Ramin karya 22

47 2 0
                                    

📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha

WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣2️⃣

Kasa da kanta shukura tayi saurin yi cike da kunya dan bata taba zaton zasu hadu da salma touch ba , bakin rashin kunya ya mutu ne naji shiru sumaya ta fada tana dariya

Shukura ce ta hadiye wani yawu Mai daci sanan ta Kalli salma touch wace ta tsaya tana jefa ma shukura mugun kallo

Dan Allah Kiyi hakuri network ne wlh aman kinsan ni bazan gudu da kudin ki ba ko shukura ta fada tana hararar sumaya dake rike da kugunta tana kalon shukura

Salma touch ta yi shewa sanan tace ni Zaki fadama Haka Bayan kinyi blocking dina zaki wani ce ba gudu zakiyi da kudi na ba

Shukura shiru tayi dan tana barin Shagon a jiya ta danna mata blocking shiyasa koda salma tana kira bai shiga ba

Sumaya ce tace Allah Salma karki kyale yarinyar nan itace fa nake Baki labari yanzu tazo aron sarka ta da zuwan zataje kasuwa irinsa taje ta saka mun sarka a biki

Salma ae nima itace wace nake baki labari tazo shago tayi mun transfer din karya saida kudin kowa ya shigo Aman banga na wanan matar ba kuma nakira ashe tayi blocking dina sabida ita yar damfara ce

Sumaya ce tace ae wlh karki barta makaryaciya kawai ta fada tana kallon shukura

Salma ce ta Mike tsaye tana cewa ae tunda dai naganta ae dole a fito mun da kudina ta rike gyalen shukura tana mata kallon raini

Shukura ce tace baiwar Allah menene haka akan dubu 15 kike rike ni kamar wace ta miki sata

Karaf sumaya ta ce da abunda kikayi da sata mene bambancinsu shukura iyye yar rainin wayo kawai

Salma ce tace kinga sumaya wai ina ne gidansu ne naje nayi tijara tunda naga abun zaizo da raini

Ah gidansu ko gidan mijinta ae wanan da kike gani da ji matar aure ce ga gidanta can gida biyu ne ya raba mu

Salma ce ta saki shukura sanan ta tafa hanayenta ta rike habbar ta ta kalli sumaya cike da mamaki tace yanzu wanan da aurenta aman take wanan halin sanan ta juya kan shukura tace kekuwa baiwar Allah mene yakai ki aikata irin wanan abubuwan

Gasa mana da rashin godiyar Allah da hada kanta da mu mu manyan mata masu auren manyan mutane sumaya ta bawa salma amsa cikin gadara dan tabawa shukura haushi

Ae kuwa shukura ta shakka aman kamata da akayi ne ya Hana ta maida martani saidai zuciyarta dake suya

Salma ce tace kawata kina nufin masatyinta baikai bane ba

Fadi ki Kara kawata faci mijinta yake aman ita tace dangin dantata ne mudai bamu gani ba a jiki sumaya ta fada cike da izgili

Salma dariya tayi sanan tace kice ordinary matar Mai faci ce take fake life Kai wayoo ni salamatu

Kinga kawata kuje ta baki kudin ki ehe idan kin dawo na karasa warware miki zare da abawa

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now