MARAICHI

1.3K 70 0
                                    

🌳🌳       ⚜       🌳🌳
🌳                             🌳
              👑👑
                🌳
     MARAICHI❣
            NA
Zainab Naseer Sarki
    (Zeenaseer😘)

0⃣5⃣

Kara rungume ta tayi a jikinta tana hawaye, ga wani masifaffan tsoro datake ji.yanxu in Shaheeda ta tashi ya zatayi da ita gata da shegiyar rigima.
    Wata iriyar yunwa take ji.
Ahankali ta kwantar da ita dan karta tashi.
Cikin daki ta nufa ta duba dan basket din da mama ke anje kayan ciye ciye sabo da Shaheeda. Cikin sa'a kuwa yasamu biscuits, chocolate da juice na jarka.
    Biscuit ta dauka da juice guda daya ta cinye.sannan ta shiga toilet tayi alwala dan ta riga ta saba sai tayi sallar ishsha kumin dare,ko tayi bacci sai ta tasheta tayi.
     Saida tayi sallah ta idar.sannan ta kama addu'a Allah ya sauki mamansu lafiya ya basu yar bby.
    Sannan ta mike ta kulle dakin.dawowa tayi ta dauki Shaheeda ta shiga daki da ita ta kwantar.
     Tana ta faman lallabata karta tashi Amma saida ta tashi dan yinwa take ji itama.
Zaune ta mike akan gadon tana murza ido tana kiran sunan Maman nata.
    Sapna dake zaune tana kallan ta tama rasa abinda zatace mata dan inhar tasan Maman batanan akwai bala'i.
    Dabarace ta fado mata ta maza ta dauko mata biscuit da juice ta bude mata tare da fadin Heedah ta maza ki ci ki shanye mama tana toilet inta fito bazata baki ba.
     Idanta arufe ta jingina da jikin Sapna, tana samata abaki tana bata juice din tana sha harta shanye.
     Sannan tayi shiru ajikin Sapna tana fadin mama!!!
    Itade Sapna sai shafa mata baya take ahankali yanda bazata tashiba.
Har taji ta dena abbatar sunan Maman tata.
    Anjiyar zuciya tayi tareda kwantar da ita,ta rungume ta tayi musu addu'a tareda rufesu da bargo.
    Tabbas tana tunanin bazata iya bacciba dan bata saba kwana su kadai ba.
     Hawaye ne ya rinka rubo mata ta gefan ido mayesa mama bata tafi dasu ba gaskiya tsoro takeji.
     Mikewa tayi ta dauki Shaheeda ta kuma goyata sannan ta fito daga cikin dakin ta kuma komawa dakin Umma.
    Wannan karan bata shigaba saita tsaya abakin kofa tana kuka kasa kasa.
      Babu kowa cikin falon dan Umma ta jima dayin bacci.
     Hafsat ce take waya,kara jin kuka yasan yata lekowa.
    Sapna ta gani tsaye ta hada kanta da bangon dakin tana kuka.
    Ahankali ta karaso wajansu kamar tayi musu kuka tace!
   Sapna bazaku iya kwana Ku kadai ba ko,yanzu gashi dare yayi Dana kaiki gidan Aunty Naja (yayar mamansu).
   Amma kinga shigo mu kwana tare daku afalo tunda Umma bata tashi da asbah saiku koma da kinku kinji.
    Shigowa tayi tana goge idanunta Har sunyi ja.
   Sauko Shaheeda tayi daga bayanta Hafsat ta amsheta tareda kwantar da ita kan kujera sannan ta nunawa Sapna three sitters ta kwanta.
Daki ta shiga ta dauko blanket ta lullubesu.sannan ta janyo katifa tsakiyar falon ta shimfida itama ta lullube.
     Harta kwanta Shaheeda tace ya Hafsat ki maido Shaheeda kusa daki sabo da tana farkawa amma kinga inta farka taji da mutun kusa da ita baxatayi kukan ba.
    Murmushi tayi tareda dau kota ta maido kusa da ita.
     Sannan ta rufesu tareda yin addu'a.
Sai lokacin hankalin sapna ya kwanta amma Har yanzu tana tunanin rashin Maman tasu.

⚜⚜4:00am⚜⚜
    Lokacin Hafsat ta farka dan bacci rabi da rabi tayi dankar Umma ta farka ta koresu cikin dare.
     Tana mikewa lokacin duk basu farkaba.ahankali ta dauki Sapna ta nufi dakinsu ta kwantar da ita kan gado.dan batasan ta farka.sannan ta koma ta dauko Shaheeda ta maidota kusa da ita sannan ta fita daga dakin.
     Tun lokacin da Hafsat ta dauko Sapna ta farka shiru kawai tayi dan batasan damun hafsar.
Matsuwa tayi tareda kuma rungume kanwar tata.

👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Ita kuwa mamansu bayan tafiyar su makaranta ta farajin kanta yana Sara mata hakanne ya sanyata kwanciya tadan huta Amma tun daganan ta fita haiyacinta ta dinga birgima akasa ga ciki ajikinta tamkar mahaukaciya.
     Dan kwalin kanta ta cire tare da fito ahaka.
    Hafsat na tsakar gida tana aiki taga ta fito tayi hanyar waje.
Da sauri ta kaomota tareda fadin lafiya Aunty ko nakudarne bara na kira miki Aunty Naja dan ita tasan bazata fara tunkaraa ummantaba yanzuma tasan wanka take data fito ta fara fada.
     Itade maryam idanta arufe sai wasu irin maganganu take.
    Daker tasamu ta turata cikin daki sannan ta kullo.
Hijab dinta ta sanya sannan ta nufi gidan Aunty Naja.
Da sallama ta shiga gidan da yake yaranta maza guda biyu koma duk basa nan.
     Falon ta shiga hankalinta atashe.
Itama fitowa tayi daga daki danjin sallamar da daketa faman yi.
    Aww! Hafsat ce lafiya na ganki ahaka.
   Wallahi ba lafiya ba ni bansaniba Aunty maryam nakuda take kokuma nide dan Allah kizo kiba yanda take Allah abun tausayi.
     Innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un.
Dama saida akace ta tafi gida ta haihu ita uwar San yaya tace yaranta ga kuma makarantar su.
     Bara na dauko hijab dina muje.
    Daki ta shiga ta sanya hijab dinta ta dau key din motar ta sannan tace da Hafsat muje ko.
      Cikin motar ta suka shiga nan danan suka isa kofar gida.
      Daker ta iya parking dan hankalin ta duk atashe yake.
Cikin gidan suka shiga kai tsaye dakinta suka nufa Hafsat ta bude sannan suka shiga.
Kwance suka ganta akasa duk ta ji ciwo a kanta.
     Hafsat pls kamamin ita mu fita musata amota.
    Da yake Aunty Najar tana da dan jiki.
Nan suka fito da ita Har sunkai bakin kofa.
    Dakata Umma ta fada cak suka tsaya.
Gidan ubanwa zakije dawo nan.
    Tsaki Najar taja tareda  ciccibar Maryam din tayi waje da ita cikin mota tasaka ta.sannan ta shiga side din driver ta fiji motar zuwa cikin asibitin.
      Amma Umma gaskiya ke rage kiyaryar da kikema su Aunty maryam dan bakisan inda rana zata fadi ba.
     Agidan ubanki zata fadi sakaran banza marar kunya.Anya kuwa kina da hankali,
Dande agida na haufeki da asibiti ne cewa zanyi canje akamin.
      Kamar zatayi kuka ta shige daki.
   Aikin banza aikin hofi wayake da asara inta mutu harda za'a rinka rawar jiki akanta.
Tsaki taja ta koma cikin dakinta.

Suna isa asibitin aka huce da ita emergency nan suka shiga duba.
   Bayan mintina kadan likitan ya fito sannan ya samu Naja ya sanar mata ta farka kuka tana dakuda Amma insha Allah nan bada jimawaba zata sauka lafiya.
Allah yasa doctor nagode.
    Nan ta zauna tanata addu'a wayarta ta dauka ta kira gida bauchi ta sanar musu nan suka hau yimata addu'a suma.dan suna tausaya mata.
      
   Bayan mintina goma wata nurse ta fito hannun ta rike da jariri ta karsu tareda fadin kune kuka kawo wata me ciki.
     Jikinta na rawa tana daga kai tace eh mune.
    Mika mata yaranta tayi .
    Da sauri ta amshe shi tana hawaye tana murmushi.yaro kyakyawa fari tas kamar mamanshi.
     Hajiya ammafa saide kiyi hakuri yaron barai yazo.
     Da sauri ta dago kanta tana kallan nurse idanta yayi jajar hawaye na diga kan fuskar bbyn.
Kasa tsayawa tayi taja da baya ta zauna tareda rungume shi a kirjinta tana kuka.
      Tabbas yanzu taga yaran Amma tajisanshi Har cikin ranta kuma taji mutuwar shi.
Kuka sosai takeyi.
     Ita kanta nurse din taji tausayinta.
Hajiya hakuri zakiyi duk mairai mamacine.
    Dagowa tayi da jajayan idanunta ta kalli nurse tareda fadin ita kuma uwar yaran fa.
Ta karashe maganar wani hawayen na dda bin fuskar ta😭...

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHIWhere stories live. Discover now