📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 1️⃣0️⃣Shukra na fitowa daga gidan sumayah ta nufi gidanta tana Jin dadi , wlh shi kadai zaici fara da mai dinsa wanan kazar haramiyar sa ce nan ta karasa gida ta bude ta shiga
Kai tsaye dakin ta ta shiga ta zauna ta fara Çin namanta tana Shan sauran lemon da tazo dashi sanan ta tashi ta kuskure bakin ta tayi sallah ishae cike da farin ciki
Ko da aliyu yadawo har ya manta da rigimar da sukayi da shukra kafin ya fita itama kuma bata dau fushi dashi ba dan ita indai zata samu abunda takeso toh duk fushin da yake zai wuce ta cigaba da sha aninta abunta
Shinkafa da manja da yaji yaci abunsa har ya koshi sanan yayi duk wani Abu da ya Saba yi sanan ya kwanta abunsa har lokacin uwar gayyar tana dana waya tana chat da kawayenta a group ana tautauna yadda bıkın gobe zai kasance
Da safe kuwa kısaı ya fita ya siyo musu suka karya saidai hakan bai burge shukra ba haka ta dinga cusa kosain ba dan ranta yana so ba kawai dan ba yadda zatayi ne
Shiryawa aliyu zaiyi zai tafi kasuwa wajen sana ar facin da yake yi , har zai fita ya dawo ya tarar da shukura na Danna waya yace toh ni zan fita idan kinga dama na dawo gidan nan naki tarar dake sai ranki ya bace kamar yadda na fada miki saikinyi wata Baki leka waje ba dan haka karna ganki a waje
Dauke da murmushi a fuskar ta tace insha Allah bazan je ko Ina ba a dawo lafiya
Ameen Allah ya miki albarka ya fada yana tafiya
Ameen ta amsa tana harara a kasa kasa
Yana fita ta ja dogon tsaki tace
"Tab kaji mun mutum wato ni nazauna a gida bakin ciki ya kashe ni toh wlh bazai yiwu ba biki kamar naje shi ne ehe "
Mike kafa tayi tana cigaba da chat dinta hankalin ta kwance ,
Tana zaune taga kiran wata yar ajin tasu shamssiya dan haka ta dauka cike da Murna
Ke Sham Ykk shukura ta fada Tana dariya
Lafiya lau aman dai zaki zo bikin nan ko aman yanaji ji kamar a gida ko home service za a yi miki ne shamsiya ta tambaya
Home service kuma bangane ba shukura ta tambaya cikin rashin fahimta
Eh Ina nufin mai make up din dazata miki har gida zatazo ne saboda naji ko kamar a gida bayan kowa yana can gidan makeup kısan fa yanzu abunda ake yayi kenan ba a zuwa gidan biki haka kawai fuska kamar dodo ta fada Tana yar dariya
Shiru shukura tayi na dan wani lokaci ita wlh ta manta da wani Abu wai shi make up gaba daya bata saka shi a lisafi ba kuma a yarda shamsiya take magana gskia idan batayi ba zataci baya sosai
Kinyi shiru shukura ko dai bakida kudi ne tayi dariya
Shukura ce ja tsaki sanan tace ke banason rainin hankali ke kinsan ni Nafi karfin wani kudin makeup kawai dai Ina tunanin gurin wace zanje ne ke wajen wa zaki je
Ni ae gurin beejay zanje shamsiyya ta fada tana yar dariya
Nawa take yi ne shukura ta fada cike da tsoro
Dubu a shirin ne kawai shamsiyya ta bata amsa
Saida gaban shukura ya fadi dataji an ambaci wanan kudin aman saita wayance ta ce ke shamsiyya ni make up dinta bai mun ba samo mun wata sainaje
Shamsiyya yace tace toh akwai wata Salma touch ki dubata a instagram sai kije can itama ta iya sosai ni kawai sai mun hadu a gurin bikin yanzu anzo kaina sai anjima ta kashe wayar ta bar shukura rike da waya a hannu
Innalilahi yanzu ita wani jaraba ta saka kanta gashi bata so ayi mata kallon raini a gurin bikin ta dafa kanta tana tunanin mafita
Wayar ta ta dauka ta shiga instagram ta na duba Salma touch din , ba wahala ta gano account dinta ta ga kwali yar da take , manyan mata taci karo da su a page din anyi musu make up masu kyau nan ta dauki numbern wayarta ta Kira ta tana addu ar Allah yasa kartaji kudi dayawa
Bugu daya biyu Salma ta dauka tana hada wa da salama
Amsa sallamar tayi sanan suka gaisa
Shukura ce ta fara magana
Dan Allah daman make up zan tambaya nawa ne kuma a ina kike
Au toh casual dai dubu 15 ne sanan kuma a kano nake zoo road yaushe za ayi miki
Gaban shukura ne ya fadi aman sai ta kuma dake wa a karo na biyu ta nisa tace toh shikenan zanzo yanzu idan nazo zoo road din zan Kira ki saiki Kara mun kwatance sosai
Toh shikenan sai kin zo Salma ta fada suka kashe waya
Shukura ce ta saki wani nauyayan ajiyar zuciya sanan tayi tagumi ita yanzu Ina zata samu dubu 15 ta bawa mai kwaliyya kodai fasawa Zanyi ne
Wata zuciyar ta ce tab ki fasa a raina ki ko raini ne zaki sha shi
Tsaki taja ta je ta dauko jakar ta changine kawai a ciki da zai mata kudin mota taja tsaki bayan ta gama Kırga kudin
Dakin aliyu ta shiga da sauri tana duba alhajinun kayan sa , nan ta ci karo da dubu 5 a wani Kaya daya cire shekaran jiya , ta ja tsaki bayan ta Kırga kudin yanzu mutumin nan yanada dubu 5 aman ya boye yaki bani wani kudin Kayan miyan Dana jiya ya kone toh wlh saina raba sa dashi ta fada tana nana de kudin
Wata zuciyar ce tace idan ajiya aka basa fa , oho dai ta fada a filli can ta maste masa ni cewa Zanyi banga kudi ba ta fada tana maida Kayan inda ta gansu sanan ta saka Kai ta fice daga dakin dan shiryawa
Dakinta taje ta shirya cikin Kayan data yo aro gurin Hafsa sanan ta saka şarka da dan kune da ta ara gurin sumyah ta dauka mayafin ta wanda ta siya wacan sallahar da kudin cefane da ta tara
Tsaf ta fito kamar matar wani hamshakin mai kudi ta sakar wa kanta murmushi bayan ta kalli madubi ko a haka ta tafi tayi masifar kyau dan shukura akwai kyau ga iya daukar wanka ko Kaya masu arha ta saka sai ta fito tsaf da ita bare masu tsada , ta fito tana ta yanga ta rufe gidan sanan ta fice ba Neman izinin aliyu ....
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...