🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)2⃣2⃣
Tana nan zaune Har aka kira la'asr nan ta fara tunanin lafiya kuwa yau habu yakai wannan lokacin bai zoba.
Gurin me gadinsu ta nufa yana zaune shima.
Aa Har yanzu ba'a zo daukar kiba yafada da mamaki tana kallanta.
Eh wallah bansan meya sanyaba.
Toh! Ikon Allah amma baki da numb kowa da za'a kira a sanar musu me daukar taki Har yanzu bai zoba.
Wallahi bani da numb kowa nasan zakayi mamakin ganin budurwa kamarni bata rike numb kowa a gidan suba ta karashe maganar tana murmushi.
Gaskiya kam da mamaki.
Yawwa baba dan Allah 10 zaka bani zansai ruwa ina jin kishi gashi ban fito da kudi ba.
Hannu ya sanya cikin aljihunsa ya dauko mata ya mika mata.
Dan durkusawa tayi ta amsa tare da fadin na gode.
Nan ta nufi wani dan shago,ruwan ta siyo sannan ta koma ta zauna tare sa shanye kayanta.
Duk tayi wani irin abun tausayi yarinyar kyakyawa amma babu gata.
Har kusan 5pm tana zaune tagade abun bana zama bane.
Tashi tayi tare da fadin baba bara na tafi gida sai gobe.
Sallama yayi mata sannan ta tari napep ta shiga.
Nan tamai kotancan inda zai kaita ya fada mata kudin ta shiga.
Nan ya nufi gidan da ita.Suna karasawa ta fito tare da fadin bara na shiga na dauko maka kudin.
Ba damuwa yace da ita.
Da sallama ta shiga gidan.dakin Umma ta shiga da sallamar ta ganin hafsa zaune ya sanyata yin murmushi duk da hafsa bata santa amma ita Har yanzu bazata daina kaunar taba.
Laaah ya hafsa sannu da zuwa.
Ywwa ta fada ba annuri a fuskar tata Sannan tace sai yanzu zaki dawo daga makarantar.
Wallahi habune bai zoba kuma na gaji da zaman jiransa shiyasa na dadi me napep ma na tara nace innazo gida sai abashi kudin.
Ubanwa zai bashi kudin dama kin anje banki agida dole ki dauko me napep Umma ta fada.
Shiru tayi dan dama tasan Umma bazata taba bada kudin nan ba koda zata mutu.
Hafsa ma banza tayi da ita sukaci gaba da hirar su.
Mikewa tayi kamar kazar da kwai ya fashema a ciki.
Part din aunty Rahma ta nufa dan tana tunanin maybe zata iya bata.
Da sallama ta shiga falon tana zaune kan kujera tana kallo.
Aunty sannu da hutawa.
Yawwa ta fada tana murmushi sai kallan ta take kamar mayyah.
Ita kanta tana mamakin irin kallan da Aunty Rahma ke yawan yi mata.
Lafiya Sapna na ganki da uniform yar yanzu baki cire ba.
Eh wallah Aunty habu ne bezoba shine na tari napep kuma gashi bani da kudi sai yanzu na dawo.shine nazo dan Allah ki bani aran 200 wallah zan baki.
Murmushi tayi na yn duniya sannan ta zaro sabowa dau ta mika mata tare da fadin ki rike kyauta sannan yau inasan kizo ki tayani kwana kinsan Abba yayi tafiya.
Toh nagode ta fada tare da mikewa ta fice ranta fal farin ciki Amma tana mamakin yanda Auntyn ta koma haka.
Rana fita ta sameshi yanata faman jiranta.
Hakuri ta fashi sannan ta mika masa kudinsa ta shige gida.
Dan gajiya kam tagaji.
Toilet ta nufa tayi wanka tayi alwala sannan ta fito.sai da tayi shafa sannan ta shirya cikin Riga da skirt na atamfa sunyi mata kyau dan dinki ya zauna ajikinta gata tana da diri me kyau. Nan ta feshe jikinta da turare dan Aunty Naja na karo mata kayan cosmetic ba laifi duk karshan wata da inner wears.Har dinkuna tana musu ita da Shaheeda.tana gama shirinta tsaf ta yi sallah.
Kitchen ta nufa ta dauki abincin ta dan tana samun abincin rana dana dare tunda ba dare ita takeyi.
Zama tayi taci ta koshi sannan ta mike ta koma daki dan ta dan huta kafin kiran sallar magrib.Bayan ta idar da sallah ishsha tana zaune ta tuna da cewar Aunty Rahma tace taje ta tayata kwana.
Mikewa tayi ta sanya hijab dinta ta nufi part din nata.
Lokacin data shiga babu kowa cikin falon dan haka ta zauna saman kujera dan ta jira fitowarta.
Abunka da gajiyayye bata dade da zamaba bacci ya dauketa.
Wani saurayine ya fito daga cikin dakin Rahama na biye dashi abaya.
Ganin Sapna cikin falon tadan tsorata amma da taga bacci take sai taji dan ddi.
Kallan Sapna ya tsaya yi tare da fadin wannan fah?
Ke da Allah muje mayi magana ta gidace ita.
Amma gaskiya tayi amma zamuyi magana daga baya saida safe.
Ta rakashi Har bakin kofa sannan ta dawo cikin falon tana kallan Sapna Har wani lashe lebe take kamar tsohuwar mayyah.
Ta kumayin murmushi ta shige dakinta.😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘
YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...