RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓bookWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣5️⃣Kai tsaye gidan ilham Shakura ta wuce bayan sun yi waya da samira akan tazo gidan ta sameta, koda tazo joseph bude mata kofa yayi yana mazurai dan samira ta sanar dashi ya bar shukura ta shigo wanan lokacin
Tana shiga kai tsaye falo ta nufa ta samu samira da ilham na falo suna magana kasa kasa dan ko kusa dasu kake ba lalai kaji abunda suke cewa ba
Samira ce ta saki Murmushi ganin shukura sanan tace sannu ko karshen wahalar ki kenan insha Allah indai kina tare damu ba wanda ya isa ya miki kallon banza bare ya kaiki wani police station ,
Washe baki Shakura Tayi jin abunda samira ta fada sanan ta samu waje ta zauna tana kallon su
Wlh hajiya duk abunda kuka saka ni zanyi indai zan samu kudi ni , a rayuwar nan nagaji da wulaknta ni da akeyi yanzu ni nake so na dinga wulakanta mutane mussaman waenda suka wulakanta ni dan haka komene kuka saka ni zanyi muku indai zaku bani kudi dazai Chanzamun rayuwa nima a dinga damawa dani nazama kamar ku na dinga juya nera badai nera ta juya ni ba ta fada tana washe baki
Dariya samira tayi sanan tace kai Shakura kina bani dariya wlh kawata kiji fa wata magana samira ta fada tana kallon ilham wace ke dana waya abunta kamar bata jin abunda Shakura take cewa,
Kawata dakefa nake naji kinyi shiru samira ta fada tana kallon ilham
Tabe baki kawai tayi sanan tace samira just give her her task madam Cynthia is waiting da ita muke chat yanzu sanan warn her wlh karda a samu wani problem dan kece zakiyi facing consequences din dan kece kika janyo mana ita dan haka duk abunda tayi ke zan rike
Haba mana ily ki yarda dani kinsan fa bana kawo shawara marar Kyau just have faith in me samira ta fada tana kallon ilham
Nidai na fada miki ki bata information din ni zan shiga ciki zanyi waya da oga hopefully nasameshi a waya idan kungama I will be inside tana gama fadin hakan ta shige ciki abunta
Shukura ce ta kalli samira tace hajiya wai mene nayi wa haj ilham ne naga kamar bata sona, samira ce tayi murmushi sanan tace aa tana sonki kawai ilham dince ba koyaushe take sakin fuska ba nima lalabata nake wani Lokacin kinga lokacina kurewa ga wanan ta Mika mata wata jakar goyo shukura ta saka hannu ta karba sanan tace idan kika fita zaki ga Mota a parking space ash ki shiga Zai kaiki inda xaki bada jakar aman da sharadi karki bude ga wanan ta mika mata wata karamar waya shukura ta karba tana kallon samira dan jin sauran bayani
ki duba call logs number din karshe shine numbeen da zaki kira idan kun isa ki bada jakar indai na tabbatar kin bayar toh naira miliyan 2 takice
zaro ido shukura tayi tana kallon samira cikeda tsoro da mamaki , daga kanta samira tayi sanan tace wanan kadan ne a cikin arzikin da xaki samu indai kin tsaya kinyi aiki kuma ba surutu toh saikin zama hajiya abun sha awa cikin al umma
kai aman hajiya nagode bara nazo naje shukura ta fada tana mikewa jikinta na rawa haka ta fito ta nufi parking space driver ya bude ta shiga suka dauki hanyar gidan madam cynthia dan kai mata hodar iblis
Cikin mintuna da basu wuce talatin ba suka karasa gidan madam Cynthia ta bada jakar sanan driver a yadawo da ita gidan
Cash miliyan 2 samira ta baiwa shukura ladan aikinta ganin takai Kaya lfy lau ba tareda wani mastala ba nan fa shukura ta fara ihun Murna tana kallon jakar kudin gaskiya yau tana cikin farin ciki marar mistaltuwa
A gidan ta kwana bayan ta cika tumbinta da abinci Mai rai da lfy sanan ta kwanta nan take bacci yayi awon gaba da ita mai cikeda mafarki masu dadi tama manta da bawan Allah aliyu wanda a yanzu bata san makomar aurenta ba
Shikuwa aliyu bayan ya koma gida sosai abunda shukura ta janyo masa ya bata masa rai aman hakan baisa yaji zai rabu da ita ba saidai kuma rashin ganinta ya saka ya koma police station ko tana can aman aka Sanar masa da an salameta dan haka ya nufi gidan su nan ma aka sanar Dashi bata gidan dan haka cikeda damuwa ya dawo gidan yana tunanin inda ta shiga Ranar bai iya wani baccin kirki ba
Washe gari da safe ya fito ya kuma komawa gidan Nasu aman shiru haka ya dawo gidan ya kwanta da kansa ba karamin ciwo yake masa ba nan wani wahalalaen bacci ya dauke shi
A cikin baccin yaji Alamun ana Taba Kaya dan haka ya bude ido ganin shukura na had a Kaya ya saka ya ware idanuwaansa yana kallon ta shukura ina kika shiga ne ya fada da muryar bacci
Tsaki taja mai kara sanan tace inda ka aikeni nusarin namiji kaga aliyu kake ko wa ba dan ka tambyeni inda naje ba ya saka nazo nazo ne ka rubuta mun takadar sakina ka danka mun abuna a hanuna nasan zawarci nake Akan wanan kadararen Auren naka
Sakin baki aliyu yayi yana kallon ta batareda yace komai ba sanan yace shukura lfy kuwa idan ma da wanda akayi wa laifi ae nine aman ke ce kike fadin wanan maganar
Kai Dakata mallan kai waye nawa kake dashi nawa ka Tara ba ko sisi bakadashi kuma baka bawa kowa ajiya ba dan haka Kamin shiru ka bani takardata aure dani dakai ya kare ko a lahira bana son na kara ganinka
Shikenan shukura tunda haka kika nema zanyi miki aman ki sani zakiyi dana sanin wanan hukuncin da kika yanke
Dariya tayi sanan tace dana sani yana gurin Wanda bashida ko sisi kagani nan ni da kake gani na bawa miliyan biyu baya dan haka dana sani ba Tawa bace ba dana sani naka ne kai da kake fama da talauci aman ni shukura yanzu kuma na dace can kaje ka karata da talaucinka ni yanzu ba ajinka bace ba
Aliyu ne ya Gyada kai zuciyarsa na suya sanan yace ba komai shukura arziki na Allah ne kije na sake ki saki daya
Wlh aliyu saika cike biyun nan dan wlh bazan dawo gareka ba ni shukura na haramta a gurinka dan haka dan ubanka ka cike
Ni kike zagi shukura aliyu ya fada cikeda jin zafin zagin da ta masa
Eh din ka sake ni mallan dole ne wai zama dakai
Ba dole bane ba shukura kije na sake ki saki uku Allah ya baki daidai dake yana gama fadin haka ya fice daga gidan gaba daya
Dariya shukura tayi sanan tace kai Allah alhamdulilah wlh naji dadi sosai nan ta haka Kayan ta badan tana bukatar su ba ta nufi gidan su
Tana zuwa yara suka shigo da kayan niki niki nan mahaifiyata cikeda mamaki ta shiga tambya meya kawo kayanta haka
Ya sakeni saki uku ni na nema aman fa dan wlh mama Aurensa ya fita raina wanan Kayan gashi ku ku raba ni bana Bukata yanzu ma gida zan nema na koma nasamu Aiki acan zanyi idda abuna ta fada tana kallon mama
Nan kaninta suka nufi kayan da murna suka shiga zaba , mama kuwa sakin baki tayi tana kallon shukura Kafin daga bisani tace yanzu ke shukura rayuwar da kika dauwaka kanki kenan
Shiru tayi tana cuno baki sanan tace kai mamma kema haka zakice nace miki fa yanzu na samu aiki kuma nayi kudi wlh yanzu na girmi ajin aliyu
Ba shaka toh wlh saidai ki zaba ko ki Daina koma wani shieme kike kika samu wanan kazamun kudin ko kuma na yafeki cikin yarana shukura
Au mama kema bakin cikin kike mun kamar aliyu kenan shikenan mama na zabi aikina ni kinga tafiyata shukura ta fada tana mikewa
Mama cikin fushi tace dawo nan shukura nice fa na haifeki ni ne kikecema ina miki Bakin ciki
Toh mama idan ba bakin ciki ba menene dan Allah dan annabi nace na samu aiki maimakon ki mun murna kince wai saidai na zaba toh idan na bar aiki me zaki bani talauci gaskiya ni bazan iya ba gwanda nabar miki gidan daman idan kin kwantar da hankalinki ni ba zama zan ba a wanan gidan dan haka kinga tafiyata
Tana gama fadin haka ta saka kai ta fice daga gidan tana mita.....
Mrs abba
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...