🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer😘)2⃣7⃣
Mikewa tayi tsaye tare da kwada mata mari sannan cikin kuka tace uwarki kike zagi.
Kuma kace mayyah mahaukaciya wanda batasan darajar abinciba.
Kebar ganin ke yaya tace wallah kawai sabo da Umma nake raga miki.mutun marar baki shine dan iskako?
Hannun ta rike da fuskar ta cikin mamaki ta nuna kanta tare da fadin ni kika mara Sapna?
An mareki kuma kinsan ba karfina kikafi bah.
Nan itama takai hannu zata rama suka hau dambe dama Sapna tafi Safiya karfi.
Safiya najin wahala ta dauki murfin tukun ya ta kwalama Sapna a kanta nan ta fasa mata goshi ya fara jini.
Da sauri ta saketa taja da baya tare da dafe gurin ganin jini na zuba tace ni kaka fasama kai.
Kukan kura itama tayi tare da turata ta buga kanta itama da abun sick na kitchen din.
Nan take kanta itama ya fashe.
Jin zafi kuma ga jini na zuba ya sanya ta bude baki ta zunduma uban ihu.
Wanda yasanya Umma da hafsa fitowa daga daki da gudu jin ihun safiya.Kitchen din suka nufo.da sauri suka karasa wajan Safiya dake kwance a kasa jini na zuba a kanta.
Umma ce tace laaah!
Shikenan ta fasa mata kai zata kashe ta.
Hafsa ce ta shaki huyan Sapna cikin daga murya ta fara fadin.
Ubanme ta miki kika fasa mata kai.
Cikin kuka tace ni bakuga yanda ta fasa min kainaba kodanni bani da gata.
Taasssa! Ta kuma kasheta da mari tare da fadin ni kike gayawa wannan maganar shegiya mayyah.
Cikin kuka tace wallah niba mayyah bace akanme zata fasamin kaina,in bani dame ramamin a duniya a lahira Allah zai yimin sakayya.
Yimin shiru munafuka,Umma ta fada tare da taso zuwa wajan da Sapna take tsaye ta hau dukanta tana masifa kamar Allah ya aiko ta.
Da ker ta rabu da ita ta koma gefe tana huci sannan tace bade akan abinci ake fadanba toh wallah sai bayan kwana biyu zakici abinci a gidan nan.
Sannan ta koma ta kama safiya sukabar kitchen din itama hafsar tabi bayanta suna zagin Sapna dake kwance a kasa cikin wani irin mahuyacin hali na rai ko mutuwa.Banda kanta dake jini yanzu harda baki da hanci dan buskarta duk ta kumbura dan ko daga hannunta bata iyawa sabo da jikinta yayi tsami.
Har gefan idanta saida ya kumbura hawaye ne ke zuba ta gefe da gefen idanta.
Tana nan a kwance tana numfashi sama sama sabo da ta daku.
Ahankali tafara motsa yn yatsun hannun ta dana kafarta.
Karfinta dafa hannun a hankali ta mike zaune tana cige lebanta na kasa.
Da ker ta kama window ta mike zaune.
Haka ta fito daga cikin kitchen din tana dafe dafe ahankali harta samu ta fito waje dan bamata gani sosai dishi dishi take ganin garin.
Tana tako kafarta waje ta kuma faduwa kasa.
Ooch! Ta kuma fada tana kwance a kasa kuma fashewa tayi da kuka maras sauti dan ita kadai tasan yanda take ji.{ni kaina tafan tausayi Har kullah na zubar mata😓}Ji tayi baza iya tashiba lokacin.haka ta yini kwance a tsakar gidan nan ba me tausayinta.
Har bayan sallah magrib tana kwance koda suka fito suka ganta babu me karfin imani a cikin au haka suke harkokinsu ko kallanta basamayi.
Saida taga gari ya fara duhu.ta lallaba ahankali. Dan ta shiga cikin daki.
Hafsa ce ta fito zata tafi gida su Umma suka rakota Amma suna ganin yanda take Jan jiki tana kokarin shiga daki haka suka huce ta ko tausayi babu.
Safiya kuwa ji tayi babu ddi dan tabata mugun tausayi Amma itama haka ta huce ta barta anan.
Ahaka taja jiki Har cikin dakin sannan ta kwanta a tsakar dakin tana maida numfashi.
Haka ta daure ta mike ta nufi toilet.
Tana kuka tana gasa jikinta harta fara jin ddi.
Fuskarta duk tayi wani irin dan dukan da tasha.
Saida taji ta gasa ko ina bataji Ciwan sosai sannan ta fito daga toilet din ta sanya Riga da wandanta masu taushi..
Azaunema ta iya yin sallah dan yanda take jinta.
Kofi ta dauka ta nufi toilet ta dauko ruwan zafi sannan ta dauki Lipton ta sanya shiga tasha tea din ta gasa cikinta.
Da ker ta nemo wani paracetamol tasha ko zataji dadin jikinta.
Bayan ta gama sha nan kan abun sallah ta zauna tana tunanin wata badakalar dazata fuskanta wajan Rahama da ya Abba. Shin menene mafita arayuwata kode guduwa zatayi daga gidan.
Toh amma inta gudu ina zataje wata sani kuma wajanwa zata.wannan tambayoyinne zuciyarta ta kasa bata Amsarsu.
Idanta ta rumtse tana sauraran kiran kiran sallar ishsha da akeyi.
Ahankali ta gyara zamanta ta tayar da sallah bayan ta idar saida ta dau lokaci tana kuma kai kukanta ga ubangiji sannan ta kwanta kan abin sallah bacci ya dauketa.
Bata jima da kwanciyaba safiya ta shigo cikin dakin duk sai taji ba ddi ganin yanda Sapna ta koma ta dalilin su.
Tayi fari so sai ta rame gashi kuma duk fuskarta ta kumbura saboda dukan da Umma ta mata.
Dakinta Shiga ta dauko blanket ta rufeta sannan ta kashe mata wutar dakin ta shige itama ta kwanta.😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘

VOUS LISEZ
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...