RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustaphaWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣7️⃣Hannu ta dora akai ta ce nashiga uku ni shukura yau me yake shirin faruwa Dani ne wai , dube dube ta shiga yi aman har yanzu ba mahaluki daya da ta gani gashi Ruwan sai kara karfi yake , mayafin ta taja ta şaka fuskarta a ciki ta dauko wayarta tana sake kiran ilham aman shiru har ya kaste , tana faman mayarda wayan cikin jaka aikuwa waya ta subuce ta Fadi kasa nan kuwa ruwa yayi gaba dashi , ihu ta saka tana bin wayar tana ganin yadda take gudu cikin ruwan aman bata damu ba , batayi aune ba taji ta ta fadi a kasa nan ma ko a jikinta ta tashi ta cigaba da bin wayar har tayi nasarar cafko ta dan haka ta tsaya tana mai da numfashi
Yanke hukunci tayi kawai ta koma gida tunda dai ruwan yaki tsayawa gashi jikinta gaba daya a jike , tsaki ta dinga ja tana tafi ya harta iso bakın titi , bata wani sha wahalar neman abun hawa ba ta samu bayan ta masa kwantance unguwar su wato gidan iyayenta
Har kofar gida mai dan sahu ya ajiye ta sanan ta fito ta bashi kudin sa ta shige gidan yanzu kuwa har ruwan ya tsaya yayafi kawai akeyi
Tana shiga a rumfa dake tsakar gidan ta samu kaninta suna zaune suna ganinta suka fara darıya ah ah shukura dantata suka fada a tare dan dashi suke tsokanar ta kasancrwar ta mai karya da wai ita yan gidan su dan tata ne , hararara ta buga musu sanan tace ku banson iskanci ni sa r ku ce ta fada tana huci, ahh yi hakuri suka fada a tare suna darıya
Mahaifiyar su ce ta fito tana magana ah shukura keçe haka ya naganki a jike ne daga ina kike haka
Zumburo Baki tayi sanan tace wlh inna daga gidan şu kawata nake naje gidan aman ban sameta ba shine ruwa ya mun duka ta fada tana tashi tsaye
Ayyah ayyah aman kema tayaya zaki je gidan mutane baki fada ba , murmushin takaici tayi sanan tace wlh inna baxaki gane ba nidai bara nashiga na cire wanan kayan kwanaki ae na bar kayana bara na saka na fito ni yunwa ma nakeji ta fada tana yin hanyar dakin innar
Nuratu da zainab ne suka tafa suna darıya dan sunsan halin shukura da zuwa kwadayi gidan kawaye dan a lokalin da take gida Tasha zuwa gidan kawayen su zainab din da Nuratu indai taga gidan ana Çin abu mai maiko, an mata fadan an mata nasihar aman dük bataji ba ruwanta sai dai idan bata samu damu ba
Bata jima ba ta fito cikin riga da skirt na leshi sanan ta Shanya wanda ta cire ta zauna a kusa dasu zainab gamida janyo jakarta
Wayar ta ta soma kunawa aman taki kunuwa dan haka ta ja tsaki shikenan wayar da nake takama da ita itama ta lalace
Kallon juna zainab da nuratu sukayi sanan nuratu tace garıin yaya wayar ta lalace , wlh a ruwa ta fada shukura ta bata amsa tana Bude wayar , Allah ya kyauta aman dai ki shanya ta maybe ta kawo, bara na cire layina kawai dan Allah watan ku ta aramun wayarta na saka layina nayi waya , nuratu ce ta mika mata wata keypad tace gata aman sai kinyi a hankula itama tanada dan mastala gaskiya
Karbar wayar shukura tayi sanan ta şaka layinta a ciki ta shiga neman numbern ilham dan bazata iya hakura ba , Indai ta saka kanta abu toh fa saitayi take samun sukuni tunda ta saka kanta zuwa gidan ilham bazata taba hutawa ba sai taje, ringing daya biyu a na uku ta ilham ta dauka
Washe baki shukura tayi tana jin lham ta dauki wayar , cikin sauri ta fara magana ,Besty nazo fa tünda safe inata kira inata kira aman baki dauka ba
Tabe Baki ilham tayi sanan tace nagani aman dai bara na tambayeki wai ke bakisan courtesy ba ne ba ta fada tana sauraran amsar shukura
Uhm mene shi kuma ta fada tana washe baki , forget it namanta kaman ke ba bakiyi school ba dan da kinyi baxaki jera mun missed calls har kusan 30 ba for what naci miki bashi ne
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...