Ramin karya 31

26 1 0
                                    

RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book

WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣1️⃣

Koda huda ta tafi rumfar kasuwar su gaba daya jikinta ba lakka, jikinta yayi sanyi sosai komai da take yi a sukwane , a haka dai har suka gama abunda zasu yi suka koma gida bayan magariba,

Preety kuwa bayan an ajiye su Zee takira Samir aman yaki dauka dana haka tace da driver dinta ya kai ta gidan sa , driver yau gaba daya ji yayi kamar yace bai zai kaita ba dan shi gaba daya jikinsa yaki aminta da zuwan gidan datace yakaita duk da ba yau ya saba kaita ba ,

Bakajina ne nace ka kaini gidan Samir ta fada cikin masifa , ranki ya dade kiyi hakuri naji aman wai da nace kodai

Kodai me motar ta babanka ce ta fada a hasale, aa hajiya Allah ya baki hakuri driver ya fada yana sunkuyar dakai dan yau ne Rana ta farko da prerty ta masa wanan zagin,

Muje tunda mota ta ubana ce maganar banza kawai ta fada Tana danna wayar , haka driver yaja mota badan ransa ya so ba yayi hanyar gidan Samir da ita suna tafiya tana ta trying wayar aman daga baya ma kashe wa yayi dan ta dameshi

Ashar ta saki tana kallon wayar sanan tace lalai ma guy dinan wato ni zai kashe ma waya bayan ya hadani da abun kunya wlh saina fasa masa kai kai driver ka kara gudu naga kana wani tuki kamar wani mai Jin bacci

Shiru driver yayi bai tanka ba saidai kara gudu da yayi , nan da minti kadan sai gasu su a gidan Samir , sukayi horn mai gadi ya bude dan yasan itace sanan suka shigo, preety ce ta fito daga motar ko rufewa batayi ba ta nufi cikin gidan cikin baccin rai tana mazurai

Tana tura kofar falon taga wayam sai jaka Akan kujera da takalmi na mace dan haka bedroom din ta nufa tana kissima rashin mutuncin da zata Shuka ma Samir indai tagansa da wata

Tura kofar bedroom din tayi tana kiran sunansa cikin masifa, wata mace ta samu a kan gadon tana danna waya shikuma dai dai nan Samir ya fito daga toilet rike da towel a hanunsa, au ananata zakaci Samir prerty ta fada tana kallon sa , tabe baki yayi yana kallonta yace wai ke bakida hankali ne ke wace irin mahaukaciya ce kin kira ni na kashe waya tabbaacin I don't want to talk you aman kanki dake ba tunani kin kamo hanya kinzo mun gida for what ? Me zan miki

Darıya prerty tayi wanda za a iya cewa na takaici ne sanan tace wlh karya kake ka fadamun magana bayan ka cuceni kamun ciki shine yanzu zaka dawo gurin wanna mai Kama da kazar ni kenan ka gama Dani toh wlh bazan yarda ba ,

Ke don't call me that name yarinyar ta fada tana dagowa daga kan gadon dan ma bahaushiya bace ba

Samir ne ya kalli yarinyar sanan yace let her be keesha barta  , she is insane, oo nice banida hankali ko Samir wlh zaka ga rashin hankali nan ta waiga ko zata ga wani abun duka aikuwa ta hango belt nan kuwa ta dauka ta hau tsakiyar gadon ta shiga labtama yarinyar nan kuwa yarinyar ta hau ihu dan sosai tanajin shigar belt din dan ba kaya a jikinta

Preety ji tayi ma gaba daya belt din ba ya mata abunda take so dan haka ta Wurga shi gefe ta shiga dukan keesha da hanunta dan prerty badai karfi ba

Samir ganin abunda yake faruwa ga prerty ta Danne keesha da duka sai ihun neman agaji take ya saka ya nufo su yana Jan preety a haka ya samu ya janye ta , keesha ta sauko daga gadon tana neman rigarta, tayi kuwa nasarar saka rigar ta fara magana dük bakinta jini prerty ta fasa mata baki nan kuwa ta sauka kasa da gudu dan samun hanyar guduwa ta bar gidan dan tasan preety ta kwace daga riqon da Samir ya mata ba makawa saita aikata lahira

Prerty kuwa sai dukan Samir take da hannu Akan ya sake ta aman yaki aikuwa ta shamace shi ta gansatara masa çizo nan kuwa ya saketa yana ihu dan cizon ya shige sa sosai,

Pretty ta gudu ta nufi kasa nan kuwa tayi sa a ta gamu da keesha bata bar gidan ba , aikuwa ta shako ta ta shiga duka nan suka fadi a kan kafet sai naushi prerty take kaima keesha itakuwa sai ihu take , hannu keesha ta shiga laluba tana neman abunda zata kare kanta aikuwa hannunta yakai kan wuka da suka yanka apple itada Samir suka dora Akan tebur din dake tsakiyar falon, cafko wukar tayi ta caka ma prerty a wuya

Wani gigitacen kara pretty ta saki wanda da gudu Samir ya sauko , su driver da maigadi na waje suna dan hira suma sukaji ihun prerty dan haka da gudu suka shigo falon idonsu ya sauka Akan preety dake kwance jini ya bata ta sai numfashinta dake kokarin fita gaba daya daga jikinta

Keesha ihu ta saki ganin abunda tayi ta shiga kuka tana magana chai Jesus wetin I do , i don kill person hai Jesus ...

Samir ne ya kalli keesha yace keesha kisan kai hai kin kashe ni dai dai nan driver din prerty cikin Tashin hankali ya karaso inda preety take ya sungume ta bai damu da jinin dake ambaliya ba kamar an yanka dabba, ya fita da ita yana ma maigadi magana Akan karda ya bari su fita wlh suka fita shi za a kama

Mai gadi bude ma driver yayi gate din jikinsa na Rawa. Da gudu driver yaja mota ya bar gidan ya nufi asibiti da ita sukuwa su Samir kuka suka shiga yi suna daurawa juna laifi ganin hakan bazai fitar dasu ba keesha tace dan Allah ya mata hanya ta fita tabar gidan

Kin İsa ma Samir ya fada yana wurga mata wani kallo , wlh kece kika kashe ta dan haka kece zaki amsa query bani ba idan akwai wanda ya kamata ya gudu ma ae nine dan kar laifin ki ya shafe ni banza kawai marar imani ya fada yana harara ta

Hai am died keesha ta fada tana dora hana yenta a kanta ,

Kai tsaye driver asibiti ya kaita aman suka ce su baza su karbe ta ba sai dole an kira yan Şanda , nan da nan driver ya Kira yan sanda nan aka shigar da preety emergency sukuma yan sanda da driver suka nufi gidan Samir , kira ne ya shigo wayar driver yana duba wa yağa sunan alhaji gabansa ne yayi mumunar faduwa , yaushe alhaji ya dawo Innalilahi sai yau ya yi nadamar biyewa preety yana kaita yawo bayan alhaji ya danka masa amanar ta aman ya ci amanar alhaji yanzu gashi abunda ya faru da yarsa yanzu mai zai ce masa

Wani kiran ne ya sake shigowa a karo na biyu , çıkin tsoro ya dauka , daga bangaren alhaji yace kai wani ina kaje ne nadawo aman ance har yanzu baku dawo ba naje school din sunce tun safe yau aka tashi masu jarabawa meyake faruwa Ina yarta wayarta ma yaki shiga

Ajiyar zuciya driver yayi sanan yace alhaji akwai mastala sosai aman yanzu muna hanyar zuwa wani guri dan Allah kazo yayi masa kwantance

Nan alhaji hankalinsa ya tashi ko tambayan driver bai tsaya yi ba ya figi mota yayi hanyar gidan da yayi masa kwantace jikinsa na rawa dan jikinsa ya başa prerty ba lafiya ba ......

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now