Ramin karya 07

70 3 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 0️⃣7️⃣

Jummai dan Allah dan sonki da annabi muhammadu saw ki tausaya mana yarinyar nan ta biki rumfar nan dan Allah hansai ce take fadin wanan kalman kamar zatayi kuka tana rokan jummai da ta taimka ta tafi da badariya rumfar kasuwar dan ta siyar da zobon karda suyi asara aman jummai takı ana haka saiga baban dan jummai  dan Daba da kowa yake tsoro har jummaan kaf unguwar tsoran sa akeyi ana kiran sa da goje, ya mene yake faruwa ya tambaya muryar sa abun tsoro

Jummai cikin tsoro ta kalle shi ta kalli hansai ta fara dana sanin tsayuwa ma sauraransu hansai gashi yanzu tasan goje sai ya ce dole saita je da su kuma ita tsoran sa take bazata iya masa musu ba

Sai yau ma zai wani zo ya kusan wata 2 baya gidan aman shine sai yau yaga damar zuwa ta sake hadiyar yawu ganin goje ya fito da wata karamar sabuwar wuka sai sheki take

Cikin muryar sa ta yan daba ya fara magana

"Ke jummai wai bazaki fadamun abunda yake faruwa bane ba saina dan miki Zane ko yaya"

Aa göje zan fada maka kaga wai dole saina tafi dasu rumfa ta sun siyarda zobo nikuma gskia ba ciniki nake ba ba fada musu aman sun nace ta fada tana hararar hansai

Wai haka hansai goje ya tambayi hansai

Badariya ce tayi karaf tace "eh goje hakane kuma wlh shi kadai ne jarin mu dan Allah a taimaka mana

Goje ne ya gyada Kai yace kin Kira Allah ae magana ta kare , jummai dole fa su biki kuma ba iya yau ba kuma wlh naji labari ance kince sai sun bar rumfar saina kar ki har lahira dan daman ba amfanin komai kike mana ba yar wahala kawai

Jummai na Jin an ambato mutuwa ta fara karkarwa tsoro ya shige ta tasan halin goje Sarai indai yace zaiyi Abu toh fa ba makawa sai ya aikata abun dan haka ba yadda ta iya ta saka mai napep ya saka Kular zobon badariya ta shiga itama ta shiga itada zainabu suka Kama hanya zuwa kasuwar

Hansai tayi ta zuba ma goje godiya

Yace ba komai hansai ni na ware sai kuma kun sake gani na kuma wlh jummai ta sake hanaku kije gün tijjani yanka ki saka ya kirani zan dawo nayi maganin ta

Hansai ce tace insha Allahu ma bazata Hana ba nagode

Ki godewa mai sama ni na yanka , ya saka Kai ya bar wajen yana ma Kansa kirari...

###############################

Shukra na karasa soya manjar ta juye ta fito Tana mita , wayar ta ta dauka ta lalaubo numbern nafisa mai gwal inda take karbar hayar gwal da şarka da dan kune

Bugu daya Nafisa ta dauka tana wani Shan kamshi , Nafisa dan Allah yaushe xaki kawo mun şarka mai kyau da tsada latest aman fa inaso nayi amfani dashi jibi dan Allah

Nafisa cikin magnar ta ta yan duniya tace , kinga shukra ni ba na Baki hayan abun ba sai ayi ta kiranki ki dawo dashi kiki sai kinga dama , kuma kinsan hakan kashe mana kasuwa yake tunda dai Kaya nan na siya kikayi ba dole ne kibi dokar dawowa dashi washe gari

Shukra ce tace dakata Nafisa ba sai kin fada mun magana ba , daga Aron şarka sai ki nemi ki yaba mun magana

Nafisa wanan lokacin kuwa ta kullu dan haka tace ke yar gidan uban waye da ba za fada miki magana ba, idan da kınada kudin ki siya mana , idan fistari banza ne kaza tayi mana , aikin banza shasha sha ke bakida arziki aman kıdinga rayuwar masu arziki sha sha sha kit ta kashe wayar ko sauraron amsar shukra batayi ba

Shukra sololo ta tsaya tana bin wayar da kallo , lallai Nafisa yau ta gama da ita , taja tsaki sanan tace "ba laifin ki bane ba wlh da ace na auri mai arziki ke har ki kısa ki ganni har nazo Aron şarka a gurin ki , Kai banyi wa kaina adalci ba Dana kare a aliyu gashi tun ba aje ko Ina ba na fara Dana sani ta cije yasta tana Jin zafin abunda Nafisa tayi mata ...

Duba agogo tayi taga har an kusa kiran sallah magrib da ta yi sauri ta fada gidan makociyar ta sumayyah dan kwanaki data ganta ta ga wuyanta wani hadaden şarka mai kyau data taba gani a online ana siyarda dashi dubu 45 dan haka tasan ta saka shi ba Wanda za a kalla a gurin bikin dan so yake ma yayi kama da gwal shine Wanda ake Kira da plated gold

Alwala ta dauro sanan ta zauna tana jiran a Kira sallah tayi ta fice gidan summayh dayake gidan sumayyah n gıda biyu  ne tsakani

Ba a jima ba aka Kira Salah sanan ta tashi tayi ko lazımı bata tsaya yi ba ta fita daga gidan ta yi wa kofar gidan  key ta fice warta

Tana zuwa gidan ta kwankwasa mai gadi yazo ya bude mata , ta shigo tana sake yaba gidan kamar bata taba zuwa ba

A ranta tana sake yaba gidan sumayan dan gida ne kato mai kyau an kashe kudi sosai

Tana shigowa sumaya na kan dining tana Çin abinci  ,  ah manya manya shukra ta fada Tana washe baki

Ah shukra keçe yau kika shigo naji ki shiru Kwana 2 , eh wlh Sumy kinga shirye shirye muke na bikin yar uwata wlh kinsan mu dangin dan tata ne shine fa muke ta biki mun shiga busy dayawa

Allah sarki shukra gaskiya dangin dantata ba karamun dangi bane dole ku shiga Hidima da yawa

Kedai Bari shukra ta fada tana murmushi tana kallon plate din abincin da Sumayya take ci

Jollof rice ne da pepper chicken sai coslow tuni ranta ya biya dan rabon da ta saka irin wanan a bakin ta tun a bikin wata kawarta da suka hadu a kasuwa shima tayi mata shishigi har ta gayyace ta bıkın kawance ne ya hada su aman kowa ya tambayeta yadda take da ita saitace musu ae cousins ne da ita da yarinyar a dangin  dan tata

Sumy ta kalle ta tace bismillah fa shukra zo ki saka mana albarka ,

Au toh bara na karaso shukra ta fada ba kunya , zama tayi a kujerar dining din dake kallon sumyah ta na wage Baki

Ga plate nan ki zuba sumaya ta fada tana murmushi dan ita akwai kyauta ba ta da rowa sam

Ae sumayh bata rufe Baki ba shukra ta bude food flask ta fara loda abinci sanan ta bude dayan ma ta zuba naman kaji har yanka 3

Sanda ta saka a bakinta saida ta lumshe ido tsabar dadi ....

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now