Ramin karya 39

13 1 0
                                    

RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book
WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣9️⃣

Ae yanzu ma na gama hada kudina tsaf gida nasamu a wani GRA zan siya mai shegen kyau samira shukura ta fada tana dariya nan idan kaganta bazaka itace wanan shukurar ba tayi kyau tayi fari tayi kiba babu abunda ya dameta duniya kawai ta saka gaba yanzu haka tanada mota gida take shirin siya dan tagaji da gorin da ilham take mata na tanada mota aman batada gida yau tana hotel gobe tana gidanta shine yanzu zata siya gida na gani na fada dan ta huce haushi, mahaifiyarta kuwa bata sake sakata a ido ba tun ranar nan barantana aliyu wanda tama shafe tarihin sa cikin rayuwarta yanzu ta sana arsu kawai take, maxa kuwa sai wanda suka tada kai naira take kulawa a cewar ta yanzu bazatyi soyayar wahala ba balantana auren wahala

Da yamma kuwa haka shukura ta Lale kudin gida ta biya ta shige gidan tana ihu tana Murna tana mamakin wai itace yau ta malaki wanan gidan shukura wace mai adaita sahu ya kusa duka sbaoda kudin napep shukura wace Mai makeup ta tozarta akan kudin makeup, har sarkar sumaya data bata da suraya tamata rashin mutunci da tijara akai yau wai itace ta malaki wanan gida mai kyau da tsari ashe itama zatayi arziki, ashe itama zata zama hajiya shukura wayar ta ce ta kaste mata tunanin da take can ta duba tana tsaki

Kanwarta ce dan haka ta dauka tana yastina fuska dan duk zaton ta kudi zata tambayeta

Hello shukura mama ce fa ba Lafiya kuma tace tana son Ganin ki dan Allah kizo

Tabe baki shukura tayi Sanan tace au Allah ya bata lfy yanzu ni kinga hindatu wlh ina abuja baxan samu daman zuwa ba aman idan nadawo zanzo

Hindatu tace dan Allah shukura kizo dan Allah wlh mama na bukatar ganinki sunanki kawai take ta kira ki taimaka kizo

Tsawa ta yima hindatu har said a hindatu ta tsorata sanan tace nace miki bana nan ban gari aman ki dameni haba mana ke mayya ce ne wai

Hindatu bata damu ba ta cigaba da rokan shukura akan ta taimaka aman ko a jikinta daga baya ma kashe wayar tayi gaba daya tana sakin tsaki, ba kiran da hindatu batayi ba aman taki dauka daga baya ma saita saka ta a black list gaba daya

Mita ta shiga yi tana hararar wayar ta shiga magana au saboda sun samun labarin yanzu nayi kudi shine ake so a rabeni bayan irin abunda suka mun toh wlh daidai nake dasu kuma sisi na bazaku ci ba zaku wani fake da mama ba lafiya tsaki ta ja mai tsayi sanan ta cigaba da danna wayarta tana ta dariya abunta cikin nishadi

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tun Ranar bata kara ganin kiran hindatu ba dan kuwa tayi block dinta kuma daga ranar bata sake daukar bakuwar number ba saidai ka karaci kira indai bakuwar number ce aman bata dauka shukura babar yarinya rayuwar ta kawai take ci da tsinke abunta

Yau ce ranar da huda zasu tafi kano dan kuwa angama komai lectures zasu fara Monday dan haka yau Friday suka dauki hanayar kano Bayan ta bawa jummai kudi masu dan yawa ba laifi albarka kuwa jummai ta saka ma huda sau ba adadi haka dai suka dauki hanyar kano suna kewar gida abunsu, driver din alhaji ne zai kaisu dan haka suna baya dukansu sunata hira iatada zee suna jimamin pretty da tuni itama yanzu tana kasar waje tana karatu abunta aman Allah haka ya tsara basuda yadda zasuyi

Sun sauka kano da yamma dan haka gaba daya sun gaji nan suka nemi hostel dinsu dakin yanada girma sun tarar da wata sadiya yar level 300 sai rahama itakuma level 100 take Tara suke kenan kuma department dinsu daya

Rahama tayi farin cikin ganinsu aman ita sadiya kamar dai batayi farin ciki da ganinsu ba dan sai wani hade rai take koda suka gaidata ma ciki ciki ta amsa tana taunar chingum abunta

Kayan su suka fara dan jerawa sanan kowace ta kinsta dan sunsha hanya,

Rayuwar makaranta haka ta cigaba duk abunda  huda take bukata zata Kira alhaji ta fada masa shikuma ya tura mata wanan abun kuwa ba karamun bata ma zee rai take ba aman bata nuna wa

Saidai kwastam suna Zaune labarin rasuwa alhaji ta riske su sakamakon hastarin mota da yayi a hanyar zuwa Abuja

Huda ce mutum ta karshe da sukayi waya dan haka waenda suka tsinci wayar bayan hastarin ya faru ita suka fara Kira suka sanar mata , sosai huda taji mutuwar Allah mai yanda yaso yanzu yanzu suka gama waya ace ba bu mutum ya mutu kai wanan rayuwar ba komai bace ba ranar wuni tayi jikinta ba dadi

Zee data dawo ta samu labarin mutuwar rawa ce kawai batayi ba sosai tayi murna dan tasan karshen samun kudin huda ya kare dan dukda lalata cewa da huda datayi bata yadda da wasu maxan da zee take kawo mata tayin su bayan alhaji sambo sai gashi yanzu ya rasu tasan yanzu dole ne tadawo kan hanyar da takeso ta dawo tunda wanda yake bata kudi ya tafi wanan albishir din dataji ya saka ta manta da bakin cikin lecturer dinsu daya kunsa mata tayi missing test dinsa shine taje dan ta masa yan dabara su ta yan bariki har office dinsa ya samu ya bata marki aman fur mutimin nan yaki yarda daga karshe ma yayi mata alkawarin samun carry over mudin ya sake ganinta a office dinsa haka dai zee ta bar office tana ta Jin haushin sa tana tsine masa a cikin ranta ....


Mrs abba

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now