Ramin karya 30

23 1 0
                                    

RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book

WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣0️⃣

Shiyasa nace miki daman ni I don't trust these men shiyasa ma na Baki shawara huda da karki yarda aman Zee ta ke dora ki akan ki yarda gashi Ashe ma babanta ne abu baiyi dadi ba yanzu kiyi hakuri Zee kawai alhamdulilah da babu abunda ya shiga tsakanin su huda bara mu sauke ki anan mu wuce ko we have alots to do yau pretty ta fada tana kallon huda

Zee ba bakın magana haka dai tayi  shiru tana ajiyar zuciya dan tabbas yau taji kunya sosai cikin , huda ce ta fito daga motar bayan driver yayi parking tace nagode pretty Zee dan Allah kiyi hakuri ku gaida gida

Preety ce kawai ta amsa aman Zee banza tayi da huda ta cigaba da kukan ta abunta dan sosai taji ciwon abunda mahaifin  mata yayi , pretty ce ta shiga rarashin ta har ta samu ta dan saki ranta aman a kasan zuciyarta tsanar huda ve fal ya çıka ta dan tafi jin haushin ta akan shi mahaifin nata ,

Huda kuwa abun mamaki ya bata da tsoro ta saki wani ajiyar zuciya tana godema Allah da son zuciya bai saka ta amince da maganar alhaji garzali ba da tuni yanzu tayi abun kunya baban kawarta da abun kunyar yayi mata yawa sosai gskiya , koda ta samu alhaji garzali a shagonsa da ta başa kudin Washe baki ya dinga yi dük zaton ta ta kawo masa kanta ne dan yasan ba bu inda zata je ta samo kudin daya bata ta kashe dan haka dole ta dawo ta yarda da abunda yace mata , Washe baki yayi yana shafa gemunsa yace huda hudallah yan mata ya akayi kinzo ne ki bani hakuri ko nidai nasan bakida wanan kudin ke danma kina yar birini aman ba wayo, kalli yan matan da nake taimaka wa dayawansu yan kauye ne kin fisu wayewa aman su ina fada suke yarda aman ke kinata kwana kwana ko dake mata masu kyau irin ku saida haka ya fada yana dariyar izgilanci

Tabe baki huda tayi sanan tace ni ba zuwa nayi ba dan na aikata sabon Allah zuwa nayi na baka kudin ka , kallonta yayi sanan ya tabe baki yace ke kudina nake so complete dan nasan ke bakida shi dan haka nama fasa baki wasu kwanakin yau zan saka a dauko mun ke na fanshe kudina ya fada yana huci kamar wani kumurcin maciji shi a dole ya  fusata

Murmushin takaici huda tayi sanan ta mika masa kudin , yana ganin su gabansa ya fadi ya shiga tambayan kansa a inda ta samo kudin nan , kunya take ya lulube shi ya saka hannu ya karbi kudin yana jujuya wa , ga kudin ka nan nagode shikenan ko ba wani sauran barazanar dauko ni dan baka bina ko sisi sai kuma a kama wani şarkın ta fada tana juya wa zata bar shagon, kunya ce ta lulube dük wata gaba ta jikin alhaji garzali dan haka kasa cewa komai yayi illa mazurai da yake tayi har huda ta bar wajen sanan ya cije yasta yana dana sanin sake har huda ta kubuce masa dan ya saka kahon zuka a kanta sosai bai dauka huda zata başa wuta haka ba

Tundaga ranar huda ta samu ta huta Akan maganar alhaji garzali sai ma ya daina zuwa ko aikowa siyan abincin jummai tun jummai na zagin huda Akan ta korar mata customer har ta hakura , a haka har su huda suka fara jarabawar barın makaranta lokalin kuma soyaya mai karfi ta kuma shiga tsakanin ta da Corper faisal kuma yana taimakonta sosai wajen karatın jarabawa hakan kuwa yana mata dadi sosai dan so take ta ci jarabawar ta

Zee kuwa tunda wanan abun ya faru ta kulaci huda a cikin ranta kuma tayi alwashin saita Rama Çin fuskar da hudar tayi mata na soyaya da babanta aman babu wanda yasan da abunda yake cikin ranta, sun fara jarabawa kuma komai yana tafiya qalau kwastam watarna sun fito daga jarabawa kenan prerty ta ce tanajin jiri, huda ta kale ta sannu maybe ko rashin yin breakfast ne yau da bakiyi ba ga Karatu mu samu muje cafeteria sai ki samu wani abun kici ko

Girgiza kanta pretty tayi sanan tace no bana sha awar komai wlh huda I am exhausted gaba daya na kasa gane kaina kwana 2 , Zee ce tace ke ba wani Abu exams fever ne kinsan shi haka yake , kiran salla aka farayi a massalaci dan haka huda tace girls kunga ana kiran salla nikam yau an yafe mun kufa yakamata kuje kuyi idan kunayi dan na karfe 2 ne kar lokaci ya küre ko , Zee ce ta girgiza kai Nima banayi har tsakiyar wata ne , ke fa preety huda ta fada Tana kallon ta , eh preety naga alama almost tare mukeyi dukan mu dük wata aman wata kusan biyu kenan ke naga shiru bakice mana bakon ki yazo lafıya kike kuwa

Pretty ce ta ce wlh Nima abun yana damuna kawai na yi nauyin baki ne ban fada muku ba ta fada fuskar ta cike da damuwa , huda ce tace uhm gaskiya abun da mamaki aman abunda da za ayi shine gobe insha Allah müzo da wuri sai mu fita asibiti a duba ki agani lafıya tunda infection ma yana janyo rashin ganin al ada huda ta fada tana kallon kawayen nata ko sun yarda da abunda tace

Zee ce ta Gyada kai sanan tace hakane kam aman ya kikace preety , naji hakan ma yayi nagode da kulawar ku yanzu kuzo ku rakani nayi sallaar sai mu tafi gida driver sai ya ajiye kowa , tom shikenan suka amsa a tare sanan sukayi hanyar massalacin makaranta dan Raka pretty...

Washe gari shine ranar da bazasu taba mantawa ba gaba dayansu bayan sun kamala paper din safe kasancewar sun gama tun gurin 10 , dan haka suka ce da driver din preety ya kai su wani private asibiti , test aka yi ma pretty bayan sun ma nurses din bayanı, anyi mata test din fistari da jini , gwajin farko sakamako ya fito pretty na dauke da ciki har wata 2 da satika, tashin hankali wanda ba a saka masa ranar nan hankalin kawayen uku ya tashi , preety anan ta fadi sumamiya nan aka shiga da ita daki dan kula da ita sukuma su huda na waje sun zabga tagumi cike da damuwa, Zee ta kalli huda tace huda nashiga uku Nima na biyema pretty Allah ysa ba cikin bane Dani Nima wayoo Allah na , huda ce ta dafa ta sanan tace insha Allah bakida komai Zee kidaina wanan maganar dan Allah

Zee ce tace wlh huda kinji dadin ki yanzu mu kalli irin rayuwar da muka saka kanmu a ciki kai gaskiya RAMIN  KARYA  kurare take yanzu na sake tabbar da haka da iyayenmu basusan da abunda muke yi ba aman dole yanzu zasu sani mussaman iyayyen pretty wlh babanta sai ya kuşa kasheta dan babu abunda baya bawa preety gwanda ni halin rashi ne ya saka ni wanan rayuwar wayoo Allah na Zee ta kuma fashewa da kuka

Huda ce ta cigaba da rarashin ta har aka zo aka sanar da su pretty ta farfado dan haka suka yi hanyar dakin da aka kwantar da ita cikin sauri, a zaune suka sameta gaba daya idanuwanta sunyi jawur ta na ganin su huda ta fashe da wani irin kuka mai karfi, cikin kuka ta fara magana kungani ko da ace wanan cikin ta hanyar suna na sameta da babu Wanda yau  zai kaini farin ciki a duniya aman dake ta hanyar banza na sameta kalli yadda nake kuka da nadama kuma kuna tayani bakın ciki kaico ni kaico ni wlh sai yau na sake yin nadamar rayuwar dana saka kaina nashiga uku ta fada tana daura hannu a kanta

Kuka suma su huda suka fara suna rike da juna ba mai rarashin kowa a cikinsu saida suka yi mai isar su sanan sukayi shiru sanan kuma Zee da huda suka shiga rarashin pretty Akan tayi hakuri su samo mafita kawai

Kawai mafita zubar wa zan yi pretty ta fada tana kallon kawayen nata , dan Allah karki zubar huda ta fada tana zaro ido, tabarshi su daddy su kashe ta kike zo Zee ta fada tana kallon huda , aa ba haka nake nufi ba ni ganina gwanada ta fada musu nasan komai zaizo da sauki Akan ta kuma zubar da cikin kinga fa ta aikata laifi biyu fa kenan

Zee ce tace kinga preety it's better fa kawai ki zubar wlh shine Mafita kawai , huda ce ta girgiza kai sanan tace no preety don't do that please am begging you , prerty ce ta ce kunga ku dakata I will think about it and zan Kira Samir sabida nasan cikin sa wlh dan shi kadai na yarda dashi sauran kawia ana soyaya ne asha shisha aman ba wani Abu da yataba shiga tsakanin mu sai Samir ta fada tana goge hawayen da yake gangaro mata

Ni fa a ganina it's better ki sanar dashi ya fito kuyi aure idan kika haihu aman da. Allah karkiyi aborting huda ta fada tana kallon pretty , I will think about it huda bayan nayi magana da Samir yanzu ku tashi mu tafi gida yau kuyi hakuri a ajiye ku a kan hanya başai ya kaiku kamar yadda aka saba ba kawai so nake nagani a gida prerty ta fada tana mikewa

Tashi sukayi dukansu sukaje reception bayan preety ta biya bills din suka shiga mota aka a titi fara ajiye huda har zata tsalaka ta kuma dawowa ta rike hannun preety tace preety dan Allah don't do anything stupid dan Allah , promise me ta fada tana kallon idonta wanda ba abunda take hangowa sai tsantsar nadama a idon preety , gyada kanta Pretty sanan ta sakar ma huda Murmushi ba tareda tace komai ba

Huda ce ta sakar mata hannu sanan ta dağa mata hannu har ta ga sun ja mota sun bace mata sanan ta goge hawayen daya gangaro mata ta tsalaka titin dan samun abun hawa Ashe wanan rana shine rana na Karshe da zata sake ganawa da kawarta mai Sonta ........

Ku biyoni dan jin abunda zai faru da preety yanzu dai munzo rabi dan haka zan dauki hutu sai kuma mun dawo nanda wata daya insha Allah

Mrs abba 💕✌️

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now