📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustaphaWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣1️⃣Jummai ba abun da kike tunani bane fa huda ta fada Tana shirin yima jummai bayani
Ke dallah nace ki wuce kije kici abinci mene haka wai jummai ta daka ma huda tsawa
Ba shiri huda ta rufe bakin ta sanan ta wuce ta dauki kwano ta zubo abinci ta zauna ta fara ci harta ta ko shi sanan ta mike zata wanko kwanon
Jummai ce ta dakatar da ita ke huda yauwa nawa ya Baki zauna ki bani su na kirga jummai ta fada Tana washe Baki ta na mika ma hanunta alamun ta bata kudin
Huda ce tace jummai wlh ba kudi ba saurayina bane ba su direba din su zee ne shine suka rage mun hanya
Salati jummai ta soma Tana tafa hanayenta sanan ta rike baki lallai huda shine kinsan ba wani kudi dazaki bani kika saka na baki abinci na kika ci kika koshi to wlh Sai kin biya
Huda ce ta rausayar dakai sanan tace dan Allah kiyi hakuri jummai wlh ba haka bane ba kuma nayi niyan miki bayani ke ce baki tsaya kin saurara ba
Rufe mun Baki shegiyar yarinya jummai ta fada cikin masifa maza maza bani kudina ko na Zane miki jiki wlh ta fada cikin daga murya
Alhaji garzali ne yazo runfar jummai zai siya abinci yaga abun da yake faruwa daman ya dade yana yiwa huda Tayin soyaya Aman taki basa fuska dan haka bai bata lokavi ba ya yi guaran murya sanan yace hajja jummai wai lafiya mai yarinyar tayi ne haka
Jummai cikin fushi tace wai wanna yarinyar ni zata yaudara tacimun abincina taki biya
Cikin mamaki alhaji garzali yace kamar yaya jummai ba yarinyar ki bace ba idan taci abinci saita biya ne
Jummai yanzu kuwa ankaita bango dan haka cikin fushi da daga murya tace dallah alhaji idan ba zaka fadi magana mai ma ana ba kayi mun shiru kayi abunda yakawo ka ka barni da yarinyar nan
Alhaji murmushi yayi sanan yace ba komai jummai nawa ne kudin abincin data ci zan biya ki
Dubu daya ne da darı biyar jummai ta fada Tana hura hanci
Shikenan ki bata ta kawo mun abincina idan zainabu ta zuba zan bata kudin gaba daya jummai
Washe baki jummai tayi sanan tace Nagode fa alhaji Kai daman na daban ne wlh
Murmushi alhaji garzali yayi kawai sanan ya kalli huda kaloon su na yan bariki sanan ya juya gün zainabu wace ta tsaya Kallon ikon abunda jummai take ma huda kamar ba yar cikin ta ba Tana mamakin hali irin na jummai kullum abun nata kara gaba yake
Alhaji ne yace zajnabu kinji abund nace idan kin zuba saiki bawa huda ta kawo mun shago ko babban shagon zata kawo
Kanta kawai zainabu ta daga sanan ta juya Kallon huda wace kanta yana sunkuye Tana Jin zuciyar ta na tafasa
Badariya ce ta bude baki da niyar yima jummai magana tunda alhaji yabar wajen aman zainabu ta dora yastar ta a leben ta alamun tayi shiru karta yi magana dan Tana jiye mata tijarar jummai
Badariya shiru tayi dan tagane abunda. Zainabu ta nuna mata dan haka ta sunkuyar da kanta kasa Tana jinjina lamarin jummai
Ke bazaki juya ki maida hankali ba ki zuba masa akai masa kin tsaya kına Kallon mutane wlh zainabu ki kiyaye ni jummai ta fada Tana yiwa zainabu Kallon banza
Yi hakuri zajnabu ta fada Tana mai da hankalinta ga zuba ma alhaji garzali abinci
Ke kuma banza wawiya idan kinje karkiyi abunda zai kara miki kudi ki tsaya kamar wata sakarya marar wayo kawai jummai ta fada Tana kaloon huda wace har yanzu kanta yake a sunkuye
Sum sum huda ta ta tashi ta isa gurin zajnabu Tana jira ta gama ta bata ta tafi shagon alhaji garzali dan Kai masa abincin
Jummai kuwa cewa tayi ita zata shiga cikin kaşuwa tayi wasu siyaya Tana zuwa nan suka Gyada Kai suka mata a dawo lafiya
Bata amsa ba illa harara data bisu dashi sanan ta wuce abunta buguzum buguzum
Zainabu ce ta Mika ma huda abincin sanan tace mata yace karamun shagon zaki Kai masa dan Allah huda ki rike mutuncin ki wlh alhaji garzali ba wani mutumin kwarai bane ba kinji
Gyada kai huda tayi sanan tace nagode zainabu saina dawo
Tom a dawo lafiya huda zajnabu ta fada Tana bin huda da Kallon tausayi har ta bar wajen
Zajnabu ce ta masto inda badariya take sanan tace kinga badariya idan kina son kanki da arziki wlh kibar fada ma jummai gaskiya duk wani abu da zaki ga tanayi kedai ki zuba mata ido idan ba haka ba wlh ba goje ba koma waye idan jummai ta şaka ki a gaba Sai kin bar mata rumfa wlh nice nake Tare da jummai tin ba yau ba nice nasan halin ta dan haka ki rufawa kanki aşırı ki daina shiga lamarin jummai nidai na fada miki kinga bara naje karbo kwanuka cikin layın nan a wanke kafin jummai ta dawo ta zage dangina kaf
Zainabu na gama fadin haka ta tashi tayi wani layi dake kallon rumfar dan karbo kwanunkan su
Badariya shiru tayi Tana juya maganganun zainabu tabbas Tana son ta cigaba da neman abinci a rumfar jummai bata shirya barin wajen ba dan haka zata iya bakin ta akan abubuwan da zata gani
***********************************************
Shakura kuwa gidan sumaya ta nufa Tana hade girar sama da kasa ita dole batasan raini
Tana zuwa falon ta shigo ba ko salama sumaya na zaune da kawar ta ta ga shigowar shukra ba salama dan haka cikin fushi ta mike Tana kallon shukra
Ke mene haka wai kanki daya kuwa ? Kallon sama da kasa shukra tayi ma sumaya sanan ta tabe baki ke ni ba wanna bane yakawo ni shukra ta fada Tana harara sumaya dan Tasha alwashin saita rama rashin mutuncin da sumaya tayi mata dazu
Ga tsiyar ki mastiyaciya wace bata san arziki ba ta wulla mata kudin a daidai kafarta nan suka waste kowane kudi yayi hanyar sa a falon
Kawar sumaya ce ta mike tsaye sanan tace ke tsaya wanna ba ke bace ba kika mun fake transfer ba
Shukura tayi wiki wiki da ido Sai yanzu ta lura da mai kwaliya dake zaune tabbas wace tace ma ta tura mata kudin ta ne
Sumaya ce ta saki dariya sanan tace kawata daman itace kike bani labari akan ta miki fake alert kai wanan abu yayi mun dadi sumaya ta fada Tana dariya ......
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
KurzgeschichtenYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...