RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustaphaWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣9️⃣Rayuwar huda kuwa ta sake zama abun tausayi dan yanzu sai jummai tayi sati bata bata abimci ba dan haka take biyema yaran kasuwa suna bata na kashe wa aman har yanzu bata yarda ta sakar ma wani jikinta ana haka ne kuma fa Alhaji garzali ya fito da abunda yake zuciyarsa aikuwa huda taki amince wa nan fa yace saidai ta biyasa dük wani kudi ya yake bata nan fa huda tayita rokansa akan ita batada hanyar dazata biyasa kudin sa
Nan Alhaji garzali ya hasala yace saidai ta zabi daya ko ta biyashi da jikinta ko kuma ya bata kwana 5 ta nemo masa kudin sa ta başa ko ya saka a daukota har cikin gidansu kuma yayi abunda zai yi da ita dan shi baya kyauta saida dalili mai karfi wanda zai amfane shi sosai , Tashin hankali iya tashin hankali huda ta shigeshi dan haka ta rage walawala kullum cikin damuwa take da tunanin inda zata samu kudin alhaji garzali ta biya shi dan tasan zai Aikata abunda yace
Data samu jummai da magnanar bayan ta sanar da ita komai da ya faru dan jummai din ta biya alhaji garzali dan ita bazata iya aikata abunda yake so ba jummai tsayawa tayi kallonta na dan wani lokaci sanan tace yanzu ke wanna yarinya har yau she alhaji ya baki irin wanan kudin aman sabida ke muguwa ce shine kika ki nuna mun Bare Nima nace yau dai ni jummai Naci arzkikin ya ta haihuwa tayi mun rana aman gaskiya huda ke muguwa ce yanzu me kike so nayi miki Dani kikaci kudi da kike so na tayaki biyan kudi ko yaya ta fada tana kallonta
Girgiza Kai tayi sanan tace ba komai , jummai ce tace shikenan ae nidai sisi banci ba dan haka bazan biya ba inma ki kai masa kanki tunda wuri ko ki nemi kudin sa ki bashi tün kafin ya saka a kamo masa Ke yayi abunda zai yi dake ni ba damuwa ta bace ba kidahumar yarinya kawai tana gama fadin haka ta Mike tayi daki abunta tana mita , a ranar huda kasa rinstawa tayi saboda damuwa da tunanin inda zata samu kudin alhaji garzali, a haka har bacci yayi gaba da ita tana ta mastawa kwakwalwarta da tunani kala kala
Washe gari a makaranta bayan sun fito break shiru tayi Tana tunanin Mafita su Pretty sun Lura da Halin da take ciki dan haka prettty tayi Gyaran murya ta dafa ta a kafada tace huda wai lafiyan ki kwana biyu gaba daya fa kin chanza meke damunki ne haka , numfashi ta ja sanan tace wlh pretty ina cikin mastala kusan dai halin da nake ciki na rashin kulawa a gida shine fa na hadu da wani alhaji a kasuwa yake bani kudi nake samu nake siyan abinci da dai wani abun rayuwa yanzu kawai kwastam yace wai saina yarda dashi danace aa wai shine sai dai na biya sa kudin sa kuma ko kuma ya saka dole dole a dauko ni wlh pretty Ina cikin wani hali sosai
Zee ce ta rike baki sanan tace tab wanan babar magana ce wlh , aman ke meyasa baza ki yarda dashi ba tunda dai ya nuna shi ga abunda yake so ko Bashida kudi ne , girgiza Kai huda tayi sanan tace tab wlh ni ba yar iska bace ba kuma bazan fara a kan wanan tsohan ba ya İsa fa ya haife ni haba me kike fadi ne haka zee
Zee ce ta bata baki sanan tace badai yanada kudi ba ae magana ta kare ni wlh I don't care ki gani nan da nice da magana ta wuce dan yanzu idona ya bude dan haka magana shine kawai ki bada kai bori ya hau babanki ne
Aa Zee wanna ba magana bace ba pretty ta fada tana kaste Zee , dük rashin ji na I won't stoop so low da dating baban mutane this is not nice at all wlh , kinga huda karki yarda dashi wlh ni bazan baki wanan shawarar ba gaskiya , nasan ina dan rashin ji na aman I don't deal with old men sabida banason ayima baba na haka dan haka bazan so hakan ba gaskiya huda , Zee ce ta ce toh ke pretty da kike wanan maganar ae ba babanku bane ba so ni banga wani abu anan ni idan nice ma saina kuma karbar wani kudin mene a ciki , tsoho da kudi fa yaro ,
Pretty ce tace eh Zee zaki ce mana haka tunda ba baban ku bane ba ko
Shima fa da ake maganar nan fa baban wasu ne fa , Zee ce tace aa pretty a ina za a ga baban namu ni gaskiya banson wanan abun
Ni dan Allah karku fara wani rigima akan wanan maganar huda ta fada tana kallon su da fuskar tausayi ,
pretty ce tace yanzu wai nawa ne kudin ma da Aketa magana akai pretty ta tambayi huda , idan zan iya Tuna wa ya kai kuşan dubu hamsin fa dan har kudin jarabawa shine ya biya mun , pretty ce tace okay gaskiya da ki biyema sa gwanda na baki kudin dan haka zan baki kudin ki başa kawai gaskiya because ni bani yarda da irin wanan mutanen gwanda Clean boys kamar wanda muke kulawa aman manyan nan I don't trust them at all wlh pretty ta fada tana bata fuska
Huda cikin mamaki ta shiga yima pretty godiya itakuwa Zee batayi magana ba saima danna wayarta data cigaba da yi dan taso hüdar itama ta fada irin rayuwar da suke dan su zama daya , a ranar kafin su rabu pretty ta bama huda kudin sanan tace ta shiga mota sai su ajiye ta a rumfar jummai , dan yauma itada Zee sunada birthday a wani joint na manyan yara da suke harka dasu
Suna shigowa kasuwar kuwa pretty ta hango alhaji garzali da wata mai fura sai Washe mata baki yake itakuma sai wani sunkunyar da kai take da alamu zance dai suke yi , pretty ta ja tsaki sanan tace kalli dan Allah friends wai waenan manyan mutanen daga gani suke lalata yaran mutane ku kalli yadda yake flirting da yarinyar da wanan yayi jika ma da ita aman kalli abun so irritating ta fada tana bata rai , juyowar da huda Zatayi idonta ya sauka akan alhaji garzali ta kalli pretty tace wai da wanan mutanen kike ta nuna shi
Eh mana shi fa kali fa yadda yake flirting da mai fura ko kunya baya ji , Zee ce ta dago dan tunda zu tana kan wayar ta ne bata kalli wanda pretty ke nuna musu ba , gaban Zee ne ya yanke ya fadi da ganin alhaji garzali, huda ce tace ae wanan pretty shine wanda nake Baku labari shine yake bani kudi kuma yanzu yake mun wanan maganar ta fada tana nuna shi
Zee ce tace wanan mutumin ta fada a razane tana dafe kirjinta da gaba daya taji yayi mata nauyi , eh kwarai kuwa shine wlh huda ta fada tana kallon Zee , Zee ce tace Innalilahi daman abunda baba yake yi kenan , baba kuma pretty da huda suka hada baki a lokaci guda , Zee ce ta maste hawaye cike da takaici zuciyarta na mata daci tace wlh wanan babana ne alhaji garzali, yanada arziki aman bai San cinmu ba bare Shan mu , bare wani sutura dük shine ya saka na fada wanan halin aman Ashe wasu yake kashe wa kudin kai Innalilahi kawata baba na sai kuka ya kubce mata nan ta shiga rera wa tana ajiyar zuciya
Huda da pretty suka kalli juna cikeda alhini sanan su ka sake kallon alhaji garzali wanda shi bai ma San suna kallon sa ba sabgar gabansa yake shi da yar fulani abunsa ...
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Cerita PendekYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...