RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓bookWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣4️⃣A cikin motar hafsa da shukura in Banda Ihu ba abunda suke , hafsa ta Kalli shukura hawaye shabe shabe ga majina nan ta ce wlh shukura kin cuceni ina zaman zama na kin saka ni cikin masatala wayoo wlh ban yafe ba
Shukura ce ta juyo ta kalleta itama hawaye daya na bin daya tace wlh ba wani ni na saka ki dole nayi miki , ae ba dole nayi miki ba ko ta fada tana face majina da mayafjn ta cikeda takaicin abunda hafsa ta fada mata , macen yar sandan ce ta kaste su tace ku criminals ku mana shiru wlh na sake jin bakin ku saina chanza Muku kamani macuta kawai yan 419
Gum su shukura sukayi aman kowace tana zagin yar uwarta a cikin zuciyar ta a haka har suka iso police station din aka fito dasu kowa kowace ido wiki wiki aliyu kuwa kansa ya sunkuyar hawaye nabin idanuwansa yana takaicin irin mastalar da shukura ta saka shi a ciki yana jin zuciyarsa nayi masa radadi Dan haka sake rinste idonsa yyai yana jin zuciyarsa kamar zata fito a haka har aka shigo dasu cikin station din , a cikin station din suka tarar da wasu mata su uku suna tsaye da alama sune suka kai karar shukura kan damfarar da tayi musu nan fa Kallo ya koma Kansu shukura da aka shigo dasu, hajiya rumaisa tace yauwa alhamdulilah an kamo yan damfarar wlh bazan bari ba ku idan zaku yafe shinkenan ta fada tana kallon sauran matan
Haj Bara atu ce tace a bari a zauna ae komai ma zaizo da sauki tunda dai an kama su ae Komai ma zaizo da sauki, aa Bara atu speak for yourself wlh ni ko anbani ku Dina bazan kyale case Dinan ba sai an hukunta su gobe idan akace su kusanci damfara baza su ko ji sha awar zuwa kusa dashi ba bare su aikata dayar matar mai suna habiba ta fada tana hararar su shukura, haka su shukura nagani aka tasa keyar su har cell din mata shikuma aliyu aka kaishi na maza akan sai dpo yazo za a fito dasu Dan tautaunawa akan case din sanan su rubuta statement
A cikin cell din aliyu dafe kansa yayi yana tuna irin halayen shukura da ya saka ya aureta tabbas da yasan shukura zata saka shi cikin irin wanan masatalar da ya nisanta kansa da aurenta kuma ya bawa zuciyarsa hakuri akan Sonta
Wasa wasa dpo bai zo ba har suka kwana a cell dinan maganar irin wahalar da suka sha a cell dinan ma bata baki ne wasu irin sauro ne suke rawar shoki a kan fatar su Wanda suka Hana su koda rinstawa haka suka kwana a xaune cikeda da zallar Dana sani, nan fa hafsa ta hau zagin shukura akan duk Itace ta saka su cikin masatlar, shukura wace ta kawo har wuya Dan takaicin kudinta da kawar Ilham ta bata Samira sanan ga kawosu cell da akayi sauro yana neman halaka su
Wlh wlh hafsa idan baki daina xagi na ba zaki ga abunda zanyi miki , hafsa ce ta sake mata kallon raini da takaici sanan tace wlh shukura bazan Daina cewa kin cuceni ba da baki kawo mana wanan banzan sana ar ta damfara ba za a kawo mu nan ne , cikin daga murya shukura tace kwadayin ki da shegen hadamar ki ce takawo ki nan bani ba ehe ae ba dole nayi miki ba ko kuwa dole nayi miki mijinki yana kula dake aman baki gani ta fada sanan ta maida Kai zata kwanta ko zata samu bacci barawo ya sace ta aman haka tagama juyi ba damar bacci saita fata sauro su dame ta da kuka haka yasa ta xauna tana faman koresu da hanayenta tana tsine ma hajiyar da suka kawo karar su a haka har asuba tayi yadda suka ga rana haka suka ga dare
Da safe ne suka samu suka rinsta aman suna cikin baccin wahala aka zo aka Tashe su nan aka wuce da su office din dpo Dan sauraron case din su , kasa da kanta Shakura tayi Dan kunya gaba daya ta lulube ta bata taba tunanin za a kama ta ba a rayuwarta ta dauka shiennan taci bulus tunda dai tayi blocking din su Ashe akwai sauran rina a kaba
Dpo ne yayi gyaran Murya sanan ya Kalli Shakura da hafsa waenda sunyi wiki wiki da ido kamar zaka ce tak su ruga da gudu , kune madamfarar da aka kawo karar ku ko dpo ya fada yana Kalllon su , hafsa ce ta girgiza Kai sanan tace wlh yallabai itace dai ni wlh kawai a account dina ake tura kudin saita salame ni aman wlh itace nan take shirya Komai Dan Allah a yafe mun ta fada tana fashewa da kuka
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Historia CortaYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...