Ramin karya 20

25 0 0
                                    

📒📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha

WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣0️⃣

    Ko da aka gama break aji suka koma dan cigaba da daukar darasi har aka tashi bayan sun fito daga aji preety ta ce zee yanzu tunda kince zaki bini party dinan dole ne muje gidanku ki Chanza kaya tunda dai bakızo da wasu ba

   Zee tace eh hakane muje ko sanan ta kalli hüda wace ce komai ba kuma tana Jin su
Ke kuma yane kin Chanza ra ayi kokuwa har yanzu kina kan bakan ki

Huda ce ta tabe Baki sanan tace kuyi tâfiyar ku nikam gida zanje

Shikenan yar kauye kawai zee ta fada tana jan hannun preety

Huda ce tace aman dan Allah pretty ku rage mun hanya tunda ta kasuwa zaku bi ku ajiye ni a rumfar jummai

Toh taho muje preety ta fada sanan suka fito kofar makaranta har inda driver din pretty yayi parking sanan suka shiga

Gaishe shi zee da huda sukayi ya ansa cikin sakin fuska sanan preety ta fada masa inda zai ajiye huda su kuma tace ya wuce dasu gidan su zee dake yasan gidan ya ansa da toh dan yasan pretty bata barın sa haka duk sanda zata ce yakaita wani gurin ba gida ba toh zata cika masa aljihun sa ya manta da amanar da mahaifinta ya basa akan ya kula masa da yar sa shiyasa preety ta dade bata da driver baban ta yake kaita makaranta ya dauko ta yanzu kuma tafiya ce ta kamasa zuwa wani course a uk shiyasa ya nemo mata driver dan Bayada ya iya Akan idan tagama sai tazo ta same shi uk din tunda zai Kai kusan 5 years a can din itama saiya nema mata gurbin karatu açan din

Shida amaryar sa yatafi ya bar wa mahaifiyarsa preety dan Allah yayi wa mahaifiyar pretty rasuwa tun tana yar shekara 3 kuma ita kadai ce a gurin iyayenta har yanzu amaryar sa bata taba samun haihuwa ba

Preety ta taso cikin gata aman haka bai hana mahaifinta kula da rayuwarta ba baya barın ta fita ko kofar gida sai makaranta dan karda ta hadu da abokan baza saidai hakan da yayi kamar yayi tuya ne ya manta da albasa sabida wayar da ya bata babba ce wace bai kamata ma ace tana rike ta ba dan haka tanada acces da social media anan ta fara hadu wa da kawaye idonta ya fara budewa har suka fara gayyatar ta party haka da samari suke shiryawa

Suke hüre mata kunne akan kudin baban ta ba kudin ta bane ba dan haka ta tashi ta nemi nata kudin shiyasa duk wani party da big boys din adamawa za su hada sai anyi inviting yan kungiyar su preety anan ne kawayen ta suka saka mata suna pretty

Yanzu preety tarin samari ne da ita kala kala aman ta fi kula wani saurayi mai suna Samir shine ma ya bata sabuwar iPhone din da ta nuna wa su zee dazu

Idan aka tashi a makaranta take zuwa yawon ta , sai ta koma gida abunta idan kuma party din na dare ne pillow take saka wa a gadon ta ta rufe da abun rufa dan a dauka itace ke bacci sanan tayi ma driver waya yazo ya dauke ta ta hada Baki da mai gadi shima dan kudi take basu Wanda take rufe bakin su basa sanar da hajiya fulani wato kakar preety ...

   A cikin motar ma zee da Preety ne kawai suke hirar su hüda bata saka musu baki ba har suka karaso bakin rumfar jummai

Hüda tace yauwa nan yayi nagode fa ta dauki jakar ta fito daga motar tana daga musu hannu suma suka daga mata hannu sanan suka tafi

  Akan idon jummai kuwa  huda ta sauka daga mota kasancewar baya glass a rufe yake kuma tint ne bata gansu zee ba sai driver dake gaba ya zuge nashi glass din

  Jummai ta tsaya tana kallon hüda tana murmushi har ta karaso , Ina wuni jummai huda ta fada Tana kallon jummai ganin yau jummai ce take murmushi abun da abun mamaki kuma da alama ma da ita take toh yau me tayi da ta tantanci murmushi daga wajen jummai

Iyye yarinya kokefa wlh haka nakeso a dinga sauke ki daga mota masu kyau abun ki jummai ta fada Tana Washe Baki , yanzu dai nawa ya baki fito dashi nasan da yawa ke wanan ma zai iya Baki dala wlh kalli fa motar har sheki take Kai yarinyar nan wlh nasan daman zaki zame mun arziki tunda na haife ki

Huda ce ta risinar da Kai wato Kenan jummai ta dauka saurayi ne ya sauke ta shiyasa take mata wanan dariyar tab wanan wace irin uwa ce duk zaton ta idan taganta a motar zata mata fada sosai duk wata uwa mai hankali idan taga yar ta namiji ya ajiye ta saita tuhume ta aman ita jummai ba wanan bane damuwar ta kenan ita dadi take ji ma har tana tambayar ta nawa aka bata

Ke kinmun shiru huda taji muryar jummai na mata magana

Shiru hüda ta kuma yi bata amsa ba, jummai tace zo nan jeki zuba abinci kici ki koshi saiki kawo kudin naga alama kamar yunwa kike ji shiyasa maza maza wuce ki zuba ki zuba wanda zai ishe ki fa ..

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now