📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 1️⃣7️⃣
Jummai na sauka ta salame zainabu suka shiga da Kayan cikin gidan sanan zainabu tayi mata Salama ta tafi gida
Sai bayan magariba sanan hüda ta shigo gidan bayan tayi wa badariya godiya Akan abunda tayi mata sukayi ban kwana sanan kowa ya shige gidan su
Hansai taji dadin cinikin da sukayi aman badariya ta sanar da ita wulakancin da jummai tayi mata ba a kasuwar kawai da ta tambayeta Allah yasa dai babu abunda yafaru a kasuwar cewa tayi babu abunda ya faru nan kuwa hansai tayita Jin dadi dan Allah ya dube su ya saka yanzu zasu daina yawon maula a basu a hankula suma su samu su bude tasu rumfar ranar dai da ribar zoban suka siya Kayan abinci suka ci sauran kuma hansai ta zuba a bankin ta na kasa da take ajiya sanan ta bawa badariya kudin aka je aka siyo kayan hadin zoban da kunun aya sabida na gobe
Huda na shigowa gidan ta iske jummai na tsakar gida tana Çin tsire da lemon kwalba da ta aika yaron makota ya siyo mata ta wurga ma huda wani kallo sanan ta fara magana
Ke sai yanzu kika daman dawo wa ko
Huda ce ta Girgiza Kai sanan tace kiyi hakuri jummai banso na dade ba ta fada tana sunkunyar da Kai
Ke kika sani kuma wanan ni yanzu kizo kiyi mun wanke wanke shine damuwa na ba komai ba
Toh huda ta amsa ta ajiye mayafinta ta hau yin wanke wanke saida ta gama gaba daya wanke wanke sanan ta gyara wajen ta daura alwala ta shiga dakin ta danyin sallah
Magariba da isha ta hada dan tana hanya akayi magariba isha kuma tana wanke wanke akayi aman ba damar yi dan jummai saita zage ta idan ta bar aikin datake taje yin sallah
Bayan ta iddar sa sallah taji cikinta yana kiran ciroma ta rinste ido dan ba karamun yunwa take ji ba abincin da ta siya gurin jummai ba wani isarta yayi ba dan haka ba shiri ta tashi ta fita tsakar gida inda jummai take zaune dan ankawo wuta tsakar gidan da akwai wutan nepa ya haska tsakar gidan
Tsayawa tayi a Jan jummai wace ke Shan lemon kwalba abunta dan ta cinye naman ta taş saura kuli
Jummai abinci na yunwa nake ji huda ta fada tana kallon jummai
O duka na zakiyi kenan idan bace babu jummai ta fada a hasale tana hararar hüda
Durkuwa hüda tayi ta Girgiza Kai aa ba haka bane ba kiyi hakuri
Toh babu banyi ba dan haka ki wuce ki bani waje jummai ta fada tana mikewa tsaye ta shige dakin ta abunta Tana mita
Maste hawaye huda tayi Anya wanan mahaifiyarta ce kuwa wace uwa ce zata bar yarta da yunwa ita ta çıka cikinta da abunda take so ta Girgiza Kai tana maste hawaye
Fitowar jummai ne ya saka ta yi shiru ta risinar da kai zuciyarta na mata zafi
Jummai ta dube ta ta tabe baki ni zan fita cefane idan kinga dama ki bar fita tunda ki samo Wanda zai Baki kudi ki siya abinci kici idan kuma kinga dama ki zaman ki ki mutu da yunwa doluwa kawai ni bara Kiji lokacin da Ina kamar ki da kyau na da diri na ba abunda bana ci na Kayan dadi sanan ba suturar da bana sawa dan Ina amfani da abunda nake da shi nasamu abunda nake so
Maza har dambe suke akaina dandai da Rabon haihuwa tsakanin a da uban ku da wlh bazan aure shi ba auren sa ya saka na shigo wanan rayuwar gashi na kare da siyar da abinci a bakin kasuwa
Tana gama fadin haka ta fice daga gidan tana mita
Zaman yan bori huda tayi a wajen tana maganar jummai na yawo a kwakwalwar ta , me jummai ke nufi da taje Neman abinci tana nufin tabi maza Kenan
Ta dade tana juya maganar jummai sanan ta tashi ta shiga dakin ta ta dauko sauran changin naira Dari dinan ta fice daga gidan zuwa wajen mai awara ta siyo ta dari ta dawo gudan ta dauko takardar tsiren da jummai ta gama ci tana dangwala Sauran kulin da awarar har ta cinye taş badan ta koshi ba ta tashi ta debo ruwa a randa mai sanyi ta sha sanan ta shige dakin ta ta kwanta a wata gagulaliyar tabarma dan shine a mastayin katifar ta nan kuwa bacci yayi gaba da ita mai cike da mafarki kala kala ...
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
ContoYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...
