Ramin karya 23

49 1 0
                                    

📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha

WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣3️⃣

Hüda haka ta karasa shagon alhaji garzali tana ta Mita cikin ranta , ko da ta karasa bata tarar da shi ba cewa sukayi yana can çıkın office din sa dake yanada wani daki a cikin shagon Wanda yake cin abinci da kuma wasu abubuwan ba Wanda kuma yake shiga sai shi ko idan ya aiki wani ya shigar masa

Yana yawan kiran yan mata mussaman masu siyarda abinci zuwa dakin ta a zumar su kawo masa abinci dan ya lasta wasu , wasu su yarda da shi wasu kuma suki yarda idan waenda suka yarda haka zai dinga basu kudi kmar ba San Zafin Neman su ba saidai ganin hüda ya kwadaitu da ita sosai saidai bai Taba samun fuskar tunkarar ta da wanan zancen ba saboda bai samu fuska ba wajen hüda dan yasan halin jummai ita ba masatala bace ba indai zai bata kudi ya rufe bakin ta

Aman yau ganin wanan damar da ya samu har hüda zata kawo masa abinci toh zai amfani da daman sa wajen baygana ma hüda abunda yake ransa bazai wasa da damar sa ba

Daya daga cikin ma aikatan nasa ne suka Kira shi a waya dan su sanar da shi zuwan hudar dan doka ce indai Ana Neman sa saidai a kirashi a waya ba Wanda ya İsa ya shigo masa office Kai tsaye

Kiran wayar da aka yi masa ne ya saka ya dakata da lalubar yarınyar Mai fura da Nono da ta kawo masa fura dayake yi ya dauki Wayar yana tsaki ya kara a kunne

Hello alhaji daman ankawo maka abicin kane yaron shagon mai suna iliyasu ya fada

Au au abincin wajen jummai kenan cema yarinyar ta kawo ya fada yana washe baki

Toh iliyasu ya amsa sanan ya kashe wayar yana mamakin alhajin dan a iya yau yakawo yan mata yan talla sunkai 4 yanzu ga wata nan

Yana ciki alhajin aman yarinya dan Allah naganki Mai hankali dan Allah ki rike mutuncin ki kinji illiyasu ya fada ma hüda cikin murya kasa kasa

Hüda bata gane abunda yasaka ya fada mata haka ba dan haka ta gyada kai sanan tace da ka karba ma ka karbo mun kudin kawai

Girgiza Kai iliyasu yayi sanan yace aa alhaji bai sani wanan aikin ba kidai shiga kinga office din ya nuna mata dakin da yastan sa

Gyada Kai hüda tayi sanan ta yi wajen dakin da ya nuna mata , dayan Yaron shagon Mai şuna Ahmad yace Kai illiyasu yanzu yar gidan jummai kake ma wani wa azi wai ta kare mutuncinta aman dai kaima wawa ne sai kace baka san wace uwar ta ba

Illiyasu ne yace Ahmad kenan ae laifin wani baya taba shafar wani , daga gani wanan yarinyar tanada hankali dan haka kasancewar ta yar jummai bawai yana nufin zatayi hali irin na jummai ba dan haka ka daina fadin irin wanan maganganun

Shienan sheik iliyasu ahamad ya fada yana dariya , dariya shima iliyasu yayi ba tareda ya ce komai ba

Hüda na İsa daidai kofar  karima mai fura ta fito tana Çin magani dan sunyi da alhaji garzali zai bata dubu biyar aman zuwan hüda ya saka ya bata dubu uku wai bai samu abunda yake so ba dan haka saidai ta karbi dubu uku

Itakuma cikin fushi ta karbi kudin ta fito , dan haka suna haduwa da huda ta bangaje ta dan saura kadan ma hüda ta fadi da ita da abincin dake hanaunta Allah ya saka kawai murfin kwanon ya fadi

Tsaki karima tayi sanan ta yi gaba abunta dan ta ji ciwon abunda alhaji garzali yayi mata Akan hüda kawai dan bayada zatayi ne ta hakura dan bata so su bata da alhaji garxali dan dashine take samun kudi takeso ta tara ta siya kayan daki na keçe raini dan bata so ayi mata dariya a gari

Tun da bataso aman haka mahaifiyarta ta takura mata dole ta amin ce da alhaji garzali dan kawai ta samu ta tara kudin kayan daki dan ta burge kishiyoyin mahaifiyar Ta tunda mahaifinta matansa hudu harda mahaifiyar karimar

Kwankwasa kofar hüda tayi cikin fargaba daga ciki taji muryar alhaji garzali ya amsa yace ta shigo

Tura kofar tayi sanan ta shiga tana kale kale, Ina wuni ta gaishe shi tana Mika masa abi Çin dake hannunta

Ga abincin hüda ta fada Tana tana kallon kasa , toh toh hüda alhaji garzali ya fada yana washe baki sanan ya mika ya karbi kwanon abincin

Kallon ta yayi cikin kallon sa ta yan duniya sanan yace yan mata ki zauna mana nagama ci ko kuma ki saka hannu muci ko

Girgiza Kai hüda tayi sanan tace aa nakoshi sanan dan Allah kayi hakuri baxan iya jira kagama ci ba kawai ka aiko da kwanon kawai kudin zaka bani na tafi

Gyada Kai alhaji garzali yayi sanan yace hmm hüda kenan shikenan bara na baki kudin ko

Nan ya janyo wata jaka ya kirga naira dubu 10 sanan ya mika ma huda yana mata wani irin kallo da yake saka gabanta faduwa

Hannu ta mika zata karba nan kuwa ya janyo ta ta fada jikinsa ihu ta saki shikuwa cikin zafin nama ya rufe mata bakin ta da hanayen sa

Mene haka daga abun alkhairi alhaji garzali ya fada cikin gigicewa dan ba yarinyar da yataba kawowa tayi masa wanan ihun kamar hüda dukda yana mata kallon wayayiya tunda tana zuwa school baiyi xaton zai sha wahala ba dan haka dole ya chanza takun sa inadai yana son ya samu abunda yake so

Hüda ce ta tataro duk karfinta ta ture alhaji garzali sanan ta tashi da şauri tana wurga masa mugun kallo

Alhaji garzali ne yayi kalar tausayi sanan yace dan Allah hüda kiyi hakuri wlh shairin shaidan ne dan Allah ki yafe ni

Kallon sa tayi sanan tace haba alhaji da girman ka zaka dinga yin haka nifa yar cikin ka ce haba mana

Rausayar dakai alhaji garzali yayi sanan yace kiyi Hakuri hüda dan Allah ki yafe mun ni idan kika bani dama ma auren ki zanyi kuma komai zanyi miki wlh

Kallon bakada hanakali hüda tayi masa sanaan tace nidai alhaji kabani kudin jummai kawai nayi tafiya ta nasan yanzu tana can tana jirana karta mun fada

Naji hüda zan baki aman dan Allah kiyi tunani gamida aurena insha Allah zan rike ki anana

Naji zanyi shawara hüda ta fada a kage dan Allah Allah take tabar office din alhaji garzali

Sake karo dubu 10 yayi a cikin yar jakar nan ya zama dubu 20 sanan ya mika ma hüda bayan ya kafe ta da wasu idanuwansa yan kana na

Sunkuyar dakai ta karba hannunta na karkarwa dan gani take abunda yayi mata dazu zai sake maimaitawa

Saidai har ta karba hakan bai faru ba dan haka ta saki ajiyar zuciya sanan ta juya kudin tace alhaji wa xan bawa duka wanna kudin

Murmushi yayi sanan ya shafa gemun sa Wanda kazanta ma ta saka ya koma kore kore dan ba gyara shi yakeyi ba

Naki ne kawai kudin abincin jummai zaki Cire ki bata sauran duka naki ne ya fada yana washe baki

Hüda zaro ido tayi sanan tace yanzu duka wanan nawa ne alhaji

Eh aman wanan ae kadan ne a abunda ni alhaji garzali zanyi miki ke ae ta daban ce dan haka karki ma saka wani a ranki duk wani abunda kike so zanyi miki shi kedai kawai ki tambayeni

Nagode alhaji hüda ta shiga zuba godiya sanan ta fito daha office din bayan sunyi salama akan zai zo göbe makarantar su ya sameta ....

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now