Ramin karya 26

29 0 0
                                    

📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha

WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣6️⃣

Shukura ce kwance a Daki tana tuna karyar da Zata shararawa Aliyu ya barta ta fita taje Gidan Ilham bata so tayi karya da yan Gidan su saboda ta San Aliyu Zai iya kiran su Dan jin maganar dan Haka ta shiga tunanin karyar dazatyi masa can dabara ta fado Mata dan haka tayi murmushi

Tana murmushi tana tuna plan din data shirya taji shigowar Aliyu Gidan dan haka ta kankame bargon Tana rawar Sanyi na karya tana dan kuka ciki ciki

Salama Aliyu yayi ya shigo dakin Ganin shukura kwance tana rawar sanyi ya Saka salamar ta yanke a bakin Sa ya Karasa gadon yana kiran sunanta

Shukura shkuruka meya sameki Aliyu ya fada yana janyo bargon da Shukura ta lulbuba dashi

Kaina ne yake Aliyu kuma sanyi nake ji sosai dan , ta fada tana sake janyo bargon kamar dagaske batada lafiyan

Tahsi Muje chemist toh kinji maza Tashi Aliyu ya fada yanna Mike wa tsaye, da Sauri Shukura tace aa Aliyu banzuwa chemist ni asibiti nake so naje ban yarda na want chemist ba ta fada tana girgirza kanta

Shukura Kalli time Sanan kice mu tafi asibiti wa zamu Samu a irin wanan lokacin kiyi hakuri Kawai muje chemist din kinji

Aa nifa bzan je wani chemist ba hankalina yafi yarda da asibiti ni gaskiya

Kallon shukura Aliyu ya tsaya yi cikin mamaki dan tunda yake da ita bata taba cewa saidai ya kaita asibiti ba chemist sake Zuwa duk wani rashin lfy da yake damun su Aman yau yana mamakin maganar shukura na Kin yarda yakaita chemist

Girgiza kai Aliyu yayi sanan yace yanzu so kike na saka ki a gaba Ina kallon ki har safe sanan muje asibitin kome kike so

Gyada Kanta tayi alamun eh tana sake kankanme bargon , gyada Kai Aliyu yayi sanan yace toh shikenan bara na baki ko paracetamol ne idan ya so gobe munje asibitin Allah ya baki Lafiya sannu kinji

Gyada Kai Shukura tayi tana kallon Aliyu har ya fita debo Mata ruwa sanan ta yi Saki Dariya a hankali Kasa kasa dan kar Aliyu ya jiyo ta tana sake gyara kwanciyarta

Bai jima ba Sai gashi ya dawo dauke da ruwa a kofi ya nufi inda suke ajiye Magani ya dauko Mata paracetamol ya dawo inda take kwance yana kiran sunanta

Da kyar ta amsa ita dole Mai rashin lafiya sanan ta Mike ta saka Hannu ta karba maganin sanan ta faki idonsa ta saka a karkashin pillow ta sha ruwan kamar wace dagaske maganin ta sha ta dan bata fuska dan Shukura idan akwai abun da tsana a rayuwar ta toh magani ne idan batada lfy ma da kyar take sha bare yanzu data kirkiro wa kanta cutar karya

Sannu Aliyu ya shiga jera Mata sanan ya Mike ya gyara Mata kwanciya shima ya yo shirin kwanciya ya kwanta kusa da ita yana sake jera Mata sannu

Tabe baki tayi tana tunanin da ace yanzu shi wani mai kudi fa haka zai fita ya siyo Mata gashashan kaji da yoghurt yana lalabata yana bata a baki Aman shi ya wani cika ta da sannu dadinta ma daya kirkirar rashin lafiyar tayi da abun ya fi Mata ciwo ma

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now