MARAICHI

1.2K 58 0
                                    

🌳🌳      ⚜         🌳🌳
🌳                             🌳
              👑👑
                🌳
     MARAICHI❣
            NA
Zainab Naseer Sarki
    (Zeenaseer😘)

0⃣9⃣

Bayan yn kwanaki suna zaune cikin kulawar hafsa da dan Asabe burinsu bai huce su faran ta musuba.
    Kullum ita ke basu abinci,wanka da kuma duk sauran abunda suke bukata duk da Umma tana takura musu ko kuma ta rinka yi musu tsawa shiya inde suna gida toh fah suna daki dan basa San ganin Umma.
    Yauma bayan sunyi sallah magrib suna zaune suna kallan MBC3 ita kuma hafsa tana zaune tana gyara wasu kaya da aka kawo daga wajan guga
    Sallamar dan Asabe ce ta sanyasu kallan kofa da gudu Shaheeda ta daneshi ya dagata sama  yana mata wasa.
    Su hafsa ne suka gaidashi suna ma Shaheeda dariya.
   Amsawa yayi tareda zama.
    Yauwa hafsa ya gidan da fatan de babu wata matsala.
   Wallahi yaya babu komai.
   Masha Allah dama haka ake bukata,miko mata Leda yayi tareda fadin in akwai matsala pls ki karani a waya ko kinga suna bukatar wani abu.
    Insha Allah yaya zan fada maka.
   Yawwa toh Shaheeda maza kije abaki abun ddi saida safe dare yana yi.
    Sannan sukayi mai saida safe ya fice daga dakin.
    Ice cream ne da chocolate da yawa ya kawo musu sai tsire.
Nan hafsa ta bude musu sukaci sauran ta maida cikin fridge.
   Yana fita dakin Umma ya shiga bayan sun gaisa shima ya mika mata leda amma ita tsirene da yogourt aciki.
   Yawwa dama inasan magana dakai.
    Ina jinki.
   Dama Abbane zaiyi aure.
   Ahhh alhmdullh dama haka akeso Allah shine sanadiyar ahiriyarsa.
   Banza tayi dashi dan yabata haushi.
   Dama nafisan ya zauna kusa dani sabo da haka inka gyara wancan ban garan saiya zauna aciki tunda kai babbane saika nemi wani gidan ka zauna.
    Shikenan Umma ba damuwa Allah ya sanya alkhair.
   Ameen ta fada tareda mikewa ta shige cikin dakinta.
   Mikewa shima yayi ya fice daga dakin.

👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
   Yau kwanan salma hudu da tafiya hakanne ya sanya Fahad bai kara kirantaba danta huce kwana kin daya bata.
    Yana gama shirinsa tsaf office dinsa yanufa dan yamakara inyaje can ya yi breakfast dinsa.
    Yana shiga motarsa yayi mata key wayar shi ta fara ringing ganin sunan da screen din ke dauke dashi na Wife.
    Yana kallan wayar ya dauke kansa dan baya da bukatar jin muryarsa saboda ta boda ta bata masa rai tsaki yayi tareda Jan motarsa yabar harabar gidan.
Ta kirashi yafi a kirga haka ta turo masa sako amma ko kadan yaki dagawa.
Karshema a silent ya sanya wayar.
    Hankalinta ya gama tashi dan yanzu hankalinta yayo gida.
Amma mom dinta data lura da hakan ta kwantar mata da hankali dan batasan damuwar yar tata.

👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Yau tunda safe hafsa ta gama duk aiyikanta.
Saboda tana da lecture.
Sukuma su Sapna dama sunyi Hutu.
    Saida ta gama shirinta tsaf suma ta shirya su sannan tace da Sapna ta kula da dakin banda barna kuma in an dan jima kadan suje gidan Anty Naja su gaidata.
   Toh sukace sannan ta barsu suna kallo ta fita.
  Dakin Umman ta shiga cikin daki ta sameta dan bata falo.
Tana shiga ta sameta tana fitowa daga toilet.
  Umma ina kwana zan tafi makaranta saina dawo.
   Fita kibani guri munafuka,Wallahi hafsa baki da mutunci albasa batayi halin ruwaba.sai kace bani na haife kiba.gaba daya kin fifita yarancan akan yan uwanki.
    Amma ni Umma taimakone fa nayi kuma suma naga yan uwa nane.
     Dakyau ina magana kina magana ko?
Sannu uwar taimako ga masu bukatar taimako nan da yawa sai wa en nan en iskan zakina biyewa.
    Fita kibani guri sakare kawai.
  Dan Allah Umma kiyi hakuri ni badan nabata miki raiba nayi hakan nan danan ta fara hawaye.
    Ki fice kibani guri nagaya miki fita tabuga mata tsawa.
   Nan danan ta fice jikinta na rawa saboda tsoran Umman.
    Haka ta nufi makarantar gaba daya bata da walwala.

Ya Sapna kitaso muje gidan Anty Naja.
Toh naji dauko takalminki insa miki.
  Daki ta nufa ta dauko takalminta ta sanya,sannan itama ta sanya nata da hijab dinta.
    TV ta kashe sannan ta janyo dakin ta kama hannun Shaheeda suka nufi hanyar fita.
     Ke! Gidan ubanwa zaku Umma ta fada tana tsaye bakin kofar dakinta tana zare musu ido.
   Amm dama gidan Anty Naja zamuje mu gaidata.
    Dawo nan Najar ubanki shegiya uwar gantali toh babu inda zaki huce kije ki dauko kayan wanke wanken kitchen ki wanke.
      Umma ba me aiki take yin wanke wankenba wallah yayimin yawa.
     Turkashi Wallahi baki da kunya,ni zan saki Abu amma kice bazakiya.
Toh Wallahi sai kinyi inkuma baza kiyiba in fito inganki baki yiba.
    Nan dannan kwallah ta ciko acikin idanta.
  Ya sapna taho mutafi kinji.
    Ummace tace toh maras kunya yr tatsitsiya dake amma baki da kunya toh bazu kuba inkuma kin isa huce ki tafi.
    Kamar zatayi koka fuskarta tace nina tafi. Ta nufi hanyar fita.
   Aikuwa Umma tayo kanta zata daketa.
Da sauri Sapna ta rungume ta takareta tareda fadin Umma kiyi hakuri dan Allah karki bugeta kome kikeso zanyi tunda kinga ita yarinya ce.
     Yarinya ce ita amma ai ta'iya rashin kunya.
  Itade sapna bata koma maganaba harde ta huce ta bar gurin.
    Kwallar dake idan tace ta fado da sauri ta goge tareda fadin taso muje muyi wanke wanke saimu tafi gidan Aunty Naja kinji yr kirki.
  Kanta ta gyada tareda fadin itama Umma sai dodo ya cinye ta ko!
  Kai ta gyada mata tareda janta zuwa kitchen din.
    Tana kwaso kwanikan tana kaiwa wajan fanfo tana bawa Shaheeda wasu Har suka gama.
     Omo ta dauko da duk abunda zata bukata tazauna tanayi suna wasa da dariya tana wanke mata tana mata dauraye ta kefe akwando.
     Har suka kusa gamawa.
    Sapna masu wanke wanke Safiya ta fada tana tsaye tana kallanta.
    Dago da kanta itama tayi tareda fadin naam.
   Ke kuma jibeki yr karama dake sai wani jika jikinki kike fito daga nan gurin.
     Kafadarta ta daga alamun Aa.
    Dama ke baki da kunya shegiya karama dake sai shegiyar rashin kunya.
    Baki Shaheeda ta murguda mata tare da mata dakuwa.
   Kutt ni kikema dakuwa nan ta tsallako ta kada mata mari wanda saida ta kifa cikin ruwan wanke wanken.
    Cikin zafin nama itama Sapna ta kefama Safiya mari.
   Nan suka hau bafa Sapna kuwa ta samu safiya tayi mata tsinan duka.
    Umma ce ta fito da gudu daga daki jin kuka da alamun fada yayi yawa.
    Da ker takwaci Safiya a hannun Sapna dan zuciya gareta bata iya fishiba.
    Shegiya mayya zata kashe min yarinya.
   Ubanme tayi miki kika kama dukanta ba yayrki bace.
    Toh itama meyasa zata doki Shaheeda babu abunda tayi mata.
   Da uwarki bazagina tayiba zakice babu abunda tayimin.
    Bade uwataba kinsan wanca kike zagi.
   Lallai Sapna wato agabana kike zagina.zan nuna muku Baku da hankali.
Daki tashiga ta dauko wayar caza.
Nan yahau dukanta kamar Allah ya aikota.
Ihu take tana bata hakuri Amma kamar kara zugata take yima.
  Itama Shaheeda sai faman kuka take ita kuwa Safiya tana bakin kofa sai dariya takeyi.
   Saida Umma duk tayima sapna tabo ajikinta.
    Juyowa tayi ta kalli Shaheeda dake zaune tana faman kuka ta daka mata tsawa.
Yi mana shiru kona zaneki kema.
   Tasowa tayi tanata kukan itama Har ta karaso jikin Sapna ta fada tana kuka.
Da ker tamike daga kwancan da take ta kamata tana share mata hawayan.
   Cikin muryar kuka tace ya Sapna kicewa mama ta dawo mutafi..

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHIWhere stories live. Discover now