📒📕RAMIN KARYA
a✍️Written by Khadija mustaphaWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 1️⃣9️⃣Hafsa ce tayi salama gidan shukura , shukura ta amsa tana murmushi Kawata kice daman kina kuşa na Kira ki
Eh mana Ina kusa nazo can gidan ne karbar kaya nace bara na karaso wajen ki na karbi kayana dan nasan halin ki yanzu sai kayan nan suyi wata Baki dawo mun dashi ba
Kedai Bari Kawata wani tashin hankali na saka kaina Ina zaman zaman na
Wani irin tashin hankali ne wanan shukura , Hafsa ta tanbaya tana gyara zama
Wlh Hafsa zuwa nayi gidan sumayah can na arı şarka da sunan zanje siyan irin sa shine fa naje na saka a bikin nan wlh bansan ya akayi ba şarka ta fadi a gurin biki shine fa ta biyo ni gidan nan wai sai na biya ta gashi yanzu mai gidan yaji aman yace wlh saidai na biya shi bazai biya ba
Hafsa ce tace tabdijam har nawa ne şarkar wai Kawata
Dubu arbain fa shukura ta bata amsa
Tab kudin da yawa wai yanzu ke a Ina zaki ga dubu arbain ki bata ne
Uhm Kedai Bari da tunanin da nake kenan aman yanzu na samu mafita shukura ta bata amsa tana nuna mata wayar ta
Bangane ba Hafsa ta fada tana kallon shukura
Bara kiji wani lissafi danayi , kwanaki ba kin siya wani takalmi ba aka damfare ki aka ki kawo miki Karshe ma matar tayi blocking Dinki
Hafsa ya gyada Kai tace tabbas haka akayi mene ya alakanta wanan maganar da damfarata da akayi
Bara kiji Nima abunda zan fara Kenan una ganin sai na fi samun kudin hankalina kwance ke wlh ba karamin kudi zan samu ba
Hafsa ce ta rike Baki sanan tace yanzu shukura waye ya Baki wanan shwarar kuma tayaya zaki yi wanan abun ba tareda an kama ki ba
Kinga wanan laces din ta nuna mata wayarta
Eh nagani yimun cikaken bayani
A manhajjar Facebook nagansa shine na dora a groups groups kuma nasamu masu siya daga masu siyan 2 3 ke harda mai siyan 10 ma shine nace haka zan karbi kudin su kuma naki tura musu kaya nayi block din su sanan idan suka fada ma admin din group din Ana samuna da maganar zance bansan zance ba kokuma itama na tura mata wani abun shikenan a rufe magana
Hafsa ta yi dariya sanan ta kaima shukura dukan wasa
Kai Kawata akwai kwakwalwa daman haka kike da wanna kwanyar aman shine baki kawo wanan bussines din ba sai yanzu
Kedai Bari Hafsa kinsan ni akwai tunani yanzu dai mastala ta daya ne Banida account shine nace daman ki bada naki kinga sai na dinga Baki wani abun
Dariya Hafsa tayi sanan tace ba komai indai wanna ne Ina tare dake dari bisa dari
Yauwa Kawata shiyasa wlh nake son ki sosai yanzu dai fada mun account din na bawa mutanen nan kinga sai a fara business dinan kema ki samu ki salamı mai şarka
Yauwa Kawata shukura ta fada tana gyara zama nan Hafsa ta karanto mata numbern account dinta ta rubuta nan ta tura musu
Suna zaune nan fa alert ya dinga shigowa tun suna kallon abun kamar wasa har saida suka ji alert din kusan dübu dari
Ihu shukura ta saki ta rungume Hafsa sanda suka Kırga kudi dubu Dari cif cif
Shuuura ta kalli Hafsa tace kinga Kawata tashi kije ki ciro mun kudin nan yau inada busha busha wlh
Hafsa ce tayi dariya tace dakata Kawata kiyi a hankula kar ki haukace sabida dubu dari
Kedai Bari Kawata yaushe na taba rike dubu hamsin ma na kaina karki manta fa aliyu naira dubu 20 ya bada sadaki na dole ne na haukace yau dan na samu dubu dari nawa mana
Tafawa sukayi itada Hafsa suna dariya , Hafsa tace bara naje na ciro miki kudin nan Nima a bani nawa rabon nayi gida
Toh Kawata shukura ta fada tana dana wayar ta
Hafsa ce taje ta ciro kudin ta dawo tanata murmushi ta mika ma shukura wace sai Washe Baki take ta saka hannu ta karba
Jujuya kudin ta shiga yi tana dariya Kai Allah mai yanda yaso a duk sanda yaşo yanzu wanan kudina ne ni shukura
Kudin damfara dai Hafsa ta fada tana dariya
Koma dai menene suma ae mutanen basuda maraba da yan damfara din tayaya waenan laces din da sunkai kusan dubu hamsin ko sufi ma za a ce dubu 10 su siya su şunga kayan banza
Hafsa ce ta fashe da dariya sanan tace wanan magana hakane gobe ma sa kuma idan halin su ne nidai bani rabo na nayi gaba bancewa mijina zan dade ba
Toh naji dubu Goma shukura ta kirga ta bawa Hafsa
Hafsa ta kalle ta bayan ta Kırga kudin Kai Kawata dubu 10 kaçal zaki bani
Shukura ta dan bata rai toh dai kinga dai a cikin kudin nan zan salami sumaya ko
Hafsa ce ta tabe Baki sanan tace naji aman wlh wani deal din bazan karbi kasa da dubu 20 ba ni na tafi ta tashi ta tafi bayan sunyi salama akan zasu yi waya ko tsayawa karbar kayanta ma batayi ba dan hankalinta yayi gida
Shukura ta tashi ta shige dakin aliyu ta kirga dubu biyar ta saka masa a aljihun wandon sa inda ta dauki kudi jiya ta fito da sauri ta cire dubu arbain ta saka a rigar ta sanan ta ajiye sauran kudin a cikin jakar ta cike da Murna dan yanzu zata je gidan sumaya ta bata kudin ta bazata ma jira gobe tayi ba dan so take ta nuna wa sumayahr tafi karfin kudin da tazo take mata masifa akai.......
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Historia CortaYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...