RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book
WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 3️⃣7️⃣An fara registration din jamb Aman Huda naji nagani ba yadda zatayi ta biya haka ta hakura take bin Jummai rumfar kasuwa Aman har kasan ranta tanason zanna jarabawar dan samun shiga jami a saidai duk rokan datayi ma jummai tace ita bazata bayar ba idan Zata bawa samarin da suke neman ta dama ta basu dan su bata kudin da zata biya Aman dai ita baxata bata ko sisi ba , haka dai huda ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido kullum addu ar ta allah ya bata daman zana jarabawar
Yau bata jin dadin jikinta dan haka ta zauna a gida bata bi jummai kasuwa ba duk da saida jummai ta gama mata tijara sanan ta kyaleta ta zauna , hawaye ta gama yi tana tuna irin abubuwan da jummai take mata kamar ba yar cikinta ba , a haka taji an banko gidan ana Magana a tsakar gidan wai ina mutanen gidan ne taji muryar goje yana magana , goge hawayen tayi sanan ta fito tana farin ciki da zuwan gojen dan dukda shidin bamai nustuwa bane ba yana iya kacin kokarin sa yaga ya saka ta cikin farin ciki Indai. Zaizo gidan
Ahh goje yau kaine a gidan Aman wlh naji dadi huda ta fada tana murmushi, eh nine wlh huda Yau nan Allah ya wurgo ni huda ya naganki a gida Yau ba kasuwar ne ina ita yar rainin da hankalin nan jummai take ko wa
Kallonsa huda tayi tace Kai goje jummai fa mahaifiyarka ce baikamat kace haka ba , ke ni kyaleni da wanna maganar ae batayi mana gatan da iyaye sukema yaransu ba dan haka komai zan kirata babu ruwanki
Naji huda ta fada tana kallon goje, jummai ta tafi kasuwa nikuma banajin dadi shiyasa ban bita ba kasan na gama makarnata yanzu jamb dai naskeso na zana na samu na shiga jami a
Hakan yayi daidai dukda ni banma san mene jab din da kike cewa ba goje ya fada yana sosa kansa
Dariya huda tayi sanan tace Kai goje jamb akecewa ba jab ba , oho muku ku yan bokan nan komai mutum ya fada saikuce ba haka ba
Dariya huda ta sakeyi ba tareda tace komai ba , goje ne yace yanzu dai anyi jab din be ko jambi ne oho dai kunyi ko bakuyi ba
Ba ayi ba goje aman an kusa yanzu dai anata biyan kudin ne , ah toh kice jummai ta biya miki kenan goje ya fada yana kallon huda
Girgiza kai huda tayi sanan tace jummai taki biya goje bansan yadda zanyi ba
Hmm jummai ae bazata taba sonmu ba Kai Allah wadarai da irin uwa kamar jummai
Haba goje kadaina fadin haka mana huda ta fada tana kallonsa , meyasa bazan fadi haka ba huda kaleni kiga yadda na koma duk bakin uwata ne ya janyo min tun ina karami jummai take mun baki da kirana dan iska a kan laifi kankani Zata dakeni ta aibata ni ta tsine mun watarana ke shaida ce tace rayuwata bazata yi Albarka ba ta manta da BAKIN UWA karfi ne dashi yanzu kalleni huda ba kwayar da banasha ba harkar da banayi daga daba zuwa sare sare da sata ke kinsan komai ae ya fada yana furzar da iska mai zafi idonsa ya kada yayi jawur
Huda numfasawa tayi sanan tace kayi hakuri goje kadaina fadin haka dan allah , ya wuce fa huda yanzu nawane kudin na baki dan jiya jiyan nan nasamu arziki dan haka ina cikin arziki dumu dumu abunda yasaka ma na kewayo kenan dan na baki wani abun na kara gaba
Dubu 10 ne kawai kudin goje, goje ne ya saka Hannu cikin aljihun sa ya zaro yan dubu ya kirga Dubu sha biyu ya Mika mata , ga wanan ki biya maza maxa Yau ba sai gobe ba sauran kuma dubu biyu ki rike nakine nizan yanka sai kuma na kara kewayo wa yana gama fadin haka yayi hanyar waje
Nagode goje huda ta fada dan dan guntun hawayenta, ki godema Allah kawai ya fada sanan ya karasa barin gidan
Huda cike da Murna ta dauko mayafinta ta rufe gidan ta wuce biyan kudin jamb din , wayar zee ne ya shigo Lokacin tana dab da karasawa wajen sai yanzu ma tuna da zancen da sukayi da zee akan wani saurayinta zai dan zo ganin hudar wai zatayi masa rawa zai bata Dubu 20 aman zata bawa zee dubu 5000 daga kudin ita kuma ta rike sauran
Farin ciki gurin zee ba boyuwa dan tasha wahala kafin ya yarda zee din ta a mince zata zo , a gaskiyar maganar ba wani rawa da huda zatayi mutumin kwanciya zai yi da hudar ya bata kudin kuma duk shirin zee ne ita takai masa tallar hudar dan kawai ta saka hudar cikin harkar kamar yadda tayima Kanta alkawari
Zee kinjini shiru ko huda ta fada bayan ta dauki wayar, eh wlh huda zee ta fada tana duba agogon hannunta
Wlh zee nasamu kudin goje dazu yazo yabani kudin dan haka bazan samu zuwa ba nagode dai da taimakon
Zee furzar da iska tayi cike da haushi sanan tace me kike fada haka ne huda bangane ba
Huda ce tace wlh daman kudin jamb ne zai saka ni wanan Abun kuma nasamu dan haka bana bukata zee shine abunda nake nufi kigane mana
Zee ce tace shikenan huda aman banji dadi ba kinsaka mutum yanata jiranki ko miniti Goma kizo mana kiyi abunda zakiyi ki tafi ki samu kudin ki abunki
Aa gaskiya zee bazan iya ba kiyi hakuri tana gama fadin hakan ta kashe wayar tazo inda zata sauka dan haka ta sauka ta salami mai dan sahu yatafi abunsa
Zee kuwa wayarta ce kawai bata fasa ba tsabar takaici da haushi, ta cize yasta ta saki ashar tana kankance idanuwanta
Cikin fushi tace wlh wlh indai ina numfashi sai na saka ki cikin rayuwar dan nima na shiga wlh wanan alkawari ne na daukar wa kaina ni zainab....
Mrs abba
YOU ARE READING
Ramin karya (Hausa novel )completed
Short StoryYi sauri maza maza ki bani kayan nan kinga duk inda Aliyu yake yana kan hanyar sa ta dawo wa , kuma wlh yau ma ban tambaya ba na fito shukra ta fada Tana hada Kayan da ta zo Aro a wajen hafsa, uhm ae dole Nima nayi sauri Hafsa tace sanan ta cigaba "...