Ramin karya 09

61 2 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
Page 0️⃣9️⃣

Jummai kuwa saura kadan ta fashe dan bakin ciki abunda goje ya mata , tunda take bata taba dana sanin haihuwar goje ba sai yau , ta ja tsaki tana kallon hanya dan ji take kamar zuciyarta zata fito saboda bakin ciki

Badariya kuwa tana jinta tayi banza da ita , ita dai burin ta ya cika tunda goje ya taimake su yasaka baki jummai zata barsu su siyarda zobon su

Basu jima ba suka iso rumfar kasuwar , nan yaran da suke sauke ma jummai Kaya su jera mata a rumfar suka nufo motar suna dariya hade da gaishe da jummain data fara sauka daga mashin din

Suna zuwa suka fara shirin sauke kayan daga adaidata sahun nan suka fara da cooler zobon badariya

Ae daya daga cikin yaran mai suna modibo yana daukar cooler ya daura a kansa sai ji yayi jummai ta hankade cooler daga Kansa tana bala i

Nan zobon ya tarwaste a kasa wasu Harsun gangara kwatar dake kusa da wajen

Badariya kuwa kmar ta fasa ihu tace haba jummai me yayi zafi haka zaki barar mun da Kaya haba

Uwar kice tayi zafi jummai ta fada cikin masifa , shegu yan iska mayu , Kai kuma wlh kuna mun garaje saina kore ku Tunda ku bakuda mutunci yan iskan yara kawai ta fada cikeda masifa da zafin rai

Modibo ya shiga bawa jummai hakuri dan kuwa jummai tana musu abun Alheri duk da saita ci musu mutunci take musu wani sa in aman dai tana tare musu rigima a kasuwar dan kuwa kowa tsoran jarabar jummai yake dan ba karamar masifafiya bace ba

Badariya kamar tayi kuka haka ta durkusa ta kwashe kayan ta da jummai ta barar ta kyale na kwatar Allah ya taimake mata ba su fi guda biyar ba ne suka fada a kwatar

Zainabu ce ta nuna musu kulolin jummai da zasu kwashe suka kwashe suka jera a rumfar abunsu

Nan fa aka fara layin siyan abincin jummai waje a cika fal dan kamar ita ake jira

Badariya kuwa gefe ta samu ta zauna cikin rumfar jummai tana tallata zobon nata tayi sa a kuwa masu zuwa siyan abincin jummai suna ganin zobon sai su masto su siya a haka har ta kusa siyarwa tana ta jin dadi

Can rana bayan an tashi su hüda Kai tsaye rumfar jummai ta taho tana tafiya a hankali tsabar yunwar da take ji dan naira hamsin din da jummai ta bata biscuit kawai ta siya da püre water dan yau kawar ta Maryam preety  kamar yadda suka saka mata bata zo school ba daman itace yar masu kudi take zuwa da abincin yan Gayu har huda take cika tumbin ta dan huda ba karya akwai kwadayi

Tana zuwa ta tarar da jummai tana kirga alalar da ta rage , ta hade rai tace jummai Ina wuni

Da ban wuni ba zaki gani ne har ki gaisar jummai ta fada cikin fada , Allah ya baki hkuri jummai , hüda ta fada tana kallon ta

Idan Allah ya bani sai ki kwace yar iskar yarinya kawai Karfe nawa yanzu kin gama yawon iskancin ki shine zaki zo mun nan kina wani Ina wuni na munafurci ko

Wlh jummai banje ko Ina ba daga makaranta nan gurin kawai nazo ta fada idonta cike da hawaye

Dallah can Masta mun makaryaciya wai daga makaranta , makarantar karya da yawo ko ta fada tana hararta

Shiru huda tayi tana hawaye dan sosai Çin mutucin da jummai take mata yana kona mata rai sosai

Jummai dan Allah kiyi hakuri ta bata hakuri tana hawaye

Ke kika sani kuma wanan jummai ta fada tana rufe robar alalar

Yunwa nakeji jummai dan Allah a bani abinci

Hmm nasan Kwanan zancen ae , kin gama yawan ki ciki ya zazage shine kike so kizo ni ki cinye mun abinci nazo na rasa jari Nima na shiga maula da roko  maki yana suna mun dariya ana daman haka ake so a gani
ko jummai ta fada tana kallon inda badariya take zaune dan da biyu take maganar

Girgiza Kai huda tayi sanan tace aa jummai wlh ba haka nake nufi ba dan Allah kin sanmun ko kadan ne

Bazan iya ba jummai ta fada tana mikewa tsaye

Dan Allah jummai kiyi hakuri ko bashi ne kibani idan nasamu kudi zan ,baki

Jummai ce ta kalli hüda sanan tace bashi har na nawa zan baki bashin

Shinkafa da wake na Dari uku sai a saka mun alala daya dan Allah

Shikenan jeki wajen zainabu ta saka mki aman wlh bashi na bayar ban bayar kyauta ba ehe

Naji bashi ne hüda ta fada tana barın wajen ta nufi gurin zainabu tana fada mata abunda zata bata

Zainabu batayi mamakin ganin hüda na siyan abinci ba dan tasan halin jummai wanan kadan ne daga aikin ta

Badariya ce tayi mamakin abun sosai dan dai hansai ta taba bata labarin har sunar hüda sunje lokacin da jummai ta haifi hüda aman da cewa zatayi hüda ba yar jummai bace duba da abunda ya faru akan idon ta ....

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now