🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)2⃣0⃣
BAYAN SHEKARA 3
Su sapna an zama yn mata sosai dan yanzuma suna SS2 first term.
Ta kuma kyau da haske duk da batajin ddin zaman gidan nasu haka itama safiyar.
Hafsa tana da da daya ita kuma Nana tana da yara biyu.
Har yanzu dangin Sapna basa nemansu kuda Naja taje gida tayi maganar yaran ba'a wani daukarta da mahimmanci hakan yana mutukar bata mamaki.
Hakan inta nuna tana San taje da yaran su dan Asabe basa yarda.
Haka take rabuwa dasu saide lokaci lokaci Sapna kan leka gidanta kuma ana kawo Shaheeda ma.
Ita kuwa Rahama da mijinta Abba kullum suma cikin fada suke kuma Har yanzu taki haihuwa gashi ta raina Umma.
Haka shima kusan kullum a bige yake shigowa gidan.
Wani zubin yana zage zage wani zubin kuma surutai.
Itama Umma babu abunda ya canza daga halinta kullum cikin ta kurama Sapna take bata kaunar ko kadan taga taci gaba burinta ta zamo ci baya.
Jin ddin sapna shine kawai ta tafi makaranta shiya aa kullum bata fashi tana samun hutawa.kuma kullum basa bata breakfast saide in taje makaranta kawarta Husnah ta kawo mata Har kudin makaranta take bata dan tana tau sayin kawar tata.
Monday mrng❣
Da sassafe Sapna ta tashi kamar yanda ta saba dan yanzu Umma ta kori yn aiki ita keyin komai.
Bayan ta gama aiyukanta sannan ta hada musu breakfast ta kai dakin ummar.
Toilet ta nufa tayi wanka ta shirya cikin uniform dinta.
Sannan ta fito.
Ita kuwa Safiya tana kwance saman gado dan yanzu kullum saita sanya sunyi late ko kuma a dukeso.
Ahankali ta tsaya kusa da gadan dan ta tasheta.
Fashi 8am ta kusa yanzu inta tashi tayi wanka,kwalliya, breakfast sai kusan tare tasan yau zasu tafi gashi yau dutyn Uncle John ne kuma mugune.
Ya Safiya!! Ta fada ahankali sau biyu.
Tana mikewa ta wanketa da mari.
Ke wata iriyar jakace,wata iriyar kwakwalwa ke gareki na fada miki kada ki kuma tashina a bacci ko ban gaya mikiba.
Hannunta akan fuskarta dan taji zafin Marin ta Shiga kada kai dan ta gaya mata.
Kin gayamin amma dan Allah kiyi hakuri ki tashi ki shirya dan wallahi yau dukan late za'ayima.
Akashemu kuma ni karki dameni banza kawai mutun yana baccinsa kin zo kin ta sheshi ta mike tare da bangajeta ta shige toilet din.
Binta tayi da kallo sannan ta fice daga dakin.
Waje ta fita driver na zaune cikin mota yana jiranau.
Dama shima ya saba da halin safiya shiyasa ma baya damuwa.
Gaidashi Sapna tayi sannan ta zauna tareda fadin kaga Har yanzu shiru bata gama shiryawa ba.
Hmmm! Rabu da ita komai ae lokaci ne,wlh nan gaba koda ance tayi bazatayi ba.
Hakane Allah de yasa tayi maza ta fito dan bansan dukan late wlh.
Saida suka kusa 1hr suna jiranta sannan ta fito daga cikin gidan sanye da kayan gida.
Tana shiga cikin motar ta zauna.tare da fadin ka kaita makaranta ni unguwa zaka kaini.
Cikin zuciyarta tace lallaima safiyar nan yr rainin hankali ce.dama tasan ba makarantar zata ba ta fatamin lokaci.
Habu ka fara kaini unguwar saika kaita makarantar.
Wallahi ni zaka fara kaiwa tunda nice zani guri mai mahimmanci ita ta tari napep ta tafi mana.
Ni kike gayama wannna mafanar.
Ai maganar gaskiya ne da kinsan bazakiba aisaiki fadamin amma kika zaunar damu tun dazu ina jiranki kuma yanzu ki fito kice ke za'a kai.
Habu dan Allah muje ni ina kara yin late.
Lallaima yarinyar nan ni kike gayama wannna maganar.
Banza tayi da ita bata kuma tanka mataba.
Fita tayi daga cikin motar shikuwa habu yaja motar ya tafi.Tana Shiga cikin gidan da kukanta.gurin Umma ta nufa.
Tana toilet dan haka sai ta zauna tana jiran fitowarta.
Bata dau lokaciba ta fito tana tsane kanta ganin Safiya zaune ya sanyata dakatawa tare da fadin lafiya kuwa naga kin dawo ko kin fasa tafiyar ne?
Cikin muryar shagwaba tace waini za'a ma iskanci.
Wai habu cewa yayi saiya fara kai sapna sannan zai dawo ya kaini.
Wata ashariya taja sannan tace motar ta uban shice da Har zai fadi hakan kaita yayi saide ta taho a kafa maga ubanda zai dauko ta.
Bani wayata na kira sa.Suna tafiya suna hira saura kadan ya karasa da ita makarantar.
Wayar shi ta fara ringing.
Tunda yaga numb.Umma hantar cikinsa ta kada.
Da sauri ya daga tare da karawa a kunne.
Barka da safiya hajiya.
Habu ni zaka watsama kasa a ido.ka nunamin ban isa da gidana ba.
Wallahi hajiya ba haka babe Ayi hakuri dan Allah.
Toh da ka kaita da baka kaitaba ka dawo yabzunnan na baka 5mins Wallahi ka huce abakin aikinka.
Bata jira cewar shiba ta kashe wayar.
Da Sauri ya tsaida motar tareda kallan Sapna da tayi shiru tana sauraran wayar su da Umma.
50ya mika mata tareda fadin ga shinan ki hau napep ya karasa dake sai nazo daukarki.
Toh kawai tace dan bakinciki ji take kamar ta yi kuka.
Sannan yaja motar da sauri sai can gidan.
Napep tq samu ta shiga dan ya karasa da itama makarantar dan 9:43 am lokacin.😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘
YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...