Ramin karya 43 last page

5 0 0
                                    

RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book
WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 43 last page

23/11/2024

Look yan mata daga million daya har million goma zan iya baki aikin ki kawai ki lashe mun wanan dan ciwon mutumin ya fada yana kallon huda wace ta kule idonta sakamakon mugun ganin datayi dan kuwa wani irin ciwo ne a bayan mutum din kamar zane gashi ba kyaun gani har wani gashi gashi yake da wani kore dayan bangaren kuwa kamar danyan nama haka yake

Ki Bude idonki yan mata wanan aikin mai sauki ne idan kuma kikayi taurin kai wlh sisi baxan baki ba kuma saikin lashe tas ya fada fuska a murtuke

Huda sai lokacin ta bude idonta tana kallonsa ae ba shiri ta nufi kofa ciki sa a ta samu a bude saidai tana murdawa taga wani garjajen mutum baki mai kirar samudawa fuskar nan ba annuri dauke da bindiga nan ta ja da baya tana dafe kirji

Cikin muryar tashin hankali da kuka ta fara magana dan Allah kumun rai dan Allah karku cutar dani na hakura da koma mene zaku bani wlh banaso ni wlh daga yau ma nadaina karuwanci daman ba son raina bane ta fada tana fashewa da kuka

Shii mutumin daya shigo ya fada alamun tayi shiru cikin hausar sa da bata gama nuna ba yace koma ki yi abunda oga ya saka ki or na harbe ki yanzu nan so decide yan mata

Kuka da magiya huda ta shiga yi nan fa ya kuma saita bindigansa kanta yana shirin harbin ta nan huda ta fara magana cikin rawar murya zanyi zanyi wlh.  Zanyi dan Allah karka kasheni

Okay fine juya and start ya fada yana nuna mata bayan alhaji, nan alhaji ya kwanta haka huda tanaji tana gani ta soma lashe ciwon nan tas tana jin amai haka ta danne yau bala in ta saka kanta kenan saboda biye ma zuciyarta haka dai ta lashe shi tas

Alhajin cikin jin dadi ya shiga murmushi sanan ya tashi lokacin huda ji take kamar ba a duniyar nan take bama tsabar yadda jikinta yake rawa ga hankalinta yadda ya tashi amai kawai takeso ta yi aman tsoro ya hanata yi

Murmushi alhajin yayi sanan ya kalleta yace kiyi hakuri fa kinga wanan ciwon bayan wata daya zai sake dawowa kuma wanda yafi wanna muni kuma dole na nemo mace mai kyau da taurarinta suke haskawa da wanan ne kudina zai dinga habaka

Sanan ga wanan kudin ya bata wani jaka sanan yace kudine har naira miliyan 10 idan kinyi sa a zaki iya kashe kwatar sa kafin rai yayi halinsa I wish zan iya miki karin bayani aman dai lokacine kawai zai bayyana koma menene sai watarana ko ga kofa nan zaki iya tafiya

Ae yana gama fadin hakan ta janyo jakar ta fita a guje sai waje, tana fitowa ba wahala ta samu napep dan haka ta shige tana Allah Allah ta ganta a makaranta

Koda tadawo bandaki ta wuce tana ta karalaya amai kamar zata fito da hanjin jikinta sanan tayi brush ta dawo ta kwanta tana maida numfshi ba yadda su rahma basuyi ba ta fada musu abunda ya sameta kuma sanan daga inda take aman taki kuma taki cewa komai ko abinci taki ci saidai hawaye take ta yi da dare ma yadda taga rana haka taga dare

Da kyar tayi bacci da asuba shima mumunan mafarkin datayi ne ya saka ta farka ba shiri tana ihu sai kuma ciwon ciki Wanda bata taba jinsa ba a rayuwarta ya fara

Makogoranta ya shiga Zafi nan ta hau ihu su rahma suka farka suka yo kanta suna tambayan lafiya

Nan tace ruwa ruwa nan aka bata Abu kamar wasa ya koma abun tsoro sun suna dauko ruwa suna bata tana shanyewa zata kuma cewa ruwa a haka sai da ta shanye leda daya

Nan fa hankalinsu ya tashi suka shiga tambaynta meyasameta aman Abu daya take cewa cikina makogaro na ruwa

Haka dai suka yanke hukuncin kawai a kaita Kano nan fa aka nemi mota aka taatara mata kayanta sai adamawa

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now