RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓bookWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣6️⃣Mama Sakin baki Tayi tana mamakin abunda shukura tayi mata wani hawaye mai zafi ya sauko mata cikin dabara ta goge tana dafe kirjinta
Daki ta shiga sauran kanen shukura suka bita suna bata baki dan kuwa gaba daya jikinsu yayi sanyi da abunda shukura ta yi ma mahaifiyar tasu
Wlh indai nice mahaifiyarki shukura zaki dawo kina dana sanin rayuwar da kika dauka ma kanki mama ta fada tana hawayen bakin ciki
Mama dan allah kiyi hakuri hindatu tace tana hawaye itama, hindatu dole na zubar da hawaye duk wata uwa tana farin cikine idan yarta tadau hanyar arziki ba na banza ba aman kalli hanyar da yar uwar ku ta dauka ku kunsan dole akwai dana sani komai daren dadewa
Hakane mama aman dan allah kidaina wanan kukan kinji kibar aunty da duniya rudin tane take dawainiya da ita kuma insha Allah Zata dawo tana dana sanin abunda ta aikata
Shikenan hindatu Allah yayi muku albarka mama ta fada tana goge hawayenta,
Da Amin suka amsa sanan suka yi shiru kowa na saka abubuwa cikin zuciyar sa
.......................................
Corper Faisal kuwa tunda yakoma sukayi wanan rigimar da hajiyarsu ya kasa sukuni dan kuwa baisan yanzu abunda Zai Sanar da huda ba dan kuwa yayi mata alkawarin aure sanan daga nan ta cigaba da karatun ta yanzu gashi haj ta wargaxa komai akan huda baya ganin Zai iya sabawa da mahaifiyarsa dan kuwa yana matukar son ta fiye da komai a rayuwar sa dan haka ya kasa ma kiran hudar a waya tunda ya bata karamar waya kafin ya bar garin itama kuma idan takira baya dauka Hakan kuwa ya saka huda cikin damuwa killum kuma saita kira aman haka wayar zata karaci karar ta ba a dauka
Yau kamar kullum wayar huda ce ta tashe shi haka aman yana gani yaki dauka saidai yau kiran ta daban ce dan kuwa ta kira a kalla zaikai sau goma duk a lokaci da bai fi miniti 5 ba dan haka ba shiri ya dauka batareda yace komai ba
Nauyayen ajiyar Zuciya huda ta saki sanan tace hello faisal alhamdulilah yau kaine ka dauki wayata Haba faisal menayi maka haka ta fada da Murya kamar zata saki kuka
Kiyi hakuri huda Faisal ya fada muryarsa na rawa, ni baka mun laifi ba faisal kawai ni ka fada min dalilin ka na kin daukar waya inata kiranka
Huda kinajina ko Faisal ya fada yana lumshe ido dan yau kawai yana ji zai yanke alakarsa da huda kamar yada mahaifiyarsa ta nema dan yanzu ko ansa gaisuwanta bayayi dalilin maganr huda dan haka bazai iya zaman doya da manja ba da mahaifiyarsa
Huda kina jina ko ya kuma fada a karo na biyu haryanzu idonsa a rufe, inajinka faisal huda ta fada zuciyarta na harbawa, muyi hakuri da juna huda mahaifiyata taki amincewa dake pls karki dauka a ranki na yaudare ki ne aa huda banyi hakan ba dan yaudara wlh
Faisal menayi maka zaka yi was a da zuciyata haka kai kasan kuwa yadda nake son ka ko ka manta da alakwarin da kamun ko daman duk dadin bakine naku na maza huda ta fada tana maste hawayen dake zubo mata
Aa huda ba haka bane ba wlh mahaifiyara ce taki yarda da maganar aman wlh ke kinsan ina matukar sonki kuma banida buri da ya wuce na tainaki rayuwar ki
Hmm faisal kenan kayi was a da zuciyata Wanda bantaba tsanmanin haka daga gareka ba aman ba komai nasan dalilinka nakin aurena shine dan ni ba kowa bace ba kuma wanan dalilin na Guda tun farko naki amince wa da soyayar ka kenan aman ka nuna mun na komai bane ba ashe kai shigo shigo ba zurfi kamun faisal nagode aman kasani ka cutar dani wlh kasani muma bamu muka halici kanmu ba a talakawa dan munzo a wanda basuda karfi bamu zamo abunda masu kudi zasu na wulkantawa ba har ace baza a aure mu ba dan kawai Allah ya halice mu a talakawa , kuna saka wasu daga cikinmu fadawa cikin halaka muma mu saka burin Tara abun duniya ko hakan zai saka mu auru muma dan muji dadin rayuwar batareda an tsangwamemu ba saboda Allah baiyi mana arziki ba
Wasu dayawan mata rayuwar su ta baci garin Neman kudi dan rufawa kansu asiri suma a Dama dasu wasu har ketara kasa suke sutafi can dan Neman kudi wasu garin larabwa a hakan wasu dayawan yan Matan suna fadawa ne a hanun ba ta gari rayuwarsu ta lalace garin neman gira kaga an rasa ido kenan aman ba komai Faisal nagode da cutar da zuciyata da kayi
tana gama fadin hakan ta ka she wwayar tana kuka mai cin rai
Faisal shiru yayi har huda ta ka she ya rinste idonsa yana jin kamar zuciyarsa zata fito yana so ya sake kiran ta aman toh baisan mezaice mata ba haka ya dafe kansa yana nazarin maganganun data gama fada masa wanda hakan gaskiyane ba karya a maganganun nata aman fa baya ganin zai iya tsalake maganar mahaifiyarsa duk da maganar ta shiga jikinsa
Yau sati daya kenan da faruwar hakan huda haka Tasha kukanta ta godema Allah ta saka ma ranta dangana tana Taya jummai siyarda abinci dan kuwa maganar cigaba da karatu ta waste tunda Daman Faisal ne yayi mata alkawarin nema mata makaranta yanzu gashi ya Rabu da ita tasan jummai ba biya mata zata yi ba dan haka ma bata saka ma ranta samun taimakon jummai din ba haka ta dauki hakuri da dangana ta saka ma ranta
Zee kuwa farin ciki tayi bayan huda ta sanar da ita abunda ya faru aman bata nuna mata ba , aman cikin ranta fari kal dan kuwa bata son cigaban hudar kwata kwata tasan idan huda ta auri faisal tabbas rayuwarta zata yi kyau ga kudi ga ilimi kai itakuma ta siyarda da mutucinta a titi kuma ba mijin nunawa a gari sai duk yan iska wanda suke lalubeta su bata kudi wasuma guduwa suke suce zasu bata kuma daga baya taji shiru
Dan hakan tayi alwashin hanyar da tabi dole itama hudar tabita su lalace tare to aman tun kafin rasuwar zee taso hakan aman takasa samun abunda take so dan haka taci alwashin tunda yanzu ba zee saita san yadda tayi ta janyo huda cikin harkar tasu dan gaba daya ayi mutuwar kasko
Mrs abba
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...