Ramin karya 12

23 1 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 1️⃣2️⃣

Wayar aliyu ne ya shigo wayarta ae babu shiri ta Mike zaune tana dafe kirjinta , wuyanta ta shafa saidai ji yayi wayam alama babu sarka a wuyanta , shafa wuyanta tayi a karo na biyu , saidai har yanzu wayam kirjinta yayi wani mumunar bugu ta dafe Kai Tana Jin kanta yana sara wa

Nashiga uku ya akayi sarkar wuyana ya fadi nashiga uku ta fada tana shafa wuyanta

Shamsiya ce ta Lura da Tashin hankali a fuskar shukura dan haka ta masto kusa da ita sabida ba ji ake sosai ba sabida karar sautin kida dake tashi

Meya same ki shukura lfy kike kuwa ta dafa ta tana Jero mata tambaya

Wayar aliyu ce ta kuma shigowa a karo na biyu ta kalli wayar ta hadiye wani yawu mai daci sanan ta kalli shamsiya kamar zatayi kuka

Wlh shamsiya banga sarka ta ba bansan ya akayi ta fadi ba

Innalilahi ya akayi haka shukura

Wlh bansani ba Nima yanzu naga ni babu a wuyana wlh shamsiyya sarka na mai tsada ne bansan yadda Zanyi ba idan ya bata ta fada idonta cike da hawaye

Abu baiyi dadi ba shukura Allah ya mayar miki da alkhairi duk da dai nasan wanan karami ne a cikin sarakuna nan ki ae Ina ganin ki da gwalagwalai da suka fi wanan karki wani damu Kawata

Shukura ji tayi kamar ta kwada ma shamsiya Mari Akan abunda ta fada aman saita dake dan tabbas sunsha haduwa da shamsiya a bikin kawayen su , kuma duk biki a gurin hayar gwal take haya ta saka shiyasa har shamsiya ta fada mata haka

Nagode shamsiya bara nazo na tafi gida shukura ta fada tana tashi tsaye bata reda ta kula kowa ba ta fita daga hall din

Ta jima tana neman abun hawa ga aliyu shima da ya takura mata da waya gashi takasa dauka sabida idan ta dauka zai gane da ta fita daga gidan ita dai yau fita batayi mata dadi ba

Ga satar sarkar summayah da akayi gashi ba daman tayi cigiya sabida ta nuna wa kawayen ta tafi karfin sarakar

A haka har ta samu abun hawa ko ciniki bata tsaya yi ba sabida rikicewa ta hau ta shiga tana ta tunanin abunda zata tarar idan taje gida dan har yanzu aliyu bai daina kiranta ba a waya , ga sarkar sumayah da aka sace

Sunzo unguwar su mai adaidaita sahu ya faka a bakin titi yace shi bazai shiga ciki ba ta sauko ta salame sa zai tafi

Mita ta shiga yi sanan ta fito daga napep djn ta saka hannu a jaka zata dauko kudi ta bashi

Wayam taga jakar Tata sai wasu tarkacen kayan kwaliya

Tuna wa tayi da fa ta like duka kudin ta a filin rawa nan take zuciyarta ta buga ta kalli mai napep ta kalli jakar ta

Nashiga uku ni shukura wanna wani irin masifa ne ta fada a hankula

Hajiya kin barni ni a tsaye ni dallah salame ni na wuce abuna mai dan sahu ya fada yana kallon ta

Dan Allah Mallam kayi hakuri ka shiga Dani ciki sai na karba na Baka wlh na manta babu kudi a jakana

Kutumar uba ni zaki ce ma , ni zaki hawa wa addaidata sahu ba kudi sabida kin raina ni

Daman nasan irin ku makaryata ku saka kayan aro ku dinga karya a gari yanzu sabida kin Raina ma kanki hankali zaki hau mota bakida kudi toh wlh kalleni nan kudina dubu 1 ne kuma wlh sai kin bani zaki bar nan

Kallonsa shukura tayi ta saki wani ashar yanzu Mallam sabida sata zaka ce mun kudinka dubu daya daga can zuwa nan wlh idan ba baka Dari 300 ma ka godewa Allah kuma maganar da kake bani da kudi ni bana yawo da cash ne shiyasa har hakan ya faru dan haka Karka fada mun maganar banza

Ke dakata mun Mallama mai dan sahu ya fada yana fitowa daga mashin din , mayafin jikinta ya fişge ya nanade a hannun sa ke bani dubu na ko na wuce da gyalen ki

Nashiga uku mallan nifa matar aure ce ya ka bani ma yafi na shukura ta fada tana kare jikinta da hanayenta dan dinkin ya dan fito da surar jikinta

Idan kinga na Baki mayafin nan wlh kin bani kudi na ne batareda naira biyar Dina tayi ciwon Kai ba

Nace maka ka dauke ni na kaini ciki zan baka kudin ka Mallam shukura ta fada tana kallonsa yanzu kuma gaba daya tsoro da kunya take ji wani Wanda ya Santa yazo wuce wa ya ganta ba mayafi suna rigima da mai dan sahu

Bata mayafin ta Mallam Mallam umar Makocin su shukura ya fada lokacin da yazo wucewa yaga mahawar da mai adaiduta sahu suke shi da shukura

Aa Mallam saifa ta bani kudina sanan zan bata mayafin ta kai ko wanann  matar Baku isa ku bude mun ido ba na  bata

Kaga Mallam nace ka bata umar ya maimaita masa yana kallon shukura da ta saka hannu ta kare jikinta

Kudina za a bani Mallam sanan na bada mayafi ya fada yana kallon umar

Nawa ne kudin naka umar ya fada Tana kallonsa

Dubu 1 ne

Dubu daya ya zaro daga aljihun sa sanan ya mika ma dan sahun yana bin jikin shukura da kallo

Mayafin ta ya wulo mata sanan yaja tsaki ya shige Adaidata sahun sa ya bar wajen

Shukura kuwa yafa mayafin tayi sanan ta shiga yi ma umar godiya shikuwa ya kafe ta da ido yana ta kallo dan ya dade yana yaba kyaun shukura aman bai samu fuska ba sai yau kuma daya ganta ba mayafi yaga irin dirin ta gaba daya ji yake kamar ya hadiye ta dan ta tafi da imaninsa

Ba komai fa ya fada yana sosa Kai sanan ya saka Kai ya bar wajen itama gıda ta nufa tana ta godewa Allah da Allah yakawo mata umar da ya zatayi ta tafi gida ba mayafi Kai yau dai kwata kwata bata fito da sa a ba

Tana ta tunani a haka har ta isa gida tana zuwa ta tarar da aliyu a kofar gida tsaye ya harde hanayensa ya hade girar sama da kasa nan take gabanta ya shiga bugawa shikenan yau kam tasan tana çıkin tashin hankali ...

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now