RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book
WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 41Muryar Jumai ne ya doki dodon kunnenta tana magana cikin fushi, au Huda wato zaki koma irin rayuwar ki tada ko ni Huda kike kin kulawa ko babu Komai ki bude kunenki kiji ni da Kyau Wlh , daga yanzu indai baki tura min kudi ba ba ina nufin kudi mastiyata ba aa kudi masu sunan kudi nakeso idan Kuma baki turamun ba Wlh yau zan kwashe miki albarka bani bake ki nemi wata uwar aman bani ba ehe tana gama Fadan hakan ta kashe wayar tana mita
Huda Shiru tayi hawaye na Zuba daga idanuwanta, Haka ta kwanta tana tunanin mafita, karfe 12 na dare Zee suka shirya itada sadiya dan fita dan yau akwai babban bako a club din da suke zuwa , dan haka yau suka shirya dan zuwa samun rabonsu dan ance Za a samu kudi masu yawa
Huda kallonsu tayi lokacin da take ji suna zancen irin Kudin da suke expecting samu dan Haka ta gyara zama tana kallonsu, sanan tace Zee dan Allah yau nima zanje Wlh ina bukatar kudi
Zee cikin mamaki ta kalleta sanan ta kalli Sadiya wace Itama ita take kaloo, Zee kinyi shiru kina kallona , aa ba dole na kalleki ba Huda nadauka ae yanzu kin zama ustaziyya mene na bin mu. club yau kuma
Huda ce tace dan Allah nidai kutafi Dani duk wani bayani zanyi miki daga baya
Sadiya ce tace ba komai shirya kawai, Huda cikin jin dadi ta hau shiri tana sauri , rahma ce ta kalli Huda lokacjn da suke shirin fita tace Huda dan Allah karki sake jefa rayuwar ki cikin damuwa dan Allah
Huda tayi murmuhsin takaici sanan tace rahama kenan Wlh Ina cikin tashin hankali ba yadda zanyi dan Allah ki bar ni nayi koma menene na tabbata Allah zai yafemun
Rahama ce tace aa Huda this is wrong wlh dan Allah ki zauna, Zee cikin fushi ta finciko hannun Huda sanan tace ke rahama Wlh ke yar bakin cikin ce ke zaki kula da rayuwarta ne kina fama kema da kanki ko Yaya tunda ke kina da masu miki ke yar gata ce kibarmu mu nemu na kanmu muma tana gama fadin hakan ta janyo hannun Huda suka fita daga dakin
Rahma kwanciya tayi tana tausaywa Huda itama marainiya ce kawunta ne yake kula da karatunta da itama tasan tabi hanyar dasu Zee din suke kai
A club Kuwa sosai ake ruwan nairori yan Mata kuwa sai rawa ake kamar macizai Haka Huda da su Zee suka Dage suna nuna tasu bajintar aikuwa sunsha liki Haka suka tashi da kudi masu yawa sai ana kiran sallar asuba sanan suka tafi makaranta kowace a gajiye
Da safe kuwa bacci suka dinga yi kamar matatu saida sukayi mai isar su sanan suka tashi suka shiga hirar kudin da suka samu, Huda kuwa Jumai ta tura ma rabin kudin sanan ta rike sauran aikuwa tasha albarka, nan ta sake kiran number din goje daya baramata ranar nan aman har yanzu magana daya ce dai a kashe dan Haka ta shiga tunanin ko lafiya Haka dai ta Kauda tunanin ta shiga tunanin wani abun daban a ranta tana addu ar Allah yasa dan uwanta yana lafiya
Tundaga ranar duk hanyar samun kudi da zuwa club yazama jiki a gurin Huda dan ba karamin samun kudi take ba , nan fa aka santa ta fito gari sai kuma maxa kowa Huda hakan kuwa ya saka Sadiya da Zee sake jin hashinta dan duk samarin sunfison hudar
Kudi kuwa Huda har kyautar sa take yi batajin komai , komai dinta ya chanza Huda anzama babbar yarinya
Wani Hutu da takoma gida kuwa saiga goje tayi farin ciki sosai nan ya shiga Mata Nasiha akan tayi karatu kanwata yace yana kallontab
Na am goje Huda ta amsa
Kiyi karatu Kinga idan kiga gama kika samu aiki mai kyau sai aure shikenna ke kinfita daban cikin Gidan nan Wlh zan fi kowa farin ciki ko baba Allah ya jikansa nasan zaiyi fahari da ke kinji hudallah
Kwalla ne ya fito Mata saidai cikin dabara ta goge tana murmushi
Insha Allah goje zan yi yadda kace , shikenan Huda nan suka dinga hirarasu
sanan ya bata kudi ya tafi abunsa yana murna da karatu da yar uwar tasa ta saka gaba nan fa Huda taji ba dadi da chanza tsarin rayuwarta wace bata jin Zata iya dainawa dan yanzu maxa da kudi sun zame Mata jiki bazata iya rayuwa babu su baBayan wani Lokaci yanzu har mota huda takeda dan Haka sosai Zee take jin haushi dan Haka yanzu ma bata kula Huda saboda takaici Sadiya kuwa yanzu an koreta daga makarnatar dan Haka yanzu da Zee suke gasa dan rahama bata shiga irin rayuwar
Yau tunda Huda ta tashi take jin jikinta babu dadi dan Haka ta kwanta kamar Marar lafiya tana ta tunanin rayuwarta wata number ce ta shigo da kamar bazata dauka ba saikuma ta dauka tana lunshe ido
Hello taji muryar wani mutum, wani iri taji a muryar aman saita basar sanan tace hello waye wai
Huda ce ko ? Mutumin ya tambaya
Eh I tace ' Huda ta basa amsa a takaice
Okay I want you tonight ni ima hotel room 205
Shiru Huda tayi har saida takuma jinsa ya maimaita abunda ya fada
Har zata ce bazata zo ba sai kuma wata zuciyar tace aa kawai taje
Okay zanzo kawai tace sanan ta kashe wayar
Da kyar ta mike ta hau shiri zata fito kenan taga rahama, rahama ta kalleta cike da tausayi tace Huda dan Allah ko ina zakije yau ki fasa jikina yau yana bani ba qalau ba nayi mumunar mafarki gameda ke
Murmushi Huda tayi sanan tace kai ramatu kin taba ganin mafarki ya zama gaske ke kin cika zolaya Wlh yanzu zanje na dawo ba jimawa zanyi ba kinji ko tana gama fadin Haka ta wuce tana dariya
Kamar ta dawo kuma saidai ta shige ta tafi ta bude motar ta taja, tana zuwa ta wuce reception sanan ta tafi dakin bayan an sanar da mutumin kwankwasa kofar tayi sanan ya bude ta shigo
Mutum mai kyau da kamala nan ya Mata iso sanan ya kalleta yace Huda ko
Eh ta daga Kai tana kallonsa ta rasa meyasa taji gabanta na faduwa
Nan yace ba komai zaki mun ba sai abu daya kuma ba jikinki nakeso ba kamar yadda na nace ko kike tunani
Mexan maka Haka Huda ta fada tana kallonsa
Tashi yayi sanan ya Cire rigarsa ya juya baya nan Huda taga wani abu mai tayar da hankali wanda bata fata sake ganin irin abunda tagani a rayuwar ta ......
Mrs abba
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...