📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 1️⃣5️⃣Kallon bayan sa tayi da harara taja tsaki , mts wlh ni na gaji mutum sai jaraba komai kayi ace sai anyi magana tana gama fadin haka ta Mike tsaye ta hau gadon ta tayi kwanciyar ta gamida janyo wayarta
Kiran sumayah ne ya kuma shigo wa a karo na biyu ta ja dogon tsaki tana kifar da wayar mata sai Naci sabida an ari sarkar ta ni wanan jaraba har Ina ta fada tana jan wani dogon tsakin har yafi na dazu Kara ma
A haka dai bacci yayi gaba da ita sai Kiran sallar asuba ne ya tashe ta ,
Da safe aikin gidan ta fara ta Dora Karin kumallo tana gamawa tayi wanka ta zauna ta karya ko duba aliyu batayi ba acewarsa idan ya gama fushin ya sauko dan kansa dan fita ce ta Riga da tayi ta babu abunda zaiyi Akan hakan
Tana wanke kwanunka data gama kari taga aliyu ya fito da shirin sa na zuwa gurin facin sa fuska a daure
Ina Kwana ga abun Karin ka fa ta fada tana kallon sa
Bana ci ya fada a takaice
Shikenan a dawo lafiya ta fada tana kauda kanta gefe
Bai ansa ba ya fita daga gidan bayan ya ajiye mata dari biyu akan tanki yayi gaba abunsa
Oho dai abinci kuma Naci anjima abuna ta cigaba da wanke wanken ta abunta
Sallamar sumayah ne ya kaste mata wanke wanke da take zata tashi Kenan ta güdü daki taji sumayah na magana
Yanzu shukura sabida rashin kirki zaki dinga ganin wa yana aman ki share toh gani nazo da kaina a bani şarka na yar gidan dan tata
Hade rai shukura tayi sanan tace haba sumaya haka ake banko wa mutane gida da kin tarar da MIJINA ba fa nifa banson haka
Tsaki Sumayya tayi sanan tace ke banson iskanci ya za ayi ki arı abuna da sunan zaki je siyon irin sa kawai naganshi a kunenki kinje biki dashi haka mukayi dake
Wani Muna Fikin ne yace na saka sarkar ki Sumayya ? Shukura ta fada tana zare idanuwa
Ba wani munafikin daya fada mun idona ne ya fada mun
Idon ki kuma shukura ta fada Tana Zara idanuwana
Eh Sumayya ta fada tana bude wayarta hotan shukura ta fito dashi Wanda taga ni jiya shamsiya ta Dora a WhatsApp dinta kuma abunda ya saka ta gane şarkar tace sarkar ta dan lankwashe dan haka dashi take gane natan
Tun jiya data ga ni a status din shamsiya ta yita kiran shukura aman taki dauka kuma dare yayi data fito tazo gidan shiyasa yanzu ta na gama abunda take yi ta Nemi izinin mijinta ta fito dan kar anjima yayi tazo bata sami shukura ba
Shukura ce tayi shiru tana sosa Kai tama rasa abunda zata ce ma sumayh duk karyarta ta kare tunda sumyah ta gane sarkar tace ta saka
Kinga idan zakiyi rayuwar karyar ki kije can kiyi , mijinki yana faci aman ke kin dauki karya kin dorawa kanki kına hada kanki da mu toh bara na fada miki bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane ba ko ance miki Bamusan karya kike ba ba abunda kika hada da dan tata aman kike mana karya
Dan haka kije ki dauko mun şarka na daga yau karda na sake ganin kafarki a gidana kiyi naki rayuwar nayi tawa rayuwar
Shikenan shukra ta fada Tana kallon sumayah ta yi hanyar daki gaba daya jikinta yayi sanyi
Dakin ta tashiga ta je inda ta ajiye dan kunen da abun hanun da şarka
Tagumi tayi tana tunanin bayanın da zatayi ma sumayah Akan batar şarkar ta
Ta dora hannu a kanta Tana Dana sanin karbar Aron sarkar
Muryar sumayah taji daga tsakar gida tana magana cikin masifa
Wai yanaji shiru ne a fito a bani abunda mana ko na shigo dakin wlh
Ajiyar zuciya shukura ta sauke sanan ta fito a hankula tana tafiya kamar wace Kwai ya fashewa a ciki
Bani abuna sumayah ta fada tana mika hanunta
Gashi sumayah aman an samu masatala
Mastala Mastala sumayah ta maimata sau biyu tana daure fuska
Eh wlh sumayah wlh bansan ya akayi ba sarkar ki ta fadi kinga Saura dan kune da abun hannu da zobe dan Allah kiyi hakuri
Kutumar uba sumyah ta fada cikin karaji wlh wlh shukura bazan yarda ba sai kin biya ni
Ni zaki kalla ki siyarda şarka sanan kice mun wai ya fadi baki san yanda akayi ba nayi miki kama da marar hankali
Dan Allah kiyi hakuri sumayah dan Allah
Nayi hakuri na tafi ba şarka idan MIJINA ya tambaye ni Ina şarka sainace masa uwar ki kome sumayh ta fada cikin masifa
Haba sumayah mene na zagin uwata akan şarka
Ke rufe mun Baki an zaga din mastiyaciya wlh bazan bar gidan ba sai kin fito mun da şarka ta ko kuma ki rike sauran kayan ki bani kudina ehe
Nashiga uku sumayah a Ina zan samu kudin şarka na Baki wlh Banida kudi sumayah shukura ta fada muryata na rawa
Sai fa kin Nemo wlh dan ni bazan yarda ba fa kije duk inda zakije ki Nemo mun abuna da kinsan da bakida kudin şarka kika je kika yar mun gani doluwa anan kızo kice mun şarka ta fadi na ce na hakura ko toh wlh Baki isa ba karyar ki tasha karya yar rainin hankali
Sallamar aliyu ne ya Hana shukura magana ya kalle sumyah dake tsaye ta rike kuğu ya kalli shukura da tayi wuri wuri da ido gabanta na faduwa dan tasan yadda suke da aliyu idan yasan da maganar kashin ta ya bushe
Daki ya shige ba tareda da yace komai ba daman ajiyar da abokinsa Musa yabasa ne yazo dauka dan haka Kai tsaye rigar da ya cire ya nufa ya saka hannu a aljihun zai dauki kudin
Wayam yaga ni dan haka ya saka hannu a dayan ma shima babu komai
Nan gabansa ya fadi ya sha ajiye kudi masu yawa wasu nasa wasu na ajiya aman bai taba nema ya rasa ba ya akayi wanan ya nema ya rasa
Aa aliyu ka sake duba Kayan naka wata zuciyar tace masa dan haka yayi na am ya shiga laluben aljihun rigunar sa da wanduna aman wayam ba kudi ba alamun su
A waje kuwa shukura nuni tayi ma sumayh da hannu Akan tayi shiru dan Allah bata so aliyu yasan da maganar
Sumayah kuwa harara ta jefa ma shukura sanan tace zan dawo wlh aman wlh sai an Biyani dai dai nan aliyu ya fito daga dakin kuma yaji maganar da sumayah ta fada
Me za a biya ki baiwar Allah aliyu ya fada da kaukausar murya
Shukura ce tayi daburce cikin inda inda tace ba komai fa
Bada ke nake ba aliyu ya fada fuska a daure
Ya dawo kallonsa zuwa ga sumayh yace bai war Allah nace me za a biya ki
Daman şarka ce matar ka ta ara da sunan zata je kasuwa siyan irinta shine ta saka har şarka ta bata shine nazo karbar kudin abata
Şarka aliyu ya fada yana kallon shukura
Sunkuyar da kanta shukura tayi zuciyarta na buga wa kamar zata fito dan bazata iya kallon kwayar idon aliyu ba dan tasan daga muryar sa ma ransa a bace yake ..........
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...