📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 1️⃣4️⃣Fadamun daga inda kike aliyu ya fada yana kallona fuska a daure ba alamun ya taba dariya ma a rayuwarsa , hanayenta shukura ta hada ta shiga roqo dan Allah aliyu kayi hakuri wlh Zanyi maka bayani ta fada tana kallon sa
Okay Ina jinki yimun bayani ,
Daman daman daman
Bakida abun cewa ko shukura shikenan kızı juya ki koma inda kika fito
Tsugunawa tayi a kasa ta shiga magiya
Dan Allah aliyu kayi hakuri dan Allah wlh bansan meyake damuna ba kamar dai bani kadai bace ba bana sani nake wasu abubuwan wlh
Eh tabbas baki sani aljanu ne ko aliyu ya fada yana hararta
Girgiza Kai shukura tayi sanan tace yauwa aliyu wlh Ina tunanin süne suke dauka ta suke tafiya Dani wlh aliyu
Wlh shukura kina saka mun ciwon Kai aman tsayuwa magana dake a nan ba mutuncina bane ba shige gidan aman dole ne ki tanadi bayanın da zaki mun idan nadawo daga massalaci inda kikaje da meyasa kika fita ba tareda izini na ba bayan nayi miki gargadi da karki fita yana gama fadin haka ya saka Kai ya bar wajen dan zuwa massalaci
Kallon kofar shukura tayi ta saki ajiyar zuciya , bata dauka aliyu zai bita ta lumana ba tasan yadda zata shawo hankalin sa dan shi mutum ne mai San kwaliya da kananan Kaya dan haka tasan yadda zatayi ya manta da wani fushi da ita da yake yi
Wanka ta yi sanan ta saka wasu mastatun Riga da wando ta zira hijabi sanan ta yi sallar mağrib tana zaune har aka kira sallar isha dan haka ta tashi ta yi sanan ta janyo wayarta ta shiga WhatsApp
Maganar bikin ake tayi sosai ana yabon kwali yar da kowa yayi musaman shukura dan shukura Karshe ce wajen kyau da iya daukar wanka
Murmusi tayi ta yi tana Jin dadi da cire cutar da tayi dan daman hakan ta so ta saki murmushi tace
Gskia banyi wahala a banza ba duk banza kwaliya ta biya kudin sabulu
Wayar sumaya ne ya kaste mata magnar da take , nan take ta tuna da sarkar sumayah daya fadi ta dafe Kai tana rinste ido wlh bazan dauka ba ta fada a filli sanan ta saka wayar a silent ta cigaba da abun da take
A massalaci kuwa bayan an iddar da sallah sun fito umar ya bi bayan aliyu yana kiran sa Mallam aliyu dan tsaya mana umar ya fada yana murmushi
Ah umar ya aiki ya garin aliyu ya tamabayeshi
Lfy qalau aman fa baka san baiwar da Allah yayi maka ba mutuminan
Bai wa kuma umar ya tambaya cike da mamakin abunda ya fada masa
Eh mana malam aliyu baka san mata baiwa bane ba matarka ae tafi matan mu wlh ace mace haka wlh tanada kyau da kyaun jiki Kai Masha Allah ya karasa fada yana Washe Baki kamar wani sakarai
Cakumo shi da aliyu ne ya saka ya zaro idanuwan sa yana neman shidewa
Kai sabida bakada mutunci matar tawa kake fada ma haka
Sake ni menene dan na yaba matar ka wani abun ne Kai meyasa Baka bata kudi da zata kula da kanta har ta tsaya rigima da mai dan sahu har ya kwace mata mayafi na ga surar ta ae kaine baban marar mutunci tunda Kanada mata mai kyau haka aman ka tsaya mata rowa
Naushi aliyu yakai masa har saida jini ya fita daga bakin sa , nan fa mutane suka zo aka rike aliyu ana tambayan dalili
Umar ne ya ce ku tambaye shi mana dolon namiji mai yiwa matar sa rowa
Menene haka umar me ya shafe ka da matar sa garba ya tambayi umar
Daga taimako , taimakon sa fa nayi matar sa na biya wa kudin mashin dan mai mashin yana mata wulakanci shine fa yazı yana duka na
Wai haka aliyu garba ya mayar da dubansa gurin aliyu
Bansani ba aman wlh ku fada masa idan ya sake magana irin wanan akan mata ta wlh saina cire masa hakora
Aa aliyu matar kace fa duk ta janyo wanan abun dauda ya fada yana hararar aliyu da bata tsaya rigima da dan sahu ba a Ina umar zai ganta ya taimaka mata Ina fa kallon duk abun da ya faru shi fa umar taimkonta yayi
Aliyu kan dauda yayi da shirin shima Kai masa naushi aman ya kauce , aliyu yayi kwafa sanan ya bar wajen ransa na suya a da yayi Hakuri Akan abunda shukura tayi aman yanzu wlh saiya dauki mataki mai karfi dan bazai yiwu ba yadda yake da kishi ya tsaya wani yana fadin kalmomi kamar Wanda umar yake fada akan matar sa ta sunna
Gidan ya nufa gadan gadan ya shiga ya buga kofar gidan , bedroom ya shigo ya same ta tana kwance
Ke shukura ni zaki wulakanta a unguwar nan sabida ke bakida kirki wai ke wata irin mace ce
Kamar ya aliyu me kake nufi ta tashi zaune tana kallon sa a tsorace
Eh abunda umar ya fada mun Gaskiya ne kin tsaya rigima da mai dan sahu Akan kudin mashin har ya karbi mayafin ki
Shiru shukura tayi ta shiga wurga ido dan bata dauka aliyu zai San maganar ba
Tambyanki nake kinyi mun shiru ya tambaya da kaukausar murya
Kayi hakuri wlh kudina ne ya fadi , eh kudin ki ya fadi shine kika tsaya wani mahaukaci ya biya miki
Wlh tun wuri ki fada mun inda kikaje da abunda yasaka umar ya biya miki kudin mashin
Aliyu wlh suna naje Anty Zara ce ta haihu
Anty Zara ce ta haihu shine banji ba tun wuri ki fadamun inda kika je ko kuma wlh ranki ya baci nagaji da wanna halin naki aure wata takwas aman kina Neman haukatar Dani
Kayi hakuri aliyu wlh bazan Kara ba , ta durkusa a kan gwiwowin ta tana maste hawaye ,
Allah yasani yana son shukura kuma hawayen ta yana masa ciwo shiyasa yake Jin yanzu tausayin ta aman Kishin ta yayi masa yawa , baya son wani ya kalle masa mata shiyasa ma idan zata fita yake saka ta dole saita saka hijab aman wani banza can yau ya kare mata kallo har yana fada masa tanada diri wanan abun ba karamin ciwo yayi masa ba
Tsaki yaja ya fice daga dakin gaba daya na tareda ya kuma cewa komai ba ..
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...