🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)Page 9 continuation
Rungume ta tayi tareda fadin zata dawo Amma saikin dena kuka kinji.
Bazaki tashi ki karasa wanke wankenba kuma ki bar yarinyar nan karta kuma taba mana kwanika tayi mana kazanta.
Zauna kinji Shaheeda yanzu zan karasa saina kaiki wajan Anty Naja amma kar kiyi kuka.
Kanta ta gyada tareda gogema Sapna kwallar data fado mata kan fuskarta.
Ahankali take tafiya dan duk jikinta yayi tsami harta karaso wajan.
Saura kuma naji wannan magana a bakin wani saina kusan kashe ki dake da Shaheeda dukkan ku.
Kina jina ko?
Da sauri ta gyada kanta tareda fadin eh.
Sannan ta karasa wajan tanayi tana kwallah ga kayan da uban yawa Har ta gama tanayi tana jiyowa tana kallan Shaheeda dake zaune Har bacci ya dauketa ta kwanta agurin gashi Har rana ta taddo wajan.
Ahankali ta mike dan kaita daki.
Tana GAF da karasawa wajanta Safiya tace ina kuma zaki.
Kamar zatayi kuka ta nuna Shaheeda tareda fadin tayi bacci kuma tana cikin rana shine zan kaita daki.ta karashe maganar tareda juyawa zata dauke ta.
Huce kije saikin gama duka kin gyaramin wajan tukun zan ki dauketa Umma ta fada.
Da kamar zatayi magana amma saita fasa tana juyawa tana kallanta harta koma tazauna taci gaba.
Saida ta gama duka ta kwashe kwanikan ta share wajan sannan ta dawo ta dauki Shaheeda ta kaita daki ta kwantar da ita tareda tsora mata ido tana kallan fuskarta.
Ahankali ta shafa fuskarta tareda manna mata peck adan bakinta tana tunanin yanda mamansu take rayuwa dasu.
Jin ana kiran sallah azhr ya sanyata mikewa alwala ta daura tayi sallah sannan ta rokama mamansu sauki gurin Allah itama baccin ne ya dauketa nan gurin.Hafsa na dawowa daga makaranta dakinsu ta nufa bayan tayima Umma sannu da gida sannan ta nufi toilet ta bama kanta shower sannan ta fito.saida tayi sallah taci abinci dan ita atunaninta su Sapna suna gidan Naja.
Shiyasa bata ma name suba.
Jakarta ta dauka sannan ta nufi dakin Umma de tana kallanta bat kula taba.
Sapna ta gani kwance tana bacci ga Shaheeda bisa kujera bata ce musu komaiba.
Daki ta nufa ta saka kaya sannan ta fito falan ta zauna.
Shaheeda ce ta tashi tana ganin hafsa ta kama kuka.
Lafiya Shaheeda menene kike kuka.
Safiya da Umma ne suka doki ya Sapna.
Toh ya kuri zansa dodo ya cinye su suma kinji amma fa karki gayama yaya dan Asabe dan in kika fada shima dodo cinyeshi zai yi .
Kai ta gyada mata tareda fadin bazan fada ba.
Yauwa yr kirki bara na dauko muku abinci nasan Baku ciba.sannan ta mike ta fita daga dakin.
Bayan ta fitane Sapna ta mike ta nufi toilet ta zubama kanta shower dan duk jikinta radadi yake mata.sannan ta wanke bakinta ta fito.
Lokacin Har hafsa ta fara bama Shaheeda abincin.
Kallo daya tayima Sapna taga fuskarta da idanunta duk sun kumbura.
Zama tayi tareda cewa ya hafsa sannun da dawowa.
Janyo flask din abincin tayi tana zubawa.
Me kika yima su Umma suka bigeki.
Kallo daya tayima hafsa ta dukar da kanta kasa tana zuba abincin batareda da tace mata komai ba.
Har ta gama zuba abincin sannan tace fada mukayi da Safiya. Daga nan bata kuma cewa komai ba ta fara cin abincin ta.
Amma Sapna me yasa kike boyemin wani abun.
Cikin muryar kuka idanunta na zubar da hawaye tace ya kibari kawai nace fada mukayi da safiya bakomai kuma.
Dafata tayi tareda fadin kiyi hakuri kibar kuka ya isa haka.
Rungume hafsa tayi tareda cigaba da kuka.
Ya isa haka Sapna kidena kukan nan haka.
Dan Allah Ya hafsa ki rinka yima mama addu'a Allah yasa ta warke ta dawo wajan mu.
Insha Allah ina yimatakuma zanci gaba dayi mata kinji maza kici abincinki kinsan in bakya cin abinci yaya fada zaiyi miki.
Haka taci gaba da cin abincin badan tanajin dadin saba.
Shaheeda kuwa cin abincin ta take tana kallan Sapna.
Suna hada ido Sapna ta sakar mata murmushi.BAYAN WATA 4⚜
Lokacin har anyi bikin Abba Ankawo Amarya Rahama.
Rahma ko kadan bata da kunya batasan darajar kowaba kullum cikin fada suke da Abban kowa yanaji babu wanda ya isa yayi mata magana.
Gashi kullum gidan cike yake da baki maza da mata.
Haka zalika ta tsani dukkan wani mahaluki dake gidan.
Haka shima dan Asabe yayi aure harma ya maida Shaheeda gurinsa kuma Alhmdullh ya sami mata ta gari kullum tana cikin samun kulawa.
Dayake yanxu yayi nisa dasu ba kullum yake zuwaba yakanzo ya koma ne.
Kuma yakan kawo Shaheeda taga Sapna kuma itama tana zuwa wajan ta.
Ya kaisu bauchi Har sau uku Amma Har yanzu jikin mamansu ba sauki saide abunda yayi gaba.
Kullum sapna abun tausayi agidan nan yanzu sun shiga jss1.
Kuma Har yanzu tana da ko karinta an sama Nana da hafsa rana dan suma Bilkisu za'ai nan da wata biyu.
Haka rayuwa ta kasance musu.
Kullum in Umma na cikin kyara da tsangwamar sapna komai tayi ba daidaiva.
Wani zibin kuma ta sanya Abba yayi mata duka.
Har ita matar Abban ta maida ta tamkar yr aiki.
Dan sun hade kai da Umma
Allah Sarki Sapna ga hakuri gashi ko me za'a mata bata fada.hakanne ya ke sanya Hafsat jin haushinta tun tana magana Har ta gaji.👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Haka rayuwar gidan fahad yau suyi fada gobe su shirya dan yanzu salma tabar teaching kullum bata da Lokacin sa dab business takeyi.
Ga shegen kishi amma bata iya kula da miji ba.kullum mummyn ciken fada takemai akan ya kara aure ko zai samu nutsuwa amma ko kadan yaki kamar wanda tamai asirivsaide suyita fada suna shiryawa.
Yauma tunda safe suka fara fadn da suka saba.
Haba fahad kai kullum ka gwammace muyita fada kamar wasu yara gaskiya nina gaji.
Shikenan nagaya miki banasan wannan business din naki saboda ko kadan bakya San kulawa dani.
Toh so kake na goyaka na rinka yawo dakai kokuwa ya kakesan nayi maka.
Sai naga kamarma bakin ciki kake yiman Wallahi.
Naji ina miki bakin ciki ni yawan da kikene bana kauna ki zauna mana agida arinka zuwa ana siyan kayan naki.
Wallahi bazai yiyu ba kasan ina da kishi dan arinka Tara mata suna kalle min miji Allah ya kiyaye.
Shikenan kije kiyi Wallahi aure zan kara.
Wallahi Har abada bazaka yimin kishiyava mundin kuwa ta shigo gidan nan sunan ta gawa.
Ko kulata beyiba ya fice daga gidan.
Zama tayi kan kujera tareda fashewa da kuka.akan me fahad zai ambaci sunan data tsana duk duniya Wallahi bazai sabova bara ya dawo gidan saiya gaya mata yar gidan ubanwa zai auro mata.😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘
YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...