RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓bookWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣3️⃣Na saudaukar da wanna shafin ga mahaifiyar mu hajiya Aisha bashir musa wace Allah yayiwa rasuwa 19 ga wanan watan na September 2024 Allah ubangiji ya jikan ta da rahama , Allah ya haskaka kabarinta alfarmar manzon Allah (saw) mama Allah yasa can yafi nan Allah ya yafe mata kurakurenta ya haskaka kabarinta ameennn
🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥🫥
Shukura kallon Joseph ta shiga yi tana ji kamar ta bangaje shi ta shige gidan aman bazata iya ba Dan haka ta shiga masa Magiya da Hausa aman Joseph ba Hausa yake ji ba Dan haka shi duk bai gane abunda take fada ba a haka su dauki kusan Minti 30 a wanan halin
Madam please get out stop begging me Joseph ya fada yana kallonta Dan yanzu kuma ta fara bashi Haushi , mikewa yayi ya sinkuci shukura ya daga sama bai ajiye ta ko ina ba sai a bakin Gate bai damu da ihun da take ba tana kiran sunan ilham Dan ita ba damuwarta daga tan da wani kato yayi ba ne damuwarta Aa rabata da gidan da Joseph yayi ne ya saka ta ihu (waiyyazubillah )
Har Zai maida kofar ya rufe wayar sa ya kaste masa niyar sa Dan haka haka ya dauka ganin kiran ilham cikin harshen turanci yace hello madam good afternoon
Afternoon Joseph wa nake gani ka dauka haka ne gurin wa tazo ne ta fada da harshen turanci
Erhrm madam it's one mad woman o she said she is looking for you , and I am scared she didn't look like someone that can be friends who related to you that's why I'didint let her in sorry madam
It's okay Joseph let her in unn Ilham ta fada tana kashe wayar , bude kofar Joseph yayi sanan ya leka ya kalli shukura wace ke tsaye tana ha waye kamar wace aka Hana shiga aljana
Shigo Joseph ya fada da hausar sa da bata nana ba yana mata kallon raini da kaskanci, da sauri shukura ta shigo Tana Neman faduwa
Gidan ta nufa tana kale kale kamar yar kauye har ta shigo katon falo nan ta tsaya kallo tana sakin baki murya taji ana mata magana hajiya tace ki shigo Dayan falon mai aikin ilham ta fada tana kallon shukura
Ton Ina ne hanyar shukura ta fada tana kallon mai aikin , ki biyoni kawia tace mata sanan ta yi hanyar wani falon Wanda tsayawa bayaninsa bata baki ne nan fa shukura ta saki baki ido hanci tana kallon falon Dan yatafi da imaninta babu karya
Muryar ilham taji da kawarta suna shigowa falon aman hakan bai saka ta dawo daga duniyar kallon falon ba har suka karaso suka zuba mata ido şuna kallon ikon Allah da kauyancin shukurar
Shukura ilham ta kira sunanta tana kallon ta , ah kawata har kin shigo kice kai wlh Besty gidan nan yayi kyau wlh in badan karnayi sabo ba da nace nan ae aljana ce
Darıya suka saka gaba daya sanan ilham ta kali mai aikin nata tace kawo wa bakuwata kayan mosta baki Idan an gama abinci hado mata dashi
Karaf shukura tace sanan ki hadi mun da gashashiyar kaza idan so smau ne daya banason pieces Dan Allah Dan inaso nakai gida ma ta fada tana lashe baki Dan Tuna irin dadın da zata kwasa
Kallon ta mai aikin tayi cikeda mamaki tana mamakin hali irina shukura kina bakuwa kina wanan maular daga zuwa gidan mutane Rana ta farko aman dai mai aiki bata ce komai ba ta kalli Ilham Dan jin abunda Zata ce ,
Don't mind her saka mata rabi Dan Allah shukura bana son hadama ilham ta fada rai a bace Dan badan kawarta ta takura ma ba ba yadda Zata bari shukura ta shigo mata gida
Shukura shiru tayi sai yanzu kuma taji kimya ta kama ta da abun kunyar data aikata dan haka tayi kasa da kanta tana suna kai kasa . Mai aikin barın wajen tayi ba jimawa sai gata da abinci kala kala nan fa shukura aka shiga hadiye yawu Dan kuwa kamsshi ya adabe ta nan ta zura ma kayan ido aman ta kasa ma Taba wa Dan karda ta sake bada kanta irinna dazu
Bismillah ki ci mana kawar ilham ta fada tana kallon shukura , murmushi shukura tayi sanan tace toh hajiya nan ta bude warmer din dake gabanta ganin fried rice ya saka ta hadiye yawu nan ta zuba saida ta çıka plate dam sanan ta shiga bude sauran tana zubawa nan fa ta hau loma kamar abincin Zai gudu, takaicin yadda takecin abincin ya saka ilham tashi ta bar falon ta bar kawar tata tayi shigewar ta bedroom dinta
Shukura haka ta nadi abincinta ta sha lemo ta saki kyasta abunta sanan ta kalli kawar ilam tana washe baki tace Kai aman arziki yayi wlh sis nagode sosai da karamci
Ba komai shukura samira ta fada tana murmushi sanan tace yanzu kinga kinci abinci hankalinki ya dawo jikinki zamu iya magana dake tunda ba sauran yunwa tatare dake ta fada tana kallonta
Shukura washe baki tayi sana tace ahh wlh ma koshi samira ae yunwa ta gudu,
Haka akeso samira tabfafa tana murmushi sanan tace yauwa shukura kindai ga wanan gida kina so kema watarana ko nace nanda wasu lokuta ki malaki irinsa ko Wanda yafi sa kuwa ta fada tana kafe ta da ido
Kai samira waye baizai so ya malaki irin wanan gida ba wlh inaso
Yauwa abu daya ne zuwa biyu fa zaki na mana , kuma nanda wata biyu ma yayi yauwa wlh saikin siya gida har mota ta fada tana kallon shukura
Kai menen wanna wlh zan iya komai hajjaju,
Kin tabbata kuwa samira ta fada tana kallonta
Eh wlh na tabbata shukura ta fada tana maida hankalinta kan samira, zaki talata mana kwaya zaki zama mai kai ma manyan matan masu kudi kwaya kinga hajiya ilham mijinta sanane ne bazai yiwu tana kai irin wanna abun ba da kanta ba Dan haka Muke bukatar mata irinki marasa tsoro kuma kinga ke ba a sanki ba ba kamar mu ba , Ina mai tabbatar miki wlh zaki samu kudi sosai ke miliyan daya har dari sai kin dawo kina rabawa mutane a wanna sana ar kuma ba tareda kinji komai ba samira ta fada Tana gyara zama
Kwaya kına nufin safarar miyagun kwayoyi shukura ta fada gumi na karyo mata duk da sanyin ac dake falon
Daga Kai samira tayi alamun eh
Allah ya kiyaye wlh ni baxan ba wlh Allah ya kuma ya shirye ku shukura ta fada tana mikewa jikinta na rawa, samira kallonta yayi cikeda mamaki bata dauka shukura Zata ki tayin data mata ba kasancewar shukura mace mai kwadayi duba da abunda ta dinga yi
Haba shukura arziki na binki zaki saka kafa ki ture kiyi naxari mana samira ta fada tana kallonta , Allah ya kiyaye nayi arziki da saida kwaya, shukura ta fada Tana daukar jakar ta tayi hanyar waje
Bin bayanta samira tayi sanan ta mika mata bandir din dubu 1 da takarda ga number na nan Idan Kin Chanza shawara ki Kira ni Dan ko kin Kira ilham ba lallai ta dauka ba aman kimgani nan Ina sonki da alkhairi Dan haka kiyi tunani ko ki zabi zama mai kudi ko ki cigaba da maula gurin masu kudi tana gama fadin haka ta shige ciki ta bar shukura tsaye Tana kallo
Fitowa tayi daga gidan tana tunani kala kala har ta iso titi ta hau abun hawa dan komawa gida , a kofar gida ta sauka saidai ganin mutane cikeda kofar gidan ga yan sanda sun cakumi mijinta Aliyu ana ta kokarin dana sa a motar yan sandan ga hafsa nan sai kuka take itama an saka mata ankwa a hannu ganin shukura kuwa hafsa tace gata nan wanna itace mai haka komai din Dan Allah ni ku kyaleni tunda dai an ganta wlh ba ruwana a account Dina kawai ake tura kudin
Gaban shukura ne ya yanke ya fadi ta juya gurin mai Dan sahun daya ajiyeta Dan shigewa ciki ta koma inda ta fito saidai kash mai Dan sahu yaja abunsa ga jakar ta Wanda kudin da samira ta bata ma bata dauka ba ta manta shi a Dan sahu nan ta saka ihu ga tashin hankalin data shiga na tonuwar asirin ta ga kuma ta manta jakarta a Dan sahu
Nan yan sandan Dan suka nufo ta itama aka saka mata ankwa aka danna kansu cikin motar yan sandan nan mutane suka shiga fadin albarkacin bakinsu ana Allah wadarai da halin şu harda bawan Allah Aliyu da baiji bai gani ba .......
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
ContoYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...