RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book
WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 42Yau tunda su shukura suka tashi suke cikin tashin hankali dan kuwa anyi musu waya cewa custom sun kama musu Kaya dan haka a haukace shukura ta zo gidan ilham ko kayan baci bata chanza ba
Ilham cikin tashin hankali ta shiga yin waya aman amsar daya ce dai bayada Zasu iya maganar tafi karfinsu dan haka cikin tashin hankali ta kashe wayar ta kalli shukura cikin tashin hankali tace toh shukura a stage din da ake ciki yanzu dole kowa ya kama gabansa yasan nayi dan nidai kaina nasani dan haka yau zan bar Kasar nan
Haba illy ya zakice haka ne bayan duk Tare muke gaskiya wanan abu dole ne fa ki tsaya nida banida visa ya xanyi kenan , ilham cikin massifa tace shukura kenan kinsani da ne ko Kina tunanin da da muka Taimaka miki munyi shine haka kawai aa munyi amfabi dake ne dan tara dukiya dan haka mun samu kuma yanzu lokacin zuwa hutu ne kowa ya iya allonsa ya wanke kinga tafiyata daman yarana da mijina sun dade a England dan mijina money laudary yake kuma effcc sun fara bincike kansa shiyasa mukayi dabara ya koma kasar waje da yara dan haka tun kafin azo kamani Nima zan bisu muje can kudin da mijina ma kawai ya tara mana ya ishe mu rayuwa ballana na had a da nawa kudin dan haka kisan inda dare yayi miki
Shiru shukura tayi gabanta na faduwa ganin komai take kamar a mafarki, kamar jiya nan ta ganta cikin daula suna fantama dasu ilham shine yanzu komai ya juya an barta ta karata kenan wayoo Allah na na shiga uku ta fada tana dafe kai wayarta ta dauka ta dana Kiran samira dan tasan bazata barta cikin masatala ba daman ilham ba wani sonta take ba dan haka ma batayi wani mamaki ba
Tana kiran samira bugu daya ta dauka , cikin tashin hankali shukura ta fara magana samira Muna cikin tashin hakali fa bansani ba ko ily ta fada miki an kama mana Kaya fa dan Allah mene abunyi ya zamuyi ne
Haahaha yazakiyi ke dai wani irin ma Muna cikin mastala kina cikin mastala dai
Kamar ya samira bakiji menace bane ba an kama mana Kaya fa nace , eh naji ki shukura mai bakin uwa ni kinga yanzu jirgin mu zai dauki hanya ma ina hanyar zuwa uk zan koma gaban iyayena ily kuwa nasan itama yanzu zata ware dan haka ke za a nema kece a Ruwa dan ni yanzu ma karya layi na zanyi na huta dan haka idan kije prison ki gaida masu irin hali irin naki da masu bakin iyaye kinji nabarki lafiya kit ta kashe wayar tana dariya
Sakin baki shukura tayi tana mamakin abunda samira ta fada mata tana zaune a falon gaba daya ta rasa abunda yake mata dadi, ilham ce ta fito da akwati tana ja ta kalleta tace toh shukura tashi ki fita za a rufe mun gida ko
Shukura tana haw aye ta kalli ilham tace Wlh kun cuce ni kun hanani zaman aure sanan yanzu kun barni banida wajen buya mahaifiyata mun bata duk saboda ku
Dakata kwadayinki yaja miki bamu bane ba muka hanaki ki gyara zancen ki ehe kuma ae ke ba yarinya bane ba dan haka fitar mun a gida marar kun ya wace batasan halaci ba kiyi gagawar zuwa neman yafiya wlh gurin mahaifiyarki dan kuwa alkakinta ma ba zai taba barin ki ba fitar Mun a gida
Tsinema Ilham da samira shukura ta shiga yi tana kuka wiwi harta fita , motar ta ta shige tayi hanyar gidansu da gudu a mota
Bata tsaya ko ina ba sai a kofar gidan nasu tana shiga gidan da gudu ta shiga kiran sunan mana mama tana kuka, Hindatu ce ta ce me kika zo ne ma kuma bayan burinki ya cika
Ku fadamun komai zaku fada hindatu wlh nasan na cancanci haka ni mai laifi ce a wajenku dan Allah ina mama Wlh ina cikin masatala
Murmushin takaici hindatu tayi sanan tace mama kike so kigani, shukura ta daga kai alamun eh hawaye na zuba a idonta
Mama tana kabari saikije ki ganta kuma Wlh wlh bamu Yafe miki ba kece sillar mutuwar mama wlh sai Allah ya Saka mana kin maida mu marayu tana gama
Fadin haka ta shigewarta ciki ta bar shukura Baki budeNan shukura ta hau kuka da birgima a kasa saida tayi mai isarta sanan tayi shiru tana ajiyar Zuciya, ba yadda kanenta suka iya dole yar uwar su ce dan haka suka hadu suna kuka sai neman yafiyar su take hindatu kuwa tunda ta shige dakin su bata sake fitowa ba
Bayan sati biyu da kyar su hindatu suka yafe mata dan haka yau tace hindatu ta rakata gidanta dan kwaso kayanta dan tunda tazo bata koma ba
Hanya suka dauka aaman a napep har gidan shukurar suka shiga suka shiga kwaso kaya duk wani mai amfani da takardun kadarorinta suka fito saidai kacibus da yan sanda yasaka shukura ja baya tana zaro ido
Wace shukura tahir dan sandan ya fada yana kallonsu, daga kai shukura tayi sanan tace nice yallabai cikeda Tsoro, you are under arrest ki mana shiru you have the right to remain silent because anything you say will be used against you in the court of law dan haka cikin ruwan Sanyi ki biyo mu
Haka shukura tana ji tana gani suka saka ta a gaba suka tafi da ita hindatu kuwa ta wuce gida tana hawaye
Anyi bincike sosai sanan aka kai shukura courtu su Ilham da samira kuwa sun sha dan sun bar kasar dan haka shukura naji nagani aka kwace duka wani abu data malaka aka yanke mata hukuncin shekara 12 a gjdan yari ba tara ihu da kuka ba wanda shukura bata yi ba a kotu mutane suka ji tausayinta sosai masu Allah wadarai nayi masu tausaya mata nayi
Kanenta kuwa da kyar aka raba su suna ta kuka abundai abun tausayi haka dai jami an tsaro suka tafi da shukura sai gidan yari
Nan shukura ta shiga dana sanin rayuwata data sani bata wulakanta aure ba da bijirewa mahaifiyarta ta biyema rudin duniya da kwadayi dasu ilham wanda take gani suke birgeta yanzu gashi itace shekara har sha biyu a gidan yari kai kaicona ta fada tana kuka .................
Aliyu kuwa bayan rabuwarsa da shukura ya shiga damuwa sosai dan haka ya shirya ya bar garin ya koma Lagos can ya samu aiki mai tsoka sosai yanzu haka yayi arziki yayi aure abunsa yarsa daya waatrana yakan tuna da shukura da godema Allah changin daya masa
Labarin shukura ya saka masu irin hali irin nata sun shiryu hafsa kawarta kuwa tuni ta tuba ta nemi gafarar mijinta kuma ya yafe mata su hindatu kuwa Sukan kaima shukura ziyara data gansu kuwa sai kuka tana Dana sanin abunda ta aikata da tsinema samira da ilham yanzu sosai shukura ta shiryu tana ta neman gafarar Allah , abu daya yake tayar mata da hankali idan ta tuna da bakin cikinta mahaifiyarta ta rasu saita ji gaba daya kamar ta kashe kanta ta huta aman ina zunubi zata kwasar ma kanta wanda yafi nada dan haka ta dage da istigifar tana neman yafiyar Allah sai muce Allah ya yafe mata ameen
Mrs abba
![](https://img.wattpad.com/cover/373258922-288-k585625.jpg)
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Короткий рассказYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...