🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)0⃣7⃣
Makaranta ya kaisu sannan ya dawo da Shaheeda gida.
Dakin shi ya nufa yayi wanka sannan ya shirya.
Gidan ya shigo rike da Shaheeda a hannunsa.
A cikin falo ya samu Umma da Hafsat suma sun shirya da alama asibitin zasu bisu.
Yauwa Dan Asabe dama yanzu nake ce da Hafsat tazo taje ta gaya maka inzaka tafi muma muje mu dubata mana.
Ahhh shikenan nan ma aina shirya saimu huce kawai.
Sannan suka fito suka tafi zawa asibitin.Lokacin da suka isa tun a reception suka hadu da Naja gaisawa sukayi da ita.sannan ta amshi Shaheeda a hannun Hafsat.
Ummace tace da ita yame jiki cikin nuna damuwar ta.
Jiki da sauki de za'a ce.
Toh Allah ya kara sauki Wallahi duk da ba shiri muke da yarinyar nan ba amma sai naji duk ba dadi.
Allah Sarki Naja tace,ina su safiya ko sun tafi makaranta?
Wallahi sun tafi ita da Sapna da yake jarabawa ake nace su tafi makaranta insun dawo tunda yau ba islamiyya sai suzo.
Gaskiya Allah ya bada sa'a.
Dan Asabe ne yace ya jikin nata.
Toh da sauki sunma canza mata daki yanzuma suna can za'a dau hoton kan agani.
Toh Allah ya sauwake ni bara naje in en bauchin sunzo ayimin waya mun mayi waya da Maria tace itama insha Allah tana nan tahowa.
Toh Allah ya kawo su lafiya.
Ameen yace sannan ya kalli Umma yace nizan tafi zan aiko atafi da Ku in anjima.
Toh saika dawo Allah bada sa'a abunda bata taba gayamai ba tunda suke.
Ameen sgimade kawai ya fada sannan ya huce.
Shaheeda kuwa tana jikin naja dayake ta Santa sosai kuma tana kaunarta sosai shiyasa koda dan Asabe zai tafi batayi kuka ba.
Bayan mintina 30 da tafiyar dan Asabe aka fito da ita.
Wannan karanma allurar bacci sukayi mata.
Likitan ne ya kirayi Naja zuwa office dinsa.
Nan tacema su Umma tana zuwa sannan ta mike dauke da Shaheeda a hannunta.
Bayan ta shiga ta zauna ne.
Sannan ya dubeta dakyau yace magana ta gaskiya bazamu cuce kuba komu ci muku kudi babu abunda muka gani cikin kwakwalwar tata saide in tatakin za'a Abi agurin haihu ta samu ciwon.dan Wallahi munyi binciken mu iya bin cike Amma babu abunda muka gani.
Innalillahi wa'ina ilaihir raji'un taketa ambata bakinta ta toshe idanunta na hawaye tama kasa cewa komai.
Hakuri zakiya hajiya addu'a zakuyita yimata kuma shawarar dazan baku shine Ku kaita gidan mahaukata kawai insha Allah zasuyi maganin matsallal tata.
Kuka sosai Naja takeyi sabo da abunne ba'a cewa komai.
Itama Shaheeda dake hannun ta kukan ta fara.
Akafada ta sanyata tana hawaye tana lallashinta.
Cikin muryar kuka tace shikenan liki insha Allah zamu kaita Amma ina jiran yn gidan mune su karaso daga bauchi sai asan yanda za'a yi.
Ba damuwa insha Allah,Allah ya kawosu lafiya amma kirki sannan musu ki bari su karaso da Kansu.
Toh! Sannan ta mike ta fito jikinta asan yaye toilet ta shiga sannan ta saba Shaheeda abayanta kukanta tasha dan batasan ta nunawa Umma akwai wata matsala.
Saida tagama ta wanke fuskarta sannan ta fito daga toilet din ta nufi gurin su ta zauna.
Da Sauri Umma tace yamai jikin.
Murmushi ta kakalo tare da fadin jiki da sauki.
Yauwa dama haka akeso Allah ya kara sauki.
Ameen Hafsat ta furta ita da Naja.❣MARYAM❣
Mahaifin ta shararran dan kasuwane kuma dan boko ne.
Matarsa guda daya yaransu hudu maza biyu mata biyu.
Mahaifiyar su da suke kira hajiya macece mai mutunci,kauta dasan addini.
Haka zalika mahaifin su.
Yana dasan taimakon jama'a dakuma kauta shima.
Babban dansa namijine yayi aure yana nan zaune agarin bauchi sunansa Yakubu suna kiransa da yaya.
Sai na biyu shima namijine shima yayi aure harda yara shikuma Jamilu sai kuma Naja'atu dake aure anan kebbi sai kuma autarsu Maryam.
Sun taso cikin gata da tarbiya wajan iyayansu,gashi suna Santa saboda itace auta haka zalika kowa agidan naji da ita kasancewar akwai dan nisa tsakaninta da Naja.
Lokacin da naja tayi haihuwar ta biyune sunzo suna kebbi Ibrahim ya ganta.haka kuma ya kwanta mata.
Kasancewar yace yan da mata Har biyu Babanta yace ta hakura dashi kawai amma ta nuna itade tana San sa.
Haka akasha shagalin biki aka kawota nan kebbi.
Naja taji ddi sosai saboda yar uwar tata ta dawo kusa da ita gashi unguwa daya tsakaninsu ba nisa.
Hakan yayima Maryam ddi sosai kasan cewar gata ga yar uwata duk wani abunda ke damunta ita take gayama.👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Yana kwance kan gadonsa bayan sallah insha'i ta turo dakin nasa sanye da kayan bacci ajikinta.
Zama tayi kusa dashi tare da fadin pls bby katashi inasan muyi magana dakai.
Wata magana kuma salma pls ki zo mukwanta sai gobe mayi maganar ya fada yana matsowa kuwa da ita.
Wani irin sai gobe kuma kasan abunda zan gayama kobme mahinmmancine.
Pls bakida wata magana mai mahimmancin data huce mujinki.
Hakama zakace kabari mana kaji abunda zan fada.
Kan huyanta ya kwanto tareda fadin ina jinki.
Amm dama zamuje bikine nida su mum Zariya 1wk zamuyi.
Dagowa yayi yana kallanta tareda fadin wk kuma salma.
Eh mana toh menene aciki bikin yn uwa nane ko kansu nakibzuwane.
Gaskiya inde wk zakuyi bazakije.
Haba Fahad wata irin magana kakeyine.
Ko mawa yayi ya kwanta tareda juya mata baya.
Maganafa nake maka Fahad ka juyamun baya.
Nagama magana inkin yarda zakiyi 2 days ki dawo na barki Amma wk yayi yawa.
Haba Fahad gaskiya baka yimin adalciba taya zakana hanani shiga cikin in uwana kai hanaka fita nakeyi.
Enough pls salma abunda kike ya fara insana ni nake auranki ko ke kike aurena.
Nagama yanke hukunci in kinga dama kibi inkuma bakiga dama ba ga kofa nan u cn go.
Mikewa tayi tareda fadin dama aiku maza haka kuke kafin Ku auri mutun kuna nunamai so da kauna Amma daya shigo gidanku sai kuna yimai yawo da hankali kuma Wallahi baka isa ka rabani da yn uwa naba.
Alright haka kika fada naji bana sanki kuma bana kaunarki kuma na Riga na baki choice inknga dama ki dauka in kinga dama ki barshi.
Ke in fact babu inda zakije inkuma kika fita karki dawo min nan.
Haka kafa shikenan u will c ta mike tare da janyo mai kofar da karfi ta fice.
Kanshi ya dame dan kullum sai salma ta samai headache amma ya kusa maganinta.
Ko mawa yayi ya kwanta.Itama tana shiga daki kan gado tafada tana kuka meyasa Fahad ya ke mata irin wannan gaba daya ya canza mata kode wata yakeso.
Wani kukan ta kuma fashewa dashi tabbas bazata iya rayuwa babu Fahad ba Amma meyasa baya kaunarta yanxu.
Da wannan tunanin tayi bacci.Koda gari ya waye kin hadamai breakfast tayi yanxu bata zuwa makaranta inda take teaching dan anyi Hutu.
Yana fitowa da safe cikin shirinsa na office dama beyi tunanin zata hada maiba dan haka fita yayi batare da yaneme taba.
Tana tsaye abakin window Har ya fita da motarsa tana kallansa.
Saida ya fice sannan ta dawo falon kitchen ta nufa ta hada abin karinta Amma gaba daya zuciyarta ta kasa nutsuwa dan tana mugun kwanar Fahad ba karya.
Wayarta ta dauko dan turamai sakon bada hakuri.
Bayan tayi sallama sannan ta tura masa kamar haka:
Know I've hurt u
I didn't mean to.
I am sooooooooo sorry.
Please forgive me🙏🏻Sannan ta tura masa.
Yana cikin driving yaji alert alamun an turo masa sako.ahankali ya dauko wayar ya duba ya gani shima murmushi yayi dan shima yana kaunar salma sosai.shima tura mata nasa yayi kamar haka.
Baby ix OK.
Nd am also sorry fr pls.you are d first and only person to touch my hrt wit passionate nd neverending Lov.
I Lov u m wife❣Tana cikin shan tea taji messages dinsa ya shigo dama shi take jira da sauri ta dauka ta bude.bayan ta karanta itama taji ddin hakan sosai dan haka tadau alkawarin cewa inde bai bartaba bazatajeba.
Wayar taketa faman kallo tana murmushi😊👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
[11:08am]
Daidai wannan lokacin yn bauchi suka iso babban asibitin kebbi.
Parking motarsu sukayi Hajiya da yaya ne suka zo sai kuma matar yayan Bilkisu.Dan Baban baya kasar yana Saudiya.
Cikin asibitin suka shigo.
Har lokacin Naja da Hafsat na nan zaune dan da dan Asabe ya turo mota su ummace kawai ta tafi ita Hafsat cewa tayi zata taho hakade ta hakura dande ganin mutane ta yarda Amma bata soba.
Suna shigowa Naja ta hango su da sauri ta taso ta fada jikin Hajiyar tana kuka.
Bilkisu ce itama da abun ya bata tausayi ta fara kwalla tana dafa bayan Najar.
Yayan ne yace ya isa haka Naja'atu yanzu ina Maryam din take ya jikin nata.
Itade Hafsat tana zaune rungume da Shaheeda tana kallansu itama kamar tayi kukan.
Gaba daya suka dunguma dakin da Maryam din take Har Hafsat.
Tun kafin su karasa suka fara jiyo ihu da sauri suka karasa banda naja dataja baya dan gaba daya kafafunta kasa daukarta sukayi nan ta zauna tareda zubawa dakin ido hawaye na zuba😢😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘

YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...