📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 0️⃣5️⃣Sauri take tayi a hanya har ta karaso gidan ta saka key Kenan ta bude taga tsayuwar babur din aliyu, nan fa gabanta ya fadi bata taba Tunanin dawowar sa ba a irin wanan lokacin , kalon kalo suka shiga yi wa juna kafin daga bisani ta sosa Kai tace wai har ka dawo , kallonta yayi sanan yayi banza da ita , ya raba ta gefenta ya shige gidan
Tsayawa tayi na dan wani lokaci tana tunanin abun yi , duk abunda take sosai tana Jin tsoran aliyu dan shi mutum ne mai kwarjini sosai gashi saida yayi mata warning Akan fita ko nanda makota ne babu Neman izini, itakam yau dai tasan sai yayi Kwana 2 yana fushi da ita gashi so take ta tambyeshi zuwa unguwa
Haka dai ta tsaya tana ta tunani da taga ta kasa samo mafita ta yi shahada kawai ta shige gidan tana ta zaro ido
A kitchen ta same shi zai fito gaba daya kitchen din ya turnuke da hayaki alamun dai Miya ta kone har ta fara kama tukunyar
Daga Ina kike shukura, ya tambaya murya ba wasa
"Wlh yaya aliyu kaga nadan je gidan Hafsa ne kayi hakuri " ta fada tana kallon kasa dan bazata iya hada ido dashi ba
Aliyu ne ya soma magana cikin fushi
"Ke yanzu abunda kikayi kinyi daidai , kika bar gidan nan ba tambaya sanan kuma sabida Hauka da rahsin tunani kika dora girki kiga tafiyar ki yawo , kinsan dayaya nake samo mana kudin da nake siyan kayan miyan ne sabida rashin tausayı zaki mun hakaA ajiye wanan ma a gefe kısanı wanan gidan ba nawa bane ba aro aka bani na zauna shine zaki nemi ki babaka musu gida toh wlh bazan lamunta ba duk sanda kika Kara barın gidan nan ba tareda da izini na ba wlh saina Saba miki
Sanan kuma punishment Dinki shine bana so ki kara saka kafarki a waje tsohon wata 1 , duk wani üzuri da kike dashi ki ajiye shi ba ke ba fita har nanda wata daya , yana gama fadin hakan ya saka Kai ya fita daga gidan Ransa a bace ..
Nashiga uku ya Zanyi da zuwa gidan ilham ga bikin Rumaisa ma nashiga uku shukra ta fada tana dafe kanta
Bikine zataje na wata yar makarntarsu wace suka yi secondary , shine aka fito da Anko har na kusan dubu 80 itakuma bata da kudin siyan ankon aman ta cika musu baki akan ae ita bata saka kayan 80k sai sama da hakan dan hakan ita nata zata saka shine ma dalılin ta na zuwa gidan hafsa aran kayan hafsar Wanda take bada haya ba tareda sanin mijinta ba , hafsa mijinta mai Hali ne shiyasa yake mata kaya masu tsada da keçe raini dan duk ya faranta mata kuma kar ta gani a wani waje shiyasa yake bakin kokarin sa wajen kyautata mata aman hafsa bata gani take bada kayanta rent tana samun kudi tunda shi ya hanata bussines , abunda yake rufa mata aşırı shine shi din ba mazauni bane ba yana aiki ne a port harcourt sai yafi wata 2 a can shiyasa take abunda taga dama ba tareda sanin sa ba
Kudi ba mastalar hafsa bace ba kawai rahsin godiyar Allah ne yake sawa take wanan sana ar, aman sabida Kar ya gane idan yana gari zata bi duk contact dinta ta fada musu su dakata da zuwa gidan ta ko kiranta neman kaya dan karda asirin ta ya tonu
..............
Shukra ta kara cizan yasta tana Jin zafin hanata fita da aliyu yayi , ta saki tsaki aikin banza kawai ga talauci ga bakin hali Kai dole ma ko bazataje gidan İLhasa ba ta tabbata ta samu hanyar da zata je bikin Rumaisa dan bataso a rainata so take ta nuna musu dagaske tafi karfin saka kayan dubu 80
Wlh saina je nasan idan yayi fushi ya ce ya daina kula ni na dan wani lokaci wanan kuma nasan ta yadda zan shawo kansa magana ta wuce aman bikin nan idan banje ba wlh nasan sai anfi shekara ana yi Dani ace tsoro ne ya hanani zuwa
Tayi murmushi dan harta hango ta a gurin bikin ana kallon ta ..
Dakinta ta shige ta cire mayafin jikinta sanan ta fito ta shiga kitchen din Taja tsaki tana kallon tukunyar ta wace duk tayi Baki ta ajiye a gefe sanan ta dauraye sabon tukunya ta soya manja dan ba Şauran kayan Miya kuma badan batada kudin siyan bane ba aa ita mace ce wace sisin ta baya shiga kudin cefane ta gwamace ta aro kaya dasu da şarka da dan kune akan ta taimaka ko da kuwa da kudin ashana ne komai sai aliyu ya bata
Ta saki tsaki sanan tace wlh saidai acı mai da yaji dan bazan iya ba ...:.:
✍️Mrs abba
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...