🌳🌳 ⚜ 🌳🌳 🌳 🌳
👑👑
🌳🌳
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)0⃣3⃣
Safiya ta gallama harara tareda shigewa cikin daki.
Zama tayi kan kujera Shaheeda na gefanta,
Har yanzu gurin yana miki ciwo Sapna?
Eh amma ba sosai ba kuma na gayama Auntyn mu ta dau mataki.
Allah ya kyauta muje ki canza kayanki kice abinci kutafi islamiya.
Ya Sapna nima zani makalantan kinji mama kice taje dani tana magana tana dukan ciyar Maman tasu.
Toh zataje dake dan Allah haba sai damun mutane kinasan kije makarantan kuma inkinje din kiyata dukan yayan mutane.
Baya taja tajuya tareda zama akasa tana kuka harda hawaye.
Sapna ce ta matsa kusa da ita tareda fa tsugunnawa.
Haba my cwt sis dake zan tafi rabu da mama bazamu bata abun muba.share mata hawayan tayi tareda rungume ta.
Ita kanta mama yaran nata NA burgeta burin ta arayuwata su samu rayuwa me kyau shiyasa koda yaushe take musu addu'a.
Tashi mana Sapna kije ki dauraye jikinki ga kayan makaranta can na dauko miki.
Mikewa tayi tareda rike wannun Shaheeda suka nufi daki.
Sunata wasa da dariya harta gama shiryawaabinci suka zauna sunaci suna bawa juna abaki Har suka gama.
Hajib dinta mama ta sanya mata tareda basu kudin makaranta.
Hannun Shaheeda Sapna ta kama suka fito.
Da kamar ta shiga dakin su safiya tace ta taho su tafi makaranta amma sai tayi tunanin abunda zai biyo baya.
Tafiya kawai sukayi Har suka karasa makaranta.👑👑👑👑👑👑👑
Tana zaune cikin falon ta taji sallama da sauri ta dago da kanta.
Zuby ce kawara ta.
Da sauri ta mike tsaye tareda fadin haba zuby sau nawa kike San nagaya miki bana kaunar kawata ko daya ta dunga zuwamin gida.na ce duk lokacin da kksan ganina ki fadamin dan akan mijina babu abunda bazan iyaba.
Gaskiya salma baki da hankalin. Kenan duk inda fahad din zaije kina tare dashi ko.ki angaya miki namiji ana hanashi San Abu ne.
Da sauri tayi kukan kura ta shaki huyan zuby tana fadin karya kike fahad bazai taba San wata mace a duniya ba bayan ni.
Da ker ta kwaci huyanta daga hannun salma tareda komawa gafe tana tari.
Karya kike mahaukaciya kuma insha Allah sai fahad yayi miki kishiya.
Ke ni kike gayawa wannan maganar.
Nan suka hau fada doke doke fada sosai.
Fahad dake kwance cikin daki yaji karar hayaniya.
Da sauri ya fito falon ganin kome ke faruwa.
Aa aa salma menene haka kukeyi.
Sai lokacin salma ta saki zuby.
Nan ita kuma zuby ta fashe da wani saban kuka na kissa.
Kinga ni ko salma zaki kashe musu yarinya ko,ba gurinki tazo bane.
Kallan shi take tanata faman huci tareda fadin.fahad ka koma ciki dan Allah zan bata hakuri ta tafi.
Tsaki yayi tareda yin gurin zuby yaga me takema kuka.
Janyoshi tayi tareda fadin ina ruwanka da ita kuma gaskiya fahad ka bari.
Zaki bani guri kokuwa.
Wallahi kome zakayi saide kayi amma bazaka gurin taba.
Kanta yayi Har zuwa daki tareda kulle ta yasama kofar key.
Kamar zata yi hauka tahau buga kofar cikin haushi tana kwalama Fahad din kira.
Amma yayi banza da ita tareda barin wajan.
Dan kwalin kanta ta cire tare da wargar dashi ta kama yawo acikin dakin tana hargitsa gashin kanta kamar mahaukaciya.
Duk da sanyin Ac amma ita gumi take saboda bala'in kishinta.
Shikuwa wajan zuby ya karasa tareda fadin lafiya da ko pls kiyi hakuri Wallahi narasa abunda ke damun ta kiyi hakuri pls.
Babu komai fahad Amma ya kamata ka gaya mata ta rage abunda takeyi dan wata rana zai kaita ga halaka.
Sannan ta mike tareda daukar Vail da bag dinta tabar gidan.
Zama yayi agurin tare da kama kanshi tabbas salma batada hankali yakamata yadau mataki akanta dan wata rana zata jamasa abunda yafi karfinsa.
Mikewa yayi tareda zuwa ya budeta.
Da sauri ta mike tareda biyo shi jikinta duk tayi ja.
Dakata Fahad me ka gaya mata.
Bai kula taba yaci gaba da tafiya.
Magana fa nakema Fahad ka shareni .
Kinyima yarinya duka ta kasa tafiya shiyasa na dauketa na kaita motarta.
Jiki tayanke ta fadi.
Juyowa yayi ya ganta asume.
Jikinsa na bari ya dauketa ya maida ta kan kujera tareda debo ruwa ya watsa mata.
Ahankali ta bude idanunta suka hada ido dashi.
Sabn kuka ta fashe dashi.
Da gaske ka dauki zuby Fahad.
Dariya taso bashi amma ya dake.
Menene danna dauketa bake kika jaba.
Amma meyasa kake min irin wannan pls habibee.
Am sowie bby ke kikaja banasan irin wannan kishin naki kirage zai iya illataki.
Rungume shi tashi tareda fadin insha Allah ka tayani da addu'a pls bby.
Kara matseta yayi ajikinsa anamiki koda yaushe.
Rufe idonta tayi tanajin irin son da takema Fahad din dan akanshi zata iya kashe mutun kuma ta kashe kanta.🙄👑👑👑👑👑👑👑
Bayan sunje makaranta an taso ne suna cikin tafiya wata yr makarantar su ta biyo mayanta rike da kanwarta.
Ke Sapna tsaya Wallahi ki yima wannan kawar taki magana kalli yanda ta fasama kanwata hannu saboda cizan da tayi mata.
Kallan Shaheeda tayi da alamar tuhuma.
Ya Sapna itafa ta fara tsokana ta kuma ta cijeni nima.
Dan Allah kiyi hakuri bazan karama zuwa da ita makarntar ba.
Sannan ta dafawa yarinyar da aka ciza kanta tareda fadin yakuri kinji kanwata zan rama miki.
Sannan suka tafi itama hanyar gida suka nufa tana fadin zaki gane ban kara zuwa dake tunda kika ciji yr mutane.
Ya Sapna Wallahi nima duk wanda ya doceni saina lama.
Chof! Uwar tsokana kawai.
Da sallama suka shigo gidan kasan cewar haka mamansu ta koya musu babu kowa atsakar gidan dan haka dakinsuka shiga tareda cire hijab dinsu.
Mamansu suka shiga kira amma shiru basu jiyaba Har bandaki suka duba nan Shaheeda ta kama kuka mama ta tafi unguwa ta barmu ya Sapna.
Ya kuri kinji bata tafiba rungume ta tayi dan itama bataji dadin rashin ganin Maman tasu gashi tana tsoran wanda zata tambaya.
Zani ta dauko ta goya Shaheeda data fara jin bacci dan anjima da kiran magriba.
Dakinsu safiya ta nufa da sallama amma bakowa a falon.
Saboda tsoro kasa shiga falon tayi daganan bakin kofar ta tsaya tana jirana fitowar wani.
Ummace ta fito daga dakin ganin Sapna tsaye da goyo tace lafiya zakixo ki tsayawa mutanen anan wajan.
Idonta na hawaye murya na rawa tace dama ma.....m..mam mu nake nema.
Dallacan fita kiba mutane waje.
Jiki asanyaye tana goge hawayan nata tafito waje.
Sapna kukanme kike Hafsat ta fada tana kokarin shiga dakin.
Dama mamanmu nake nema.
Haba Sapna sai kace baki da waye.to mamanku tana asibiti zata Haifa muku dan baby.dazu Anty Naja ta dauketa suka nufi asibitin kibar kuka muje ki zauna.
Ba musu suka koma cikin dakin.
Umma dake zaune kan kujera tana ganin sun kuma dawowa tace ubanme ya kuma dawo daku.
Sapna kallon Hafsat take taji me zatace.
Umma gani nayi mamansu bata nan kuma kinga ba ddi abarsu sukadai tunda yarane.
Dallacan ina ruwana abar sun mana.kufita Ku bani waje.
Sapna da Har lokacin kuka take goyeda Shaheeda a bayanta.
Juyawa tayi zata fita Hafsat ta kamu hannunta tareda fadin muje na tayaku kwana.
Dawo nan ba inda zaki tunda naga baki da hankali bakya kishin uwarki.
Umma amma da yaran zanyi kishi.
Dan uwarki inni na haifeki kuma na isa dake ki huce ki shige .
Kukuma munafukai kubarmin daki.
Hafsat kasa matsawa tayi daga gurin.
Tana ganin Sapna ta fita daga dakin tana kuka.
Kamar tayi kukan haka ta Ruga dakin.
Sapna ga tsoro fal cikin rainta ga yunwar da takeji.
Haka ta bude dakin nasu ta shige ahankali ta sauke Shaheeda daga bayanta.
Tashi tayi tareda matsowa jikin sapnar idanta rufe tace mama!
Wani kukane ya kuma kwace mata da sauri ta toshe bakinta takuma rungume yar uwar tata.😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘

YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...