Ramin karya 02

49 1 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 0️⃣2️⃣

Jummai kuwa tana ganin fitar hüda ta tashi tana mita ta janyo gwangwanin madara da Milo da sugar ta janyo katon buredi data boye a karkashin gadon ta dan kar huda tagani

Katon kofi ta dauka sanan ta hada madara da milon nan hadin kauri ta janyo biredin ta tana ci tana sha harta gama ta saki gyasta abunta sanan ta Mike ta fito ta fara kiciniyar daura girkin abincin da suke siyarwa

Tana zuba waken bayan ta gama dafa waken taji sallamar zainabu yarinyar dake Taya ta girki tadaukar mata suje bakin kasuwar da take siyarda abincin sanan su siyar su dawo da magariba

Zainabu sai yanzu kiga damar zuwa kema ko jummai ta tambaye tana karasa zuba waken a tukunya

Aa jummai kiyi hakuri wlh na tsaya wani abun ne aman bazan Kara ba dan Allah nasan yanzu sai kice zaki rage mun a kudin sallama ta

Jummai ce ta kalleta ta harareta sanan tace eh ga tsohuwar Muguwa ae dole kice mun haka ni wai meyasa kika Raina ni jummai ta fada tana kallon kodake ba laifin ki bane ba laifin shegiyar yarinyar ne huda da ta ajiye wanan karatun na banza da wofi da yanzu anfara saka mu sahun masu kudin garin nan aman ina ita ta nace saitayi boko maimakon tazo mudinga sana ar abincin nan tare da mai Zanyi dake har kina batamun rai ta fada tana rufe tukunyar

Zainabu ce ta tabe Baki sanan tace nidai yanzu jummai kiyi hakuri dan Allah na Baki hakuri yanzu Me zan kama ki dashi

Tabe Baki jummai tayi sanan ta nuna mata waken da hüda ta surfa ta ajiye tace "gashi nan saiki dauka kikai markaden alalar sanan ki dawo ki hura murhun dan wlh bazan yi ba kuma kika dade wlh a cikin kudin sallamar taki zan yagi kudin asarar lokacin da kika mun kinji ni da kyau dai ko ta karasa fada tana kama kunneta

Naji jummai zainabu ta fada tana daukar waken ta fita a ranta tana mamakin halin Jumai na masifa

Tana zuwa kuwa taci sa a ba layi gurin markaden dan haka aka fara niqa mata waken

Tana fita kuwa jummai wanke shinkafa tayi sanan ta dauko su cabbagi ta fara yan kawa tana yar wakar ta har zainabu ta dawo daga markaden

Ke kuma har kindawo ta tambayi zainabu tana tabe Baki

Eh nadawo bara na hura wutan

Wanan kuma ke kika jiyo ta fada tana cigaba da yankan cabbagin ta

Zainabu kuwa bata tanka mata ba dan idan da sabo ta Saba da halin jummai ta hura wutan ta fara hada alalaen tana kulawa a farar Leda

Da wuri suka Kamala dafa shinkafa da waken sai taliya da alala dasu dafafen Kwai da nama sai miya

Suna hada Kayan suka ji sallama , badariya ce yar makotan su ta shigo tana gaishe da jummai

Jummai ta hade rai dan ta dauka zuwa sukayi Rokan ta wani abun dan idan suna cikin wani Hali sun kan zo gurinta watarana ta basu idan yan mutuncin sunzo watarana kuma ta hana kuma bazata barsu a haka ba saita gasa musu magana

Suma ba yadda suka iya indai suka nema suka rasa ne suke zuwa rokan jummai aman da suna da yadda zasuyi ba zasu zo ko dan bakar maganar da take fada musu

Ke kuma menene jummai ta tambayi badariya tana hura hanci, aa daman innar muce tace wai maganar da kukayi na binku rumfar ku ta bakin kasuwa Nima na dinga kai zobo da kunun aya shine tace nazo naji Karfe nawa zaku tafi saina biku Nima

Jummai ce ta harareta sanan tace "kinga ki fadama hansai wanan maganar bazata yiwu ba , Muma ba wani ciniki muke ba bare mu raba wasu ku siyar da Abunku a unguwa mana dole ne sai kun bini rumfa ta

Wlh bama ciniki ne saidai muyi asarar sa kuma kinga ke bakin kasuwar nan kina ciniki sosai shiyasa dan Allah ki taimaka mana

Jummai ce tace kinga duk munafikin da yazo ya baku labarin ina ciniki toh karya yake Nima watarana raba wa almajirai nake Dan haka idan kunada kudi ku kama naku rumfar wanan shine dan haka kibar mun gida tunda bada uban wani na siya gidan ba tana gama fadan haka ta juya ta shige dakin ta tana mita

Zainabu kuwa sosai taji zafin maganar jummai dan da sunada halin kama rumfa a kasuwa babu abunda zai kawo su wajen jummai dan gwamnati ta Hana kasa kaya a bakin kasuwa saidai ka Kama rumfa sukuma basuda halin kama runfar, yanzu ma jarin wani saurayin ta ne awaisu ya basu shima saida Umman su ta hada da nata kudin da ta roki yan uwanta, tunda sunada fridge tun wani lokaci da taohuwar gwamnatin garin ta raba wa mata masu karamun karfi dan yin sana a shine suka yanke hukuncin siyarda zobo da kunun aya saidai a unguwar basa ciniki dan watarana ma saidai su kyautar ko su shanye abunsu

Shine hansai ta tambayi jummai akan badariya tunda bata zuwa makaranta zata dinga bin ta rumfar tasu tana siyarwa har Allah yasa su samu kudin kama Rumfa kuma jummai da farko ta yarda tace yau suzo su sameta shine yanzu tayi musu wulakanci

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now