Ramin karya 06

34 1 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 0️⃣6️⃣

Huda na karsawa titi ta fara neman abun hawa saidai bat samu abun hawa dai dai da kudin ta ba , daga mai ce mata hamsin sai Dari Karshe dai hakura tayi ta fara takawa da kafafuwanta har ta zo makarantar dan idan ta basu gaba daya naira hamsin din batada kudin kari idan aka fito break a makaranta dan haka ta gwammace ta taka a kafa har makarantar.

Tana zuwa makarantar lokacin har an shiga first period ta ci sa a kuwa ba ayi bulalan latti ba dan haka ta shige aji da gudu dan a ss3 take yanzu sun kusa ma Zana waec dan haka bata wasa da zuwa makaranta dan burinta shine taganta a jami a itama irin na wata makociyar su farida tana makarantar ABU na Zaria ,shiyasa karatu take ba Kama hanun yaro dan sosai tana so itama ta zama babbar  yarinya ta samu ilimi karta kare kamar jummai mahaifiyar ta ...

Tana shiga ta tarar da malamin English dinsu yana rubuta a allo , alamun shigowa yaji dan haka ya dan juya dan ganin ko waye yake shigowa

Good morning sir huda ta fada tana risina wa ,

Murmushi ne dauke a fuskar corper Faisal yace ya amsa gaisuwar

Waje ta samu ta zauna tana fito da littafin ta dan fara rubutu ,  wace suke zama tare zee tace sai yanzu hüda har an kusa gama darasin farko ,

"Uhm zee Kenan ke kinsan halin gidan mu ae , yi miki bayyani ma abunda ya saka na makara bata baki ne

Zee ce ta gyada Kai sanan tace hakane Allah ya kawo miki karshen abun kinji

Ameen zee huda ta amsa tana fara rubutu

Shiru sukayi suna kwafar note din har Corper Faisal ya gama yayi musu bayyani dala dala sanan aka kada kararuwar shiga wani sabon darasin dan haka ya tatara kayan sa ya musu sallama ya fita

Duk darasin dayake musu idon sa da hankalin sa na kan huda dan sosai yake sonta saidai har yanzu bai San ko ita wacece ba kuma taki yarda ya san gidansu a makaranta suke hadu wa abunsu , yanzu dai Şoyaya tayi karfi har da alkawari aure yayi mata sanan  ya mata alkawari ma zai shige mata gaba wajen samun gurbin karatu a jami a

Shi corper ne nysc suka yi posting dinsa Zuwa garin adamawa daga garin Zaria dan haka tunda yazo ko gida bai Kara komawa ba yace sai ya gama sanan zai tafi,

Faisal dan babban gida ne a garin Zaria dan mahaifin sa alhaji usmanu babban dan kasuwa ne a garin Zaria da yayi fice a shigowa da shinkafa , mahaifiyarsa kuwa Hajiya Safiyya mace mai kyau da Gayu saidai ita mastalar ta daya bata san talaka yaranta uku kaçal daga yayan Faisal Abdülrahman sai Faisal sai auta rukayyatu suna kiranta da rukky. Tun tasowar su Hajiya ta ke musu huduba da karda su kuşkura suyi mu amula da yaran talakawa dan haka sun taso da tsanar talaka aman Faisal ya fita daban dan shi bai dauki wanan huduba ta haj safiya ba shi ba ruwan sa

Abdülrahman wato baban yayan nasu ko da yatashi aure saida ya duba yar manyan mutane sanan ya aura , ai kuwa haj safiya tayi bajinta tun daga hada lefe da biki na kece raini da akayi a garin Zaria saikace ana bıkın yan gidan shugaban kasa , alhaji usmanu kuwa ya nuna baya so aman haj ta daka tsale ta dire tace ita bata yarda ba sai anyi haka ya hakura ya kyaleta ya zuba mata ido

Faisal kuwa bashida burin auren yar masu kudi kawai dai wace yake so take sonsa mai hankali da ilimi ita yake burin aura aman dukiya bata gabansa

Itama ruky ta taso cikin tsanar talakawa dan haka take rahsin mutunci son ranta Tasha buge mutane da mota idan ta fita tun alhaji na mata fada har shima ya zuba mata ido dan kuwa haj safiya ta daure mata gindi Faisal kawai take tsoro dan akwai ranar da aka kawo masa kararta bayan ta mari wani datijo aikuwa ba karamun duka Faisal yayi mata ba har aka kwantar da ita a asibiti

Haj safiya kuwa daure mata gindi tayi ta ci ma Faisal mutunci kuma ta gargade shi da karda ya kuskura ya kara shiga sabgar rükky duk abunda zatayi babu ruwan sa

Fushi da takaicin abunda mahaifiyar tasa tayi masa yasa ka ko da ya fito daga camp akayi posting din sa adamawa bai nemi yin relocating ba ya gwamace ya zauna a can kuma bazai dawo ba har sai ya gama wanan abun kuwa ba karamin takaici ya saka haj safiya ba aman ta Kyale shi dan kuwa Faisal akwai taurin Kai ...

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now