📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustaphaWhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 1️⃣6️⃣Ba tamayan ki nake ba kin mun shiru aliyu ya fada cikin daga murya , kunga ni waye zai bani kudin şarka na sumayah ta fada cikin fushi
Fadamun abunda ya faru aliyu ya maimaita tanbyan yana kallon shukura
Daman daman daman shukura ta fara magana cikin tsoro dan gaba daya jikinta rawa yake bataso aliyu ya ji maganar ba
Daman me bude Baki ki amsa mun tambayar da nake miki
Eh hakane na arı sarkar ta aman wlh ban san ya akayi ya bata ba kawai na neme shi ne na rasa wlh
Okay da farko me meya aike ki karbar Kayan mutane har talauci na yakai kije Aron sarkar mutane shukura aliyu ya fada muryarsa na rawa cike da baccin rai
Ya kalli summayah baiwar Allah nawa ne kudin sakar
Dubu hamsin ne şarka na ta fada tana hararar shukura wace kanta yake har yanzu a kasa
Wlh karya take bakin ce dubu arbain bane ba shukura ta fada cikin fushi da sauri
Yimun shiru aliyu ya mata tsawa nan take tayi shiru tana wurgawa sumaya harara
Baiwar Allah dubu hamsin ne kudin ki ko dubu arbain aliyu ya tambayi sumaya
Sosa Kai tayi tace dubu arbain ne na siya aman nasan yanzu naje kasuwa dole ne yakara kudi shiyasa nace dubu hamsin ta fada tana kallon aliyu aman dai aka bani arbain dinma zan karba ya Zanyi asara ce tahau kaina
Aliyu ne ya kalli shukura sanan yace an Ina sarkar ta ta fadi a sunan da kika ce kinje jiya ne ?
Shukura ce ta gyada Kai alamun eh sanan
Okay Kira Anty Zara a waya kitambaya ko an Ganshi tunda dai gida neGaban shukura ne ya buga lokaci daya ta sake waro idanuwanta dan tasan halin aliyu ya tsani karya kuma yanzu anzo inda zai San inda taje
Ita tarasa dalilinta nayi masa karya gashi yanzu komai zai kuma dagule wa
Ke fa nake jira ki kira Anty Zara din ni Ina ganin haka shine zai fi sauki dan kin gani nan inda na tsaya dinan Banida wata dubu arbain da zan bada dole ki kira Anty Zara a a ji idan kuma ba a Gani ba dole ki Nemo kudin mutane ki basu
Gumi ne ya shiga zubo wa shukura ta sake sunkuyar dakai Tana tunanin abunyi aman har yanzu ta rasa dabara
Bada ke wai nake magana ba Kira Anty Zara mana aliyu ya sake mata magana
Kayi hakuri ba suna naje ba gidan biki nake Kawata ce take aure a can sarkar ta fadi shukura ta fada da kyar har yanzu kanta a kasa
Au Kenan karya kika mun aliyu ya fada yana mata wani irin kallo
Shukura yanzu Banida abunda zance miki abunda Nasani shine kawai duk inda kudi yake ki nema ki basu dan ni babu kudi a gurina dazan iya Baki yana gama fadin haka ya fice daga gidan gaba daya ya ma manta da maganar kudin musa
Sumaya naganin aliyu ya fita ta saki tsaki sanan ta kalli shukura wace kunya da takaice ya saka ta sunkuyar da kai kasa
Kinga shukura babu abunda ya dame ni da dramar da kukayi keda mijinki ni wlh sai kin bani kudina shine magana kawai ko kuma wlh na je na sanar da hüküma
Nashiga uku sumyah hukuma kuma
Eh mana dole ne naje dan kına gani nan bawai kina mun kallon shiru shiru ba wlh na Fiki danyan Kai dole ki biya ni abuna ehe
Naji sumaya basai kin kawo mun hukuma ba kizo jibi zan baki kudin ki dan Allah kiyi hakuri shukura ta fada tana magiya
Naji aman saidai gobe kibani dan wlh bazan iya jibi ba ehe idan kuma baki yarda ba yanzu yanzun nan naje hukuma kuma kinsan Karshen zancen bugu ne zaki sha shi sanan ki biya abunda yafi dubu arbain
Dan Allah kiyi hakuri ki bar maganar hukuma sumaya naji goben kizo ki karba dan Allah kiyi hakuri ta fada tana yin kallar tausayi dan duk sumayh ta hakura
Naji gobe zan zo karbar kudina Karfe nawa zanzo
Ba tareda tunani komai ba shukura tace kizo bayan magariba insha Allah zan hada miki kudin ki
Naji sumayh ta fada tayi hanyar waje
Tsaki shukura taja tace wanan jaraba saikace gwal na batar za a dinga mun masifa haka harda hukuma
Eh ba gwal bane ba aman naga tunda talauci ya miki yawa dole mana kije aro a fake da siya za ayi taji muryar sumaya ta fada
Toshe bakinta tayi da hanayen ta ta gwalo ido bata dauka magnar ta fita haka ba har sumayah ta ji
Tsaki sumayah ta kuma ja sanan ta bar gidan dan ranta ya bace matuka
Shukura na ganin sumaya ta fita ta saki nauyayan ajiyar zuciya ta zauna ta yi tagumi
Ni yanzu shukura Ina zan samu naira dubu arbain nashiga uku ni shukura
Sako ne ya shigo wayarta ta dauka tana dubawa sako ne daga Facebook hartayi tsaki zata goge sai kuma ta bude dan ita tunda aliyu ya siya mata wayan ta bude su Facebook da su WhatsApp ba hawa take Facebook din ba sai WhatsApp dan haka bata wani duba sako daga face book din
Wani group ne na siyarda laces atamfofi tagani anyi add dinta dan haka ta shiga tana duba wa
Nan taci karo da laces masu kyau sosai saving dinsu ta shiga yi tana tunanin abunda zata yi dasu
Wata zuciyar tace ki daura su a status ki tura su group group ko xaki samu masu siya kema ki zama yar kasuwa
Ae batareda da wani tunani ba ta shiga saving din laces dinan masu kyau sosai
Saida ta gama tsaf sanan ta shiga wani group da tasan na manyan mata ne ya tura musu akan duk mai so yayi magana Tana siyarwa
Nan da nan kuwa wasu suka dinga yaba laces Din Anata tambyan nawa
Murmushi tayi sanan ta gyara zama tana karanta yadda ake ta yaba kayan da tambyan nawa kudin su yake
Amsa ta basu da su bıyota ta private nan kuwa taga mutane kusan biyar sun mata magana akan suna so nawa ne
Numbern wata Hajiya Nafisa ta shiga ta bude sakon ta kusan laces guda bakwai ta tura mata akan tanaso ta fada mata nawa ne
Jiki na rawa shukura ta tura mata da amsa tace dubu Goma göma ne nan take hajiyar tace tanaso sunyi arha sosai dan haka ta tura mata da account number
Cije lebe shukura tayi tana tunani yanzu da batada account ya za ayi hajiyar nan ta saka mata kudin laces dinan ne
Tunani ta shiga yi can ta tuna da Hafsa kawarta tana da account dan haka ta kirata a waya Akan ta turo mata da account number dinta
A bangaren Hafsa kuwa cewa tayi kinga Ina kusa da layin ku na biyo ne nace bara nazo na karbi kayana da kika zo aro dan ke ba a abun kirki dake bara na karaso idan nazo saina baki
Yauwa Kawata saikin karaso Shukura ta fada tana kashe wayar nan ta cigaba da bude sakonin mutane masu mata zancen siyan laces daga mai son uku sai mai son hudu biyar itakuwa sai fada musu kudi take ba tareda tasan kudin kayan ba wani tace masu dubu 10 wani tace dubu 5 su kuma sunga arha banza sai zaba suke suna ta tura musu da account number ....
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...