🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)2⃣5⃣
Har bakin kofar toilet din suka karasa.
Yawwa tana ciki amma tasa key.
Kallan kofar ya tsaya yi kafin yace amma kinsan irin wannan kofofin nada huyar sha'ani.
Tou yanxu meye abunyi.
Baki da wani Abu da za'a iya sawa dole saide a kwance kofar.
Amma kana tunanin hakan zai yiyu?
Kawai inda hali koma ta yaya ne Akarya kofar nide kawai burina ta gane niba sa'ar yinta bace.
Shiru yayi nadan wasu lokuta kafin yace inba damuwa zan iya zuwa na dawo.
Eh zaka iya amma kayi sauri banasan asan da zuwanka cikin gidan nan.
OK ba matsala yanzu zan dawo.Yana fita itama tabi bayansa sannan ta juyo ta dawo zuwa dakin.
Bakin gado ta zauna tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin Sapna.Ita kuwa tana cikin wardrobe tagama jigata gaba daya duk jikinta yayi weak saboda bata samun enough iska.
Gaba daya duk abunda suke fada akan kunan kunnan ta.
Jin namiji ya fita tayi tunanin kode fitowa zatayi tana ganin inba namiji zata iya cin galava kan Aunty Rahman.
Ahankali tadan tura kofar wardrobe din.
Da sauri ta koma baya tareda tushe bakinta ganin Rahama zaune saman gado tana facing wardrobe din.
Zuciyarta ce ta gaya mata kawai ta fita komai ta fanjama.
Rufe idanunta tayi tare da fara salati cikin zuciyarta da neman samun nasara gurin Allah.
Kawai bude kofar tayi ta fito da gudu ta nufi falo dan fita daga cikin part din.
Rahma dake zaune bakin gado tayi saurin tsorata tare da mikewa ganin mutun ya fito daga cikin wardrobe dinta dan ita gani take Sapna na cikin toilet din.
Bita tayi falon itama da sauri.
Tsaye ta ganta bakin kofa tana ta faman kokarin bude kofar.
Da alama ta sakama kofar key.Hahhhahahah ta kama yin dariyar mugunta.
Yaro besan wutaba saiya taka.
Ke Har kina tunanin kina da wani wayo ko?
Jingina bayanta tayi tare da zameyawa kasa ajikin kofar tana hawaye.
Da ker bakinta ya iya furta magana sabo da wani irin nauyi da taji yayi mata.
Dan girman Allah Aunty ki rufamin asiri kamar yanda Allah ya rufa miki ki barni da irin kaddarar da nake da ita.
Kada ki kuma saka rayuwata cikin wani duhun.
Ki taimaka min ta karashe maganar tare da fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya.Sapna nike da burin haskaka miki rayuwa bana fatan kici gaba da rayuwa cikin kunci.
Wallahi nayi miki alkawarin kika bani hadinkai zaki dauwama cikin farin ciki dan tana maganar tana takowa zuwa inda Sapna take.
Da sauri ta mike ganin tana yowa wajanta.
Itama tafiya take da baya tana fadin wallah da kina kaunata bazaki taba gayamin irin wannan bah.
Kuma wallah kika sake kika tabani saina kashe kaina.ta karashe maganar tare da rugawa zuwa cikin kitchen ta dauki wuka ta rike a hannunta.Kallan juna suka tsaya yi.
Rahma ce ta kuma takowa.
Dakata! Tace da ita kina kuma taku daya kuna kasheki kona kashe kaina.
Ta nuna mata wukar tana karkarwa dan gaba daya ta koma kamar mahaukaciya gashin kanta duk ya baje.na goshinta kuwa dana keyarta duk ya kwanta saboda gumin da tayi.Buga kofar aka shiga yi.
A lokaci daya suka juya dan kallan kofar sannan suka juyo suka kalli juna.
Murmushi Aunty Rahama tayi tare dayin hanyar kofar dan budewa.
Dube Dube Sapna ta shigayi dan samun abunda zata kare kanta dan tasan Mundin ta bude kofar nan kashinta ya bushe.
Dinning ta nufa dan dauko wani katan flask me dauyi.Ita kuwa harta karaso wajan ta xura key din hannunta cikin kofar tana kokarin budewa.
Da gudu ta karaso gun tare da buga mata shi a kanta.
Batare da tayi wani kwakkwaran mutsiba ta badi kasa sumammiya.
Yanda flask din hannunta tayi tana karkarwa ta kuma dannawa kofar key.
Gaba daya ahankali ta ya tashi ga dodo sai faman buga kofa yakeyi.
Ahankali tane ya dawo kan Rahma dake kwance a kasa ko motsi bata yi.
Da sauri ta karaso wajanta tareda tsugunnawa ta kamo kanta tare da dorawa a kanta ciyarta.
Jin lema a hannunta ta yasanyata saurin dubawa.
Jini ta gani duk ya bata gurin.
Idanunta ta zaro tare da sanya hannun data shafo jikinta tushe bakinta.
Itama jinin duk ya bata mata kaya.
Gaba daya hankalin ta ya gama tashi.
Aunty!! Ta shiga kiran Sunanta tana jinjigata tana kuka.
Da sauri ta mike daga kusa da ita tare da komawa gefe da baya da baya tana girgiza kanta.
Durkushewa tayi tare da saka hannayanta cikin gashinta ta fashe da wani saban kuka.
" Wayyo Allah na ni Sapna wannan wata iriyar mummunar kaddarace.yau nayi kisan kai kenan.koda yake gwarama a kasheni nima tunda rayuwata bata da wani amfani.
Tabbas ban cancanci zama cikin duniyar nan ba hausawa na fadin bayan huya sai ddi,amma ni gashi kullum abun kara gaba yake na shiga uku Allah na rukeka dan darajar wanda ka halicci duniyar nan dominsa Allah kadau raina a cikin daran nan dan bana fatan na wayi gari acikin wannan duniyar Allah".
Fashewa ta kuma yi wani saban kukan tana kallan Rahma a kwance.
Idanunta ta kulle tare da furta kallamar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.
Ita taketa faman maimaitawa ko taji sanyi cikin zuciyarta😓Shikuma dodo daya gaji da bugawa kawai yyi tsaki tare da barin gidan dan bayasan wani ya gansa.
😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘

YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...