a kunen ta gamida salama

Amsawa shukura tayi sanan tace kawata ya kike ya gida kwana biyu kin buya

Murmushin yake ilham tayi sanan tace lfy lau ya kike , Lafiya qalau wlh xan fa zo kimun kwatancen gidan ki

Dan jim ilham tayi sanan tace toh shikenan zan tura miki da address din Yaushe zaki zo

Gobe goben nan zanzo kawa shukura ta bata amsa cikeda zumudi

Toh shikenan allah ya kaimu ilham ta fada tana ajiye wayar ko salama bata bari sunyi ba

Ilham na kashe wayar ta ja tsaki Kai banson mutane masu Naci wlh ta fada tana kallon kawarta ruky, me kuma ya faru hajaju ilham ta Tambaya tana murmushi dan tasan halin kawar ta ta

Ke daga zuwa kasuwa na hadu da yar jaraba gashi na kwaso wa kaina jaraba ilham ta fada tana hade rai

Fadamun ni abunda ya faru nidai

Nan ilham ta bata labarin haduwar su da shukura da yadda take kiranta a waya da kiran datayi mata yanzu akan Zata zo gidan

Dariya ruky tayi sanan tace ke haryanzu baki da wayo, ae irin waewnan mutane su business dinmu yake nema, yadda cikin wayo da dabara zamu dinga amfani dasu muna running bussiness dinmu ba tareda samun wata mastsla ba

Ilham cikin rashin fahimta ta kalli ruky sanan tace ruky mama bangane ba what are you trying to say ?

Ruky ce ta nisa sanan tace hala ganin ki Haka living your best life shine ya Saka take kwadayin zama kawar ki toh da irin waenan masu kwadayin ake running busssiness Dinan  da muke yi haba illy wani bayanin basai nayi miki ba yakamat ace kigane

Shiru ilham tayi sanan ta kaima ruky dukan wasa cikin Dariya tace Tabbas maganar ki gaskiya ne a man dai bara tazo din zamu sake karantar wace ita banason ni Muna zaman zaman mu mu janyo wa kanmu fitina shine kawai ya saka ba  kowa nake sakar ma jiki ba

Ruky ce ta gyada Kai sanan tace Hakane illy mussaman mu masu business irin haka muna bukatar sirri sosai dan karda a samu mastala

Illy wai maigidan baya nan ne ruky ta tambayi ilham tana duba agogon dake falon

Ina baya nan ya kuma tafiyar wanan lokacin yace sai yayi 5 months ilham ta fada cikin wani yanayi mai nuna damuwa

Ruky ce tace kice na tataro kayana na dawo tunda dai maigida baya nan

Ilham ce tace aikam you are free to do so you are always welcome mastalata dake kawai daya ne indai kika zo zama sai Kin ta tara mun maza nikuma banso ga shi ki saka mu yita taba kudin sana a

Dariya ruky ta kece da ita sanan tace dadina dake wlh ilham son kudi akwai laifi idan kadan taba kayan ka

Aa ba laifi a man dai kinsani dan riba ake sana a dan haka nikam bazaki dinga saka wa ba muna taba Kayan sana ar mu

Karki damu illy matar senator Yakub tace zata zo kwasar kaya kuma kinsan bata siyan na kana nan yara dole sai alert ya girgiza account dinki idan tazo kedai kawai ki jira tace cikin satin nan zata zo

Ilham ce ta Saki murmsuhi sanan tace Kai Aman naji dadi wlh Ashe da rabon zanji alert mai rikita ni Allah ya kawo ta dan na hango wani gwal wlh ya tafi da imani na

Aikin Kenan siyan gwal ruky ta fada Tana kallon ilham

Naji kekuma fa da kike bawa wani kato kudin ki ni na fada miki wlh jabir samir ba auren ki zaiyi ba idan ma zaki daina basa kudin ki ki daina

Ruky ce ta bata rai sanan tace kinga illy ya isa haka basai kin cimun fuska ba it's enough

Allah ya baki hakuri Ilham ta fada tana janyo wayar ta dan yi ma shukura typing din address din ta

Shukura na zaune taji karar shigowar sakon ilham tana budewa ta ci karo da address din ta a wani estate nan fa shukura ta saki murmurshi dan ta dade tana jiran wanan Ranar da zata je gidan ilham

Danna kiran hafsa tayi akan ko tana gida dan zuwa aron kayan da zata je gidan ilham din

Bayan hafsa ta sanar da ita tana gida ko Neman izinin aliyu batayi ba ta saka hijab ta zura takalmin ta tayi hanyar waje sai gidan hafsa

Tana zuwa kamar kullum gidan a cike mata waenda suka zo hayan kaya sun zo sai zaba suke

Nan itama shukura ta bi layi ta dage ta zabo wani hadaden material Wanda mijin hafsar ya kawo mata wani tafiya dubai da yayi material mai kyaun gaske da tsada

Haka ta shukura ta dauka bayan ta biya sanan hafasar ta saka mata a leda ta mata salama ta tafi gida dan Allah Allah take ta koma karda aliyu ya dawo gidan ya tarar bata gidan ..

**********************************************

Yauma kamar jiya jummai gaba tayi bayan an tashi daga kasuwar, haka badariya da suka dawo aman yau huda ce ta biya da har badariya zata tambayeta inda ta samu kudi saidai kuma ta fasa har kofar gida mai mashin din ya ajiye su sukayi wa juna salama kowace ta shige gidan su

Kai tsaye dakinta huda ta shiga tana Neman in da zata boye sauran kudin da Alhaji garzali ya bata

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now