Assalamu alaikum
Barkanmu masu karatu da wanan sabon littafin mai suna "Ramin karya " wato nazo Muku da wani sabon salo ne Wanda zai nishadantar daku insha Allah
**********************************************
Wanan littafin bana kudi bane ba sanan kirkiraran labari ne duk wace ta Chanza mun littafi ko ta siyar mun da littafi ban yafe ba ...
📒📕RAMIN KARYA
✍️written by Khadija mustapha
Page 0️⃣1️⃣Aşalın labarin
Garin Adamawa ⚡️Yau tunda ta tashi bata zauna ba tanata aikin Shara da wanke wanke dan dole ne ta yi duka wanan uban aikin ko idan ba haka ba bata da abun kari sanan haka zata daba taje makaranta ko sisi jummai bazata bata ba
Ba tareda da bata lokaci ba ta kammala aikin da tasan dole nata ne sanan ta shiga bandaki dan yin wanka sabida lokaci yana tafiya kuma bakwai ya dan gota
Buhun ta ta dauka Wanda shine soson da take wanka dashi tana mita saidai tana duba kwandon da suke ajiye sabulu ta ga wayam sabulu ya kare
Zumburo baki tayi sanan ta ja tsaki , tana fitowa daga cikin bandakin tayi hanyar dakin jummai mahaifiyar su tana zumburo baki
Daga labulen dakin tayi sanan ta fara magana ba ko gaisuwa
Jummai wai ina sabulu ne naga babu a kwando
Wace aka Kira da jummai ta gala mata harara sanan tace ina Kwana mama huda
Jummai yi hakuri ina Kwana nace ina sabulun ne banason na makara
Nace yana gurin dangin ubanki jummai ta bata amsa cikin masifa
Haba jummai dan me zaki zagi dangin ubana daga tambayar ki sabulu ta fada tana murguda Baki
Iyye akan na zagi mastiyatan dangin ubanki shine kike fadamun wanan maganar huda ta tambayeta
Aa kiyi hakuri nidai ki bani sabulun
Bani dashi kuma Banida kudin siya wlh huda idan Baki kauce mun a nan ba saina Hana ki abinci kuma yau makarntar nan a kafa xaki je marar kunyar yarinya kawai ta fada Tana hararar huda
Huda tasan halin jummai indai ta fadi Abu toh bazata Chanza ba yasa yasa ta sakar mata labulen tana çıka tana bastewa ta nufi bandakin
Tana ji tana gani ta kwara ruwa kawai a jikinta ta fito ta nufi dakin ta
Vaslin ta dauko ta shafe jikinta da shi sanan ta dauko uniform dinta daga Karkaahin filo Wanda tayi ma tashi da shi ta hau saka wa ta janyo takalminta Wanda duk ya lalace ta saka tana mita a ranta
Ta rasa wanan maqo na jummai tana da kudin siya mata sabon takalmi aman tana ganin ta da wanna takalmin aman ta ki sauya mata uniform dinta ma duk yasha paci aman haka jummai take kallonta bata damu ba
Leda ta dauko Wanda shine a maxaunin jakar makarantar ta ta nufi dakin jummai
Jummai ina abinci na ta fada Tana kallon ta, hmm abinci gadai guntun biredi nan ki dauka akwai ruwa a randa ta wulo mata naira 50 ga wanan kudin tarar ki ne sai kin dawo saura idan an tashi ki biya kwadayi wlh dole kizo ki same ni a bakin kasuwa da wuri idan ba haka ba , saidai ki wuni da yunwa yar iskar yarinya kawai
Hüda wace hawaye ya ciko mata tayi shiru sanan ta dauki guntun biredin da ko jariri aka bawa bazai ishe shi ba , shine aka bata ita taci bayan Jumai bata bata ko abincin dare ba tun awarar da wani ya bata lokacin da taje karbar kudin shinkafa da waken da ya siya ...
Tana gama ci ta dauki kudin da jummai ta jefa mata tamata salama ta fita tana goge hawayen dake sintiri a kumatun ta
A hanya kuwa sai tunani take ta gaji da tambayar kanta shin jummai mahaifiyar ta ce ko kuwa dai ita din yar ruko ce Kai kowa cewa yake yasan lokacin ma da jummai ta haife ta toh meyasa take mata haka haka dai tayi ta tunani har ta karaso titi ta samu abun hawa ta hau dan zuwa makaranta ....
Kuyi comment dan nsan labarin yana Muku dadi ko baya Muku dadi
Mrs abba ❤️📒
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Короткий рассказYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...