MARAICHI

1.1K 45 0
                                    

🌳🌳        ⚜       🌳🌳
🌳                              🌳
               👑👑 
                  🌳
       MARAICHI❣
               NA
Zainab Naseer Sarki
     ( Zeenaseer😘)

2⃣8⃣

    Can cikin dare ta farka saboda wata iriyar yinwa da take damunta.
   Ahankali ta mike ta nufi kitchen din dan samun abunda zataci duk da a tsorace take dan tana ganin kamar Umma zata kamata.

    Tana tura kofar ta kunna wutar kitchen tahau bude budan kwanika amma bbu alamun abinci ko dugo.
    Da sauri ta juya gurin wanke wanke tana neme neme.cikin sa'a ta bude wani flask tuwone gaya babu miya.
   Zama tayi tanata ci kamar wanda ta shekara bataci abincinba.saida taji cikinta ya fara tasowa sannan ta mike ta dauki ruwa tasha sannan tayi gyatsa.
   Taji ddin ganin tuwannan sosai duk da gaya ta cishi.

  Daki ta shigo tare da turawa ta kulle.
  Kan abun sallar taga blanket da mamaki ta tsaya tana kallo dan itade tasan bata dau koba amma ya akayi hakan dan tasan ko sanyi zai kasheta Sapna bazata rufeta ba.
   Kafada ta daga tare da fadin maybe ma nina dauko ban saniba.
    Saman kujera ta hau tare da lullube wa nan danan ta koma baccin da tana bukatar hutun.

Saturday [ 6:32am ]🌝
     Lokacin ta farka daga bacci dan ta makara sosai ita da tasaba tashin asbah.
   Toilet ta nufa ta dauro alwala sannan ta tada sallah bayan ta idar tana zaune saman abun sallah tana en addu'o'in ta da tasabayi ko wace safiya.
   Tana idarwa ta shafa sannan ta nade sallayar ta maida ma ajjinta.
   
    Har yanzu fuskar ta bata saceba daga kum burin da tayi ga saman goshinta inda ya fashe shima yayi kullutu.
     Kitchen ta nufa ta hadu katan wanke wanke takai inda akeyi sannan ta gyara kitchen din.
    Ruwan tea ta dura sannan ta fere doya ta Dora.
   Bayan ta juye ruwan tea din sannan ta gyara kayan miya tayi musu yr stew.ta soya doyar da kwan ta anje.
     Tana gamawa ta kuma wajan wanke wanke ta shiga yi Har ta gama.
   Bayan ta gama jere kwanikan a kitchen ta dauki tsintsiya ta share tsakar gidan.
   Duk wani aiki da tasan nata ne tayi ta gama.
  
   Dakin ummane kawai bata bare ta gyara mata ita kuwa hakan ba karamin dadi yayi mata bah.

   Dakinsu ta nufa ta gyara shi duk safiya nata faman bacci dan ko sallah batayi sai lokacin da ta tashi tukun ko karfe nawane.
    Toilet ta wanke sannan tayi wankanta ta shirya tsaf dan tau tana cikin farin ciki shiyasa tayi aikinta da huri.
   Dan duk karshan wata ana kawo Shaheeda ta yini yau kuma gashi assabar kuma za'a kawo ta.
Shiya take kokarin kore duk wata damuwa dake cikin ranta dan batasan yr uwar tata ta gane tana cikin wani hali.

    Sai kusan 10am sannan ta gama duk abunda ya kamata.zuwa tayi ta mike kan kujera tare da kallan saman rufin dakin tana tunanin rayuwa.
   Tana nan kwance batasanma lokacin da Safiya ta tashiba.
   Wanka tayi itama ta tsara kwalliyarta.sannan ta sanya kaya ta fita daga cikin dakin.
    Karan rufe kofa ne ya sanyata dawowa daga duniyar tunanin da tatafi.
   Zaune ta mike tare da kallan agogon dakin da ganin 11saura Amma Shaheeda bata zoba.

     Bata gama tunanin ba taji sallamar ta da sauri ta mike tare da rungume ta itama rungume tan tayi sabo da murnar ganin yar uwar tata.
    Janyota tayi tayi suka zauna kan kujera ta shiga kallanta tana sha'awar yanda ta kara girma.da yake Ita rana da girman jiki tayi fari tayi kiba tayi mulmul da ita ga kwalliya kayanta kala kala gwanin ban sha'awa.
   
    Ya Sapna ya gidan da kowa da kowa.
   Murmushi tayi tare da shafa fuskar tace lafiya qlau yr lukuta.
       Dariya ta danyi tare da fadin kai yaya nice yar lukutar.
    Eh mana kinaga yanda kika koma kuwa ai kinyi biyuna.
    Dariya ta kuma yi sannan tace ya dan Asabe yana gaidake.
   Duk da tasan karya take kawai ta fadane dan taji ddi.
    Kanta a kasa tace ina amsawa.
    Kai! Ya Sapna meya sameke duk fuskar ki tayi wani iri.
     Shiru tayi bata bata amsaba saida ta kuma maimaita mata tambayar sannan tace bigewa nayi.
Ta shiga lalubar ledar data shigo da ita tana fadin me kika kawomin yar kirki.
    Itama bata yarda da abinda sapnar ta fada bah saita danne ledar alamun bazata badaba.
    Dago da idanta tayi ta kalleta da mamakin hanata daukar ledar sannan tace ki gayamin ya Sapna meya sameki.
     Ohh! Shaheeda dole sai kinji believe me mana na gaya miki abunda ya faru aa ya kikeso nayi ne.
    Am sowie sis I don't means to upset u Jst am caring ne Amma shikenan. Kinga ta shiga dauko mata abubuwan cikin ledar tana murmushi tana nuna mata.
Kinga wannan duk abunda yaya ya siyamin nake tara miki
Chocolate, biscuit da sauran su.
    Kallan ta kawai Sapna keyi duk da karancin shekarunta tana da hankali.
    Kin gani ya Sapna taci gaba da nuna mata duk dan ta sanyata farin ciki.
    Sannan ta kuma janyo wata ledar tace kinga duk juice ne nake tara miki nasan kina so ko.
   Totally speechless dan batama da bakin magana sai ido take zuba mata.
    Ya sapna kinga kudin makarnta na 50 saina raba biyu na anje miki rabi tunda nasan kinaso ko?
    Batasan lokacin data rungume taba tana kuka.
   Shiru tayi rike da kudin a hannunta tana jin sautin kukan yayar tata.
    Sapna duk wannan abun niya kamata ace ina miki amma bani da damar hakan.
     Ahankali ta janye jikinta daga nata itama hawayan take tasa hannu tana goge mata tare da murmushi tana girgiza kai alamun ta daina kukan.
     U deserved it sis,ur my world,everything mind is belongs to u even my self.even god knows hw I feel about u dats y,am still here for u I rwwly Lov u nd I always Will♥
      Kuma rungume ta tayi tana kuka sannan ta danka mata kudin a hannunta ta tana murmushi.
      Sapna! Sapna!! Taji murya Ya Abba na kwala mata kira.
   Gabantane yayi mugun faduwa take suka kama kallan juna ita da Shaheeda,
Hannu ta Dora aka tare da fadin nashiga uku 🙆🏻

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
  01 Amal fansclub 💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHIWhere stories live. Discover now