MARAICHI

1.1K 47 0
                                    

🌳🌳       ⚜        🌳🌳
🌳                              🌳
               👑👑
                 🌳
       MARAICHI❣
              NA
  Zainab Naseer Sarki
      (Zeenaseer😘)

2⃣6⃣

Tana nan zaune kamar wanda nata dare dan ko motsi bata yi banda hawaye babu abunda ke zuba daga idanta guri daya take kallo amma ba komai take kallo ba gaba daya zuciyar ta shiga cikin rudani.
    
    Tana nan zaune aka fara kiraye kirayan sallar asbah.
   Maza tayi ta mike ta nufi toilet alwala ta dauro Sannan ta shiga yin sallah ba kakkautawa rana neman mafita wajan ubangiji.
    Tana zaune tana addu'a aka tada sallah.
Mikewa itama tayi tareda tada sallar ta.
Bayan ta idar ne ta cigaba da mikawa Allah kukanta.

     Har gari ya fara aske Amma bata dena zubar da hawaye ba tana ta faman addu'a.
  
   Cikin ikon Allah ta fara motsa hannayanta.
   Hakan ya santa Sapna saurin mikewa dan duba halin da Rahman ke ciki.
   
   Ahankali ta mike zaune tareda dafe kanta idanunta a rumtse sabo da zafin da taji yana yimata kan nata.
   
    Da sauri ta matsa wajanta tare da fadin Sannu Aunty.

    Idanunta ta mike tare da saukesu kan Sapna gaba daya.
   Karfinta kuma zaro idan tana kallanta cikin mamaki.
   Zuciyarta ta fara tunanin abunda ya faru daran jiya.
  Ashefa yarinyar nan ce sana diyar ganinan cikin wannan halin zan koya miki hankaline ta fada cikin ranta sannan ta mike tana dafa bango.
    Da sauri ta matso dan taimaka mata.
   Daga mata hannu tayi alamun bata bukata.
   Jikinta a sanyaye taja baya ta tsaya tana kallanta Har ta shige cikin dakinta.
   Wata sassanyar Ajjiyar zuciya ta sauke tare da kuma yima Allah godiya daya sanya bata mace bah.
   
    Ruwa ta dauko da da abun duster dan goge gurin datasan ya bace.
Saida dakin yayi tas sai kanshi freshener yake sannan ta bude dakin tare da fita.
     Da sauri ta nufi part dinsu.dan lokaci ya kuri sosai.
   Ganin Safiya bata cikin dakin ya sanyata kaduwa dan mamaki ta tafi makaranta.
Yanzu kenan meye abunyi dan bata San zaman gidan kwata kwara baya mata ddi.
    Jikinta a Sanyaye ta nufi toilet dan yin wanka.
   Dama ita makeup be dame taba,doguwar Riga ta sanya ta dan shafa farar powder a fuskarta ta gyara gashinta sannan ta dure kanta da dankwali.
    Ji tayi wata kasala ta saukar mata sakamakwan baccin da batayi jiyaba.
   Matsawa tayi kan gadan tare da lumshe idanunta nan dannan bacci ya dauketa.

Tana shiga daki toilet ta nufa tayi wanka sannan ta fito ta janza kaya ta dauki magani tasha dan Ciwan da kanta yake mata.
     Itama gadan ta koma dan hutawa.
    Hmmm! Ni Rahama wata zatayi kokarin kashewa lallai yarinya baki da hankalin zan nunana miki baki da gata a fadin duniyar na. Kuma yanzu kika fara shiga cikin tsanani.
     Da wannan tunanin itama baccin ya dauketa.

Sai kusan karfe biyu Sannan Sapna ta farka daga baccin da take yi.
  Ahankali ta sauka daga kan gadan ganin 2:43pm gashi ko sallah batayiba ga yinwa datake faman ji.
     Toilet ta nufa ta dauro alwala sannan tayi sallah tasan Safiya ta dawo daga makaranta dan ganin yanda ta watsar da kayan ta a kasa dama haka takeyi koda yaushe kwata kwatanta kazamace babu abunda ta iya.
    Sai da ta gyara cikin dakin sannan ta nufi kitchen dan dauko abincin ta dan wata iriyar yinwa da take ji.
      Cikin sa'a kuwa an gama abinci ta dauko kenan ta fito daga kicin din sukaci karo da safiya abinci ya bare a kasa gaba daya.
     Da sauri safiya taja da baya tare da dura wata uwar Ashariya.
    Ita kuwa durkusawa tayi dan kwashe wanda beshafi kasa ba.
      Kafa tasa tare da take abincin tana fadin dan uwarki kin matamin kayana da abinci amma sabo da baki da hankali baza ki ma duba niba saide ki tsaya kina wani kwashe abinci sai kace mayyah.

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
  01 Amal fansclub 💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHIWhere stories live. Discover now